An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Labarai
Thursday, 10 April 2008 11:47

Barazanar Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Gaza

Piraministan Gwamnatin H.K.I. Ihud Ormert ya sake jaddada cewa bazai yiyu akai ga matakin karshe ba a kokarin da akeyi na ganin an warware rikicin dake tsakanin Palasdinawa da Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila (H.K.I). a wannan shekara ta 2008. sannan ya sake bayyana aniyarsa na ci gaba da kai hare haren wuce gona da iri kan al'ummar Palasdnu. A karshen yawon bude ido da shugaban kasar Amurka George . W. Bush ya gudanar a yankin gabas ta tsakiya, haka nan a lokacin taron Anapolis shugaban na Amurka yayi ta jaddada alkawari wa duniya cewa kafin karshen shekara ta 2008 za'a kai ga kulla yarjejjeniyar sulhu tsakanin Palasdinawa da Gwamnatin H.K.I. amma tun bayan alkawarin na George Bush babu wani abu a kasa da duniya ta gani dake gaskata furucinsa banda ci gaba da kashe Palasdinawa, mamaye musu yankuna ta hanyar gine ginen sabbin matsugunan Yahudawa 'yan kaka gida da kuma tsananta yin kawanya wa al'ummar Zirin Gaza. sannan a bangare guda kuma Gwamnatin H.K.I. ta fake da zaman tattaunawan da takeyi da shugaban hukumar palasdinawa Mahmud Abbas wajen ci gaba da gudanar ta siyasarta na wuce gona da iri kan al'ummar Palasdinu.Sakamakon haka tsigeggen Piraministan hukumar cin kwarya kwaryan gashin kan palasdinawa Isma'il Haniyya yayi kira ga Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas kan ya dakatar da tattaunawan da yakeyi da jami'an gwamnatin h.k.I. domin babu wani alfanu da palasdinawa ke samu daga zaman tattaunawan banda karin cutuwa. Kuma a daidai lokacin da shugaban hukumar palasdinawa Mahmud Abbas ke gudanar da zaman tattaunawa da gwamnatin h.k.I. a gefe guda kuma matsin lamban Amurka dana 'yar lelanta H.K.I. sun hanashi daukan matakin gudanar da zaman tattaunawa na kai tsaye da 'yan uwansa palasdinawa dake Zirin gaza domin warware sabanin dake tsakaninsu, saboda gwamnatin H.k.I. da uwar gijiyarta Amurka basu kaunar ganin palasdinawa sun hada kai waje guda, kuma a kullum babu abin da sukeyi banda kokarin kara kunna wuta rikici tsakanin palasdinawan, don haka nema suka kakabama yankin Zirin Gaza takunkumi tare da yi masa kawanya da haka ya wurga al'ummar yankin cikin mummunar halin kakani kayi, kuma wani karin abin takaici shine ganin yadda yankin dake gabar yammacin kogin Jordan dake karkashin shugaban hukumar palasdinawama bai tsira daga hare haren wuce gona da irin sojin H.k.I. ba, gami da bakar siyasar gwamnatin H.K.I. na mamaya da killace yankin da ganuwar zalunci.Sakamakon wannan mummunar mataki da gwamnatin Amurka da 'yar lelanta H.k.I. ke ci gaba da dauka kan al'ummar Palasdinu, masana da masu fashin bakin waken siyasa ke bayyana cewa matukar gwamnatin H.K.I. zata ci gaba da gudanar da bakar siyasarta na nuna fin karfi kan al'ummar palasdinu tofa maganar kulla yarjejjeniyar sulhu tsakanin palasdinawa da Gwamnatin H.k.I. kafin karshen shekara ta 2008 da muke ciki da'awa ce kawai da shugaban kasar Amurka George. W. Bush ke furtawa domin cimma wasu bukatunsa na siyasa, kuma ita kanta gwamnatin H.K.I. da ta san ba a shirye take ta dakatar da gudanar da bakar siyasarta kan al'ummar palasdinu ba, shi ya sanya take riga kafin cewa bazai yayu a kai ga matakin karshe ba a shirin sulhunta tsakaninta da palasdinawa kafin karshen wannan shekara ta 2008 da muke ciki da shugaban kasar Amurka George. W . Bush ke babatu a kai, sannan take barazanar ci gaba da daukan matakin soji kan al'ummar palasdinu
