An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Labarai
Firayi ministan kasar Belgium ya sanar da cewa gwamnatin kasar za ta ci gaba da tsaurara matakan tsaro da zama cikin halin ko ta kwana duk kuwa da kame wani adadi na wadanda ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai wa kasar kwanakin baya.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zargin sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na cewa tana barazana ga tsaron yankin Gabas ta tsakiya tana mai cewa wajibi ne Amurka ta daina goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda sannan kuma ta fice daga yanki matukar dai tana son taimakon tsaron yankin ne.
Rahotanni daga Belgium na cewa mutumin nan mai suna Mohammed Abrini da aka cafke jiya, ya tabbatar da cewa lalle shi ne "Mai Malafa", da ake zargi shi ne mutum na uku da bam dinsa ya ki tashi, a harin Brussels.
Kasar Korea ta Arewa ta sanar Yau Asabar da cewa tayi nasarar sake harba wasu makamai masu linzami samfurin ICMB masu iya kaiwa ko'ina.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kery ya yi kira ga 'yan Taliban na Afganistan da su shiga shirin samar da zamen lafiya domin kawo karshen zubar da jini a wannan kasa.
Ofishin Jakadancin Amurka a Turkiyya ya yi gargadi akan yiwuwar kai hare-hare ta'adanci a biranen Satambul da Antaliya.
'Yan adawa a Djibouti sun kalubanci zaben shugaban kasar da Ismail Omar Guelleh ya lashe da gagarimin rinjaye.
Jami'an tsaro a Guinea Conakry sun dauki matakin tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar da nufin dakile duk wani shirin kai harin ta'addanci musamman bayan hare-haren ta'addancin da aka kai kasashen Mali da Ivory Coast.
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya zargi kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da kokarin kunna wutan rikici a kasarsa ta hanyar tunzura wasu al'ummar kasar.
Kungiyoyin kasa da kasa da suke gabatar da tallafin bil-Adama da suka hada da kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross da na Red Crescent sun yi gargadi kan karin tabarbarewan al'amura da zasu wurga jama'a cikin mummunan yana yi a kasar Burundi.
Page 4 of 2063