An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, ala tilas ne kasashe masu girman kai suka amince da shirin Iran na nukiliya, domin basu da wani zabin da ya wuce hakan.
Published in Jagora
Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya aike da wasika zuwa ga shugaba Rauhani dangane da batun yarjejeniyar yin aiki d yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.
Published in Jagora
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar dukkanin ci gaban da Iran ta samu tsawon shekaru talatin da wani abin da suka gabata ta same su albarkacin juyin juya halin Musulunci na kasar, yana mai cewa matukar aka ci gaba da riko da koyarwar juyin, to lalle irin tasirin da Iran take da shi a yankin Gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya zai ci gaba da karuwa.
Published in Top News
Kafafen Watsa Labarun Duniya Sun dauki jawabin jagoran juyin Musulunci na Iran da ya yi na gargadin Saudiyya dangane makomar mahajjatan kasar da su ka rasa rayukansu da kuma wadanda su ka bace. Gargadin na jagoran juyin Musulunci dai ya zo ne a wurin yaye dalina jami’ar Soja, a ranar larabar da ta gabata. Jagoran da ya ambato abinda ya faru a Mina, ya ja kunnen  mahukuntan Saudiyyar akan duk wani mataki da za su dauka na cin zarafi da kuma wulakanta gawawwakin mahajjatan Iraniyawan  ko kuma wadanda su ke a raye. Jagoran ya ce; matukar saudiyya ta yi hakan, to Iran za ta maida martani mai tsanani akanta. Bugu da kari, jagoran ya bayyana wajabcin kafa kwamitin bincike wanda zai kunshi dukkanin kasashen musulmi da su ka hada da Iran domin gano hakikanin abinda ya faru. Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya dauki labarin ne da cewa: “Wajibi ne mahukuntan Saudiyya su kwana da sanin cewa duk wani cin zarafi da wulakanta mahajjatan Iraniyawa, a makka da Madina, to zai sa su fuskanci martani mai tsanani daga Iran. Shi ma kamfanin dillancin labarun Associaten Press ya dauki labarin ta hanyar bijiro da wani sashe na jawabin sannan kuma ya ce; Idan har Saudiyya ba ta yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta ba na mayar da mahajjatan Iran da su ka rasu zuwa Tehran, to za su fuskanci martani mai tsanani. Tashar telbijin din cnn ta Amurka wacce ta bijiro da wani sashe na jawabin jagoran, ta karkare da cewa; Kin mayar da gawawwakin mahajjatan Iran da su ka rasa rayukansu a Mina, to za ta fuksanci matsanancin martani. Sauran Kamfanonin dillancin labarun da su ka dauki jawabin na jagora, sun hada da Xinhua na kasar Sin, da tashar telbijin din i.b.c news. Sai kuma wasu jaridun wannan yankin kamar Al-Yaum, Sabi’i ta kasar Masar da al-Nashrah’ ta Lebanon da kuma alqudsul araby. Kawo ya zuwa yanzu dai hukumar aikin haji da umrah, ta Iran, ta sanar da adadin  mahajjatan kasar da su ka rasa rayukansu da cewa sun kai 464. Kuma tun a jiya alhamis ne aka yi ganawa a tsakanin miniztocin aikin lafiya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Hassan Hashimy da kuma takwaransa na Saudiyya Khalid Bin Abdulaziz, suka cimma yarjejeniyar  dauko mamatan mahajjantan zuwa Iran.  
Published in Sharhi
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi kira kan kara habaka karfin sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran domin kara karya karfin gwiwar makiya kan daukar duk wani matakin wuce gona da iri kan kasar Iran.
Published in Top News
A wani jawabi da ya yi a jiya lahadi gabannin fara darasinsa na “Bahasul Kharij”, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi magana kan hadarin da ya faru a Mina da yayi sanadiyyar mutuwa da raunata dubban mahajjata inda ya bayyana cewar: Al’ummar musulmi suna da tambayoyi masu yawa kan abin da ya farun, don haka mahukuntan Saudiyya, maimakon kokarin wanke kansu, wajibi ne su nemi afuwar musulmi da iyalan wadanda abin ya ritsa da  su, sannan kuma su dau alhakin gazawar da  suka yi da kuma sauke nauyin da ke wuyansu.
Published in Sharhi
Jagoran juyin Musulunci na Iran ya kira yi Saudiyya da ta dauki alhakin abu maras dadi da ya faru na mutuwar mahajjata a Mina, bisa ka’idar gaskiya da  kuma adalci. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei da ya fitar da bayani akan abind aya faru a Mina na mutuwar mahajjata, ya taya iyalan wadnada su ka rasa rayukansu alhini tare, tare da fatan samun sauki ga wadanda su ka jikkata. Jagoran juyin musuluncin na Iran  ya kuma shelanta kwanaki uku na zaman makoki a Iran, sannan ya kara da cewa:  A tsawon yau, wakilan jagora a hukumar aikin haji da umrah, sun dukufa ne wajen sanin Iraniyawan da su ka rasa rayukansu  da kuma gaggauta yi wa wadanda su ka jikkata magani da dawo da su zuwa Iran. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ci gaba da cewa; Hukumar Aikin Haji da Umrah ta Iran ta bada duk wani agaji da taimako ga sauran mahajjata na sauran kasashe bisa aiki da hakkin ‘yan’uwataka, ta Musulunci.      
Published in Jagora
Shimfida: Kamar yadda aka saba a kowace shekara, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kan aike da sako na musamman ga mahajjatan da suka fito daga kasashe daban-daban na duniya wanda ake karanta shi a ranar Arafa. Abin da ke biye fassarar sakon da Jagoran ya aike wa mahajjatan wannan shekarar ta 1436 ne:
Published in Top News
Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khamina, ya ce kutse cikin
Published in Top News
Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya kirayi kasashen nahiyar turai da su zama masu ‘yancin siyasa, maimakon zama ‘yan amshin shata ga siyasar Amurka.
Published in Jagora
Page 2 of 5