Thursday, 10 April 2008 11:46

Ikirarin Shugaban CIA Kan Iran

A hira da ya yi da wata tashar telebijin ta Amurka (NBC) ranar Lahadin da ta gabata, shugaban hukumar leken asirin Amurka CIA Mr Macheal Hayden, ya yi zargin cewa kasar Iran tana kokarin kera makamin nukiliya, amma yace wannan raayinsa ne ya fadi. A gefe guda kuma, Mr.Hayden yace ya amince da rahoton da Cibiyar Leken Asirin Amurka ta fitar a ranar 16 ga watan Disambar bara, cewa shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya ne. Amma duk da haka shugaban na CIA ya ce, kunnen-uwar-shegun da kasar Iran take yiwa kudurorin Kwamitin tsaron  Majalisar Dinkin Duniya (MDD), yana nuni da cewa akwai abin da Iran take boyewa a aiyukanta na tace sinadarin uranium. Gwamnatin kasar Iran ta fadi ta nanata cewa, Iran tana gudanarda aiyukan tace sinadarin uranium ne domin aiyukan zaman lafiya, kuma wannan aikin ana yinsa ne karkashin sa idon hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya. Bisa yarjejeniyar Hana Yaduwar Makaman Nukiliya NPT, duk kasar da ta rattaba hannu kan wannan yarjejeniya, tana da hakkin tace uranium saboda samarda makashin nukiyar ga tashoshin nukiliyarta, domin aiyukan zaman lafiya. Kasar Iran dai mamba ce ta wannan yarjejeniya tun da dadewa.Saboda haka ne kudurorin Kwamitin tsaron MDD masu neman kasar Iran din ta dakatar da aiyukan tace sinadarin uranium a cikin kasarta, an zartar da su ne saboda manufofi na siyasa, kuma sun sabawa yarjejeniyar NPT. Tace sinadarin uranium da ma dukkan aikace-aikacen nukiliya da kasar Iran take yi, ana gudanar da su ne bisa dokokin kasa-da-kasa; a fili ake yinsu, kuma karkashin sa-idon masu bincike da kuma na'urorin daukar hokon hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya.Kofofin tashoshin aikin nukiliyar Iran dai, kullum a bude suke ga masu binciken Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, kuma babu wani abin boyewa a ciki. A baya-bayan nan ma wannan hukuma ta kasa-da-kasa ta fitar da wani rahoto inda ta baiyana cewa an warware dukkan batutuwan shidda dangane da shirin nukiliyar Iran, da a da take son tantancesu.Sai dai Amurkawa suna ta nanata zarginsu mara kan-gado, domin su nuna cewa sun sami wasu sabbin bayanai masu nuna cewa, wai kasar Iran tana kokarin kera makaman nukiliya a boye. Suna wannan zargi ne da zimmar wanzarda batun nukiliyar Iran din a hannun K.S.n MDD, lamarin da ya saba doka. HKMN, ita ce da da alhakin tabbarda cewa dukkan kasashenda suke cikin yarjejeniyar Hana Yaduwar Makaman Nukiliya NPT suna mutunta wannan yarjejeniya, ba kwamitin tsaro ba.Al'ummar kasar Iran da gwamnatinta ba zasu taba bada kai bare-ya-hau ba, kuma duk wani matsin lamba, da kudurorin da suka saba doka da Kwamitin tsaron MDD zata fitar, ba zasu hanata ci gaba da shirin nukiliyarta na zaman lafiya ba. Suma kasashen duniya sun san cewa, manufar Amurka da ma wasu manyan kasashe, shine hana kasar Iran samun ci gaban tattalin arziki, ta hanyar hanata cin moriyar fasahar nukliya ta zaman lafiya. Abin da yasa wadannan kasashe suke kokarin hana kasar Iran tace sinadarin uranium, shine takaita aikin tace uranium a hannun kasashe yan kadan kawai, domin hana sauran kasashe samun wannan fasaha
Thursday, 10 April 2008 11:42

Halin Da ke Ciki A Zimbabwe

