An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Labarai
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, kasashen Iran da Rasha za su ci ga da yin aiki kafada da kafada a dukkanin bangarori.
Babban mai shigar da kara a kasar Belgium ya sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kame wasu mutane da ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai birnin Brussels a kwanakin baya.
Rahotanni daga kasar Madagascar sun bayyana cewar firayi ministan kasar Jean Ravelonarivo ya sanar da murabus dinsa daga matsayin bugu da kari kan rusa gwamnatinsa biyo bayan tsanantar takaddamar da ke tsakaninsa da shugaban kasar Hery Rajaonarimampianina.
Rahotanni daga kasar Yemen sun bayyana cewar sojojin kasar Yemen da dakarun sa kai na kasar sun sami nasarar hallaka wani adadi na sojojin Saudiyya da kawayenta bugu da kari kan wadanda aka kama a matsayin fursunonin yaki.
Mukaddashin babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Birgediya Janar Massoud Jazayeri yayi watsi da bukatar sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry na tattaunawa da Iran kan shirin makamanta masu linzami yana mai kiran ma'aikatar harkokin wajen na Iran da su mayar da masa da martani mai karfin gaske.
Ayatullah Muhammad Emami Kashani, daya daga cikin mataimakan limamin Juma'ar birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ja kunnen al'ummar kasar da su yi taka tsantsan dangane da ci gaba da kokarin makiyansu na ganin sun cutar da su a duk lokacin da suka sami wata dama.
Yau juma’a ana gudanar da zaben shugaban kasa a Djbouti, inda shugaban kasar mai ci Isma’il Umar Guelleh ke fatan samun galaba a wannan zabe.
Banki Duniya ya amince Baiwa Kasar Tanzaniya Bashin Dalar Amurka million 65
Kasar Girka ta fara mayar da kashi na biyu na yan gudun hijra zuwa kasar Turkiya.
Akalla Mutane biyu ne suka sara rayukansu sakamakon buda wuta da wasu 'yan bindiga suka yi a birnin Magadushu fadar milkin kasar Somaliya.
Page 5 of 2063