An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kai ziyara gidajen iyalan wasu mabiya addinin Kirista da suka rasa iyalansu yayin kallafaffen yakin Iran da Iraki don taya su murnar bukukuwan Kirsimeti
Published in Jagora
Wani masharhanci kan harkokin kasashen musulmi a kasar Tanzaniya ya bayyana cewa; Sakon wasikar da jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya aike ga matasan kasashen yammacin Turai ya fayyace hakikanin kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Published in Jagora
Wani fitaccen marubuci dan kasar Italiya ya bayyana wasikar jagoran juyin juya halin muslunci zuwa ga matasan kasashen turai da cewa tan ada matukar muhimmanci.
Published in Jagora
Jakadan Iran Gholam Ali Khosrou a zamn babban zauren majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa manufar wasikar jagora Ayatollah Sayyid Ali Khamenei zuwa ga matasan turai it ace bayyana mahangar musulunci kan yaki da ta’addanci a matsayi na duniya baki daya.
Published in Jagora
Shugaban kwamitin al’adu na majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Malam Ahmad Salik ya bayyana cewar manufar wasikar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike wa matasan Turai a kwanakin baya ita ce gabatar da Musulunci na hakika.
Published in Top News
 Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Sakon da jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran ya rubutawa da matasan kasashen yamma, bayan harin da yan ta’adda suka kai a birnin Paris na kasar Faransa makonni biyu da suka gabata dana dauke da darussa masu muhimmanci wanda yakamata a kula da su. A cikin sakon dai Jagoran juyin juya halin Musulunci Aya. Sayyeed Aliyul Khaminae ya bayyana yan ta’adda a matsayin musiba ga  musulmi da kuma kasashen yamma gaba daya da kuma duniya gaba daya. Sakon ya kuma kara da cewa hari na karshe karshen nan da yan ta’addan suka kai birnin Paris na kasar faransa, wanda ya hargitsa harkokin zamantakewa a kasar da kuma wasu kasashen turai , ya zama darasi ga wadanda suke jin irin abubuwan da suke faruwa a kasashen Iraqi, Syria, Afganistan, Yemen da sauran kasashen Musulmi wadanda suka dade cikin wannan halin. Abin bakin ciki inji jagoran , shi ne wasu kasashen yamma suna goyon bayan wadan nan yan ta’addan har ma suna masu rarrabasu tsakanin masu kyau da marasa kyau. Jagoran ya rubuta wannan sakon ne ga matasa a kasashen yamma, don sanin cewa matasan sune wadannan yan ta’adda suke farauta don shiga cikinsu, ganin cewa gogewarsu a harkar rayuwa kadan ne, kuma su ne suke da zukata masu tsarkin da zasu iya karban gaskiya a duk lokacinda ta zo masu. Wannan dai shi ne sakon jagoran na biyu bayan wanda ya rubutawa matasan a cikin watan Jenerun shekara ta 2014 bayan harin da wasu yan ta’addan suka kan ofishin wata mujalla a birnin Paris na kasar Faransa. Sakonnin guda biyu dai suna kira ne ga matasan kasashen yamma musamman kasashen Turai da Amurka na su fahinci wannan gaskiyar kafin su fada cikin tarkon yan ta’adda masu wuce gona da iri da sunan addinin da basu sanshi ba. Har’ila yau sakonnin biyu dai sun yi ishara ga yadda shuwagabanni da kuma yan siyasa a kasashen yamma da Amurka suke goyon bayan yan ta’adda wadanda suke kira “masu matsakaicin ra’ayi”, don suna zaton wadan nan yan ta’addan zasu zama masu amfani a garesu, don zasu kasu ga cimma manufifinsu a kasashen musulmi. Amma wadanda suke cutar da su kuma sune yan ta’addan ta yakamata a yake su. Jagoran ya bayyana cewa matukar yan siyasar kasashen yamma sun ci gaba da daukar yan ta’adda kamar yadda suke a halin yanzu, to kuwa babu ranar da za’a kawo karshen ta’addanci a duniya. Sakonnin zuwa matasa kasashen yamma sun jaddada bukata ga  shuwagabannin kasashen yamma na su daina dorawa sauran kasashen duniya al’adunsu wadanda suka bambanda ta na sauran mutanen wadan nan kasa she. Don hakan yana daga cikin dalilan suke samarda masu tsatsauran ra’ayin a cikin al’amuran al-adu ko iddinan wadanan kasashe ko mutane.
Published in Sharhi
A jiya ne aka fitar da sakon jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei wanda ya aike zuwa ga matasan nahiyar turai.
Published in Jagora
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa; Iran zata ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Palasdinu da dukkanin karfinta tare da kare musu hakkoki.
Published in Jagora
Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya gana da Firayi ministan harkokin wajen kasar Algeriya Abdulmalik Salal.
Published in Jagora
Page 1 of 5