A cikin shekaru 28 da shugaban kasar Zimbabwe Robet Mugabi ya kwashe yana jan ragamar mulkin kasar tun bayan da ta Samu yancin kai daga hannun kasar Birtaniya a shekara ta 1980 A karon farko Jam'iyarsa tasha kashi a hannun Jam'iyun Adawa na kasar a zaben yan majalisun dokoki dana shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar data gabata. Sakamakon zaben da aka fitar a kasar ta Zimbabwe ya zuwa yanzu ya nuna cewa Jam'iyar Adawa ta MDC Movemen for Democratic Chenge itace ta samu kaso mafi yawa a Majalisar dokokin kasar, inda ta samu kujeru 96 cikin kujeru 207 na Adadin kujerun majalisar kasar, yayinda itama daya daga cikin jam'iyun adawa ta samu kujeru 9 haka shima wani dan takara mai zaman kansa ya samu kujera guda daya kwal, Ita kuwa Jam'iyar Zanu PF mai mulki ta samu kujeru 94 cikin adadin kujerar majalisar kasar, da hakan ya sa ministoci 7 a gwamantin mugabi suka rasa kujerun su a majalisar dokokin kasar.To sai sanar da wannan sakamakon zabe ke da wuya sai magoya bayan jam'iyun Adawa na kasar suka bazama akan tituna suna nuna farin cikin su game da wannan gagarumar nasarar da suka samu, inda Jam'yar Adawa ta MDC ma ta bayyana cewa ko shakka babu itace ta lashe zaben shugaban kasar kuma dan takarar ta Mugan cangarai shine sabon shugaban kasar Zimbabwe kuma ba zasu taba amincewa da duk wani sakamakon zabe da hukumar zaben kasar zata sanar da ya sabama hakan ba, domin ya zuwa yanzu dan takarar su ya samu kashi 50 da digo 3 cikin dari na Adadin kuri'un da aka kada akasar wanda ya zarce Adadin kuri'un da kundin tsarin mulkin kasar yabukaci dan takara ya samu kafin lashe zaben. Don haka suke ganin duk wani jinkiri wajen sanar da sakamakon karshe a hukumance na zaben shugaban kasar yana dora Alamar tambaya dake nuna cewa da dukkan alamu gwamnatin Mugabi tana son tafka magudi da canza alkalum zaben da zai bata damar yin tazarce akaro na 6. to sai dai fitar da wannan sanarwa ke da wuya da Jam'iyar adawa ta kasar tayi sai gwamnatin Mugabi ta fito fili ta karyata wannan zargi kuma ta bayyana cewa wannan sanarwa tamkar riga malama Masallaci ne kamata yayi su dakata a kammala kirga sauran kuri'un da suka rage na sauran mazabun da ba'a riga an kirga ba wanda a nan ne za'a tantance zare acikin abawar sa. Shi kuwa Robet Mugabi shugaban kasar ta Zimbabwe da yake neman wa'adi na 6 na shugabancin kasar da tun kafin fara kada kuri'ar ya bayyyana cewa matukar yana raye tofa babu yadda za'ayi ya mika mulkin ga yan kuran kasashen yamma wato abokin hammayar sa kenan na Jam'iyar MDC Mogan Cangarai. amma sai gashi daga karshe ya nuna cewa a shirye yake ya sauka daga kan karagar mulkin kasar matukar ya sha kaye a zaben shugaban kasar, tun kafin fara zaben shugaban kasar ta Zimbabwe Mogabe ya hana duk wasu masu sa ido na kasashen wajen zuwa kasar sa domin sanya ido kan yadda aka gudanar da zaben inda ya gayyaci wasu kasashen da yake dasawa dasu kawai, wannan mataki ya bakanta ran kasashen turai don haka ne ma suka zargi mugabi da kokarin tafka magudi da harigidon kuri'u shi ya sama ana kammala zaben suka fara kiraye kiraye da a sanar da sakamakon zabe na karshe domin duk wani jinkirin yana nuna kokarin yin magudi ne, Masu fashin bakin lamuran dake gudana a kasar sunyi ammanna cewa irin goyon bayan da Mogan cangarai dan takarar Jam'iyar adawa na kasar ke samu daga kasashen turai da kuma iri halin kunci na tattalin Arziki da Alummar kasar suke ciki ya taimaka soosai wajen bawa jam'iyun adawa samun gagarumar nasara a zaben sakamakon irin Alkawuran da yayi musu na kawo canji da gyara tattalin arziki kasar, Inda farashin kayyakin masarufi ya tashi fiye da kashi 7000 cikin dari to sai dai wasu na ganin yana da kamar wuya Alummar kasar su gani a kasa cikin gaggawa ko da kuwa cangarai ya lashe zaben domin daya daga acikin abinda ake harsashin zaifi bada karfi shine budewa yan mulkin mallaka irin su birtaniya da kawayen ta kofa su dawo kasar su cigaba da cin Karen su bababaka,domin kowa yaci ladan kuturu bazai ki yi masa Aski ba, yanzu dai ana iya ciyewa kasar Zimbabwe ta dauki ciki lokaci ne kawai zai bayyana abinda zata haifa. Musamman bayan gwamnatin kasar ta sanar da sakamakon zaben na karshe a hukumance
Thursday, 10 April 2008 11:40

Sabon Rikici Tsakanin Sudan Da Chadi

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan Ali Assadiq ne ya bayyana hakan a gaban taron manema labarai a birnin Khartum, ya ci gaba da cewa a ranar Talata jiragen yakin kasar chadi sun yi shawagi har sau uku akan yankunan yammacin kasar sudan, inda kuma da safiyar laraba jiragen yaki masu safkar angulu mallakin sojin kasar chadi suka yi ruwan wuta a kan kauyen Ummu kunjub dake yammacin Dafor, kuma suka harba wani makami mai lizzami akan wani sansanin sojin gwamnatin sudan dake kusa da kauyen. Gwamnatin ta sudan ta ce wannan tsokana ce daga bangaren chadi a kanta, kuma hakan yana da matukar hadari, domin tamkar chadin ta sa kafa ne ta shure yarjejeniyar sulhu da aka cimmawa tsakaninta da sudan a watan da ya gabata, a zaman shugabannin kasashen musulmi na kungiyar OIC da aka gudanar a birnin Dakar na kasar Senegal.Bayanin gwamnatin sudan din ya ce a halin yanzu sojin sudan suna ci gaba da yin hakuri da danne zuciyarsu, amma idan hakan ta ci gaba, to zasu mayar da irin martanin da ya dace domin kare kansu da kasarsu daga duk wani shishigi na chadi a kansu.A nata bangaren gwamnatin chadi ta zargi gwamnatin sudan da zuga mayakan ‘yan tawayen kasar wajen kai wasu hare-hare a ranar Talata da ta gabata, a kan garin Adiy dake gabacin kasar Chadi, inda aka kafsa fada tsakanin mayakan ‘yan tawayen da kuma dakarun gwamnatin Chadi, lamarin da dukkanin bangarorin biyu suke ikirarin samun nasara a kansa, amma gwamnatin sudan ta kore wannan zargi.Wannan dai ba shi ne karo na farko da bangarorin biyu suke zargin junansu da marawa bangarorin ‘yan tawayen kasashensu baya ba, amma abun da ya ba kowa mamaki shi ne irin yadda bangarorin biyu suka koma ‘yar gidan jiya ba tare da an je ko ina ba, bayan kulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu wadda kowa ya yi zaton cewa zata taimaka wajen lafawar kura a rikicin da bangarorin biyu ke fama da shi, duk da cewa tun kafin rattaba hannu a kan wannan yarjejeniyar sulhu da shugaban kasar Senegal Abdallah Wad, ya kirayi shugaba Albashir na sudan da kuma shuga Idris Debi na Chadi zuwa gareta, da ma bayan rattaba hannu kan yarjeneiyar, kawancen ‘yan tawayen kasar Chadin ya sanar cewa yarjejeniyar ba ta shafe su, hakan ya shafi gwamnatocin Chadi da sudan ne kawai, amma su zasu ci gaba da gwagwarmaya har sai sun ga bayan gwamnatin da suka kira ta kama karya a Chadi.Wannan bayani da ya fito daga bangaren ‘yan tawayen na Chadi, ya dada sa shakku a kan cewa ko wannan yarjejeniya zata yi tasirin da ya kamata ta yi wajen kawo karshen rikicin ko ba zata yi ba, to amma kuma sake tada jijiyoyin wuwan baya bayan nan tsakanin gwamnatocin Chadi da sudan ya kara tabbatar da cewa da ma wannan yarjejeniya bata wuce kan teburin da aka kulla ta ba.
A ganawar da yayi da kamfanin dillancin labaran kasar Japan Kiyodo a ranar Alhamis data gabata uku ga watan Aprilu shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadi Najad ya jaddada cewa kasarsa bazata amince da duk wani batun tattaunawa kan hakkinta na sarrafa ma'adinin uranium ba, kuma Iran ta riga ta shiga cikin sahun kasashen da suka mallaki fasahar makamashin nukiliya a duniya, don haka babu dalilin da zai sanya a bukaceta data dakatar da shirinta na sarrafa ma'adanin uranium da dokokin kasa da kasa suka tabbatar mata. Wannan bayani na shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadi Najad yazo ne a matsayin mai da martani kan rahotonnin da suke bayyana cewa manyan kasashe da suke membobi ne na din din din a kwamitin sulhun m.d.d. gami da kasar Jamus suna shirin gabatar wa kasar Iran da wasu tarin alkawura na kwadaitawa kan ta amince tayi watsi da shirinta na sarrafa ma'adanin uranium. Wanda Jaridar Washinton Times ta watsa rahoto a watan maris da ya gabata take dauke da cewa Jami'an kasar Amurka dana kasashen yammacin Turai suna shirin gabatar wa kasar Iran da wasu alkawuran kwadaitarwa ta fuskar tattalin arziki, kasuwanci, da bunkasa fasahar shirin makamashin nukiliya matukar Iran din ta amince da bukatar dakatar da shirinta na sarrafa ma'adanin uranium.A hakika matakin da kasashen yammacin Turai suka dauka bisa matsin lamban kasar Amurka na mika shirin makamashin nukiliyan kasar Iran zuwa gaban kwamitin sulhun m.d.d. tare da kakaba mata takunkumi domin ta dakatar da shirinta na sarrafa ma'adanin uranium gami da matakin gabatar wa Iran din tarin alkawuran kwadaitarwa duk dai da nufin ganin ta amince da bukatar yin watsi da hakkinta na sarrafa ma'adanin uranium, matakai ne na siyasa da sukayi hanun riga da dokokin kasa da kasa da suka bawa ko wace kasa a duniya hakkin mallakar fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya ciki har da hakkin sarrafa ma'adanin uranium kamar yadda yarjejjeniyar hana kera makamin nukiliya tare da yaduwansa a duniya ta N.P.T. ta tsara.Don haka matakin da manyan kasashen duniya suka dauka na gabatar wa kasar Iran alkawuran kwadaitarwa ta fuskar tattalin arziki da bunkasa fasahar makamashin nukiliya maras kargo domin Iran din tayi watsi da hakkinta da tsarin dokokin kasa da kasa suka tabbatar mata, mataki ne da yake daidai da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Iran, saboda mataki ne da yake neman sanya kaidi ga al'ummar Iran a kokarin da takeyi na ganin ta bunkasa ci gaban kasarta karkashin tsarin dokokin kasa da kasa.A bisa wannan dalili ne shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadi Najad ya jaddada cewa kasarsa bazata amince da duk wani batun alkawuran kwadaitarwa da za'a gabatar mata ba kan tayi watsi da hakkinta na sarrafa ma'adanin uranium da dokokin kasa da kasa suka tabbatar mata, kuma kasarsa bata da bukatar sake bata lokacinta wajen tattaunawa da wata kasa a duniya kan batun shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya, wanda duk wani zaman tattaunawa da kasar Iran zatayi dangane da batun shirinta na makamashin nukiliya zai takaita ne kawai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya domin itace hukumar dake da hakkin sanya ido kan shirin makamashin nukiliya a duniya.Ita dai kasar Iran tana sarrafa ma'adanin uranium ne da nufin wadata cibiyoyin nukiliyarta na zaman lafiya da makamashin da suke bukata kamar yadda yarjejjeniyar hana kera makamin nukiliya tare da yaduwansa a duniya ta N.P.T. ta tsara kuma kasar Iran tuni ta rattaba hanu kan yarjejjeniyar ta N.P.T. amma duk da haka kasashen yammacin Turai sun zaburo da dukkanin karfinsu domin ganin sun hana kasar ta Iran kaiwa ga hakkinta da dokokin kasa da kasa suka tabbatar mata, ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, sai dai ganin burinsu bazai kai ga samun nasara ba, don haka suka bullo da makircin gabatar wa kasar ta Iran da alkawuran kwadaitarwa, tsammaninsu ta haka ne zasu samu nasarar hana Iran kaiwa ga hakkinta na mallakar cikekkiyar fasahar makamashin nukiliya ta zaman lafiya domin bunkasa ci gaban kasarta
A jiya Talata (8/4/2008) ce aka gudanar da bukin ranar nukiliya a nan Jamhuriyar musulunci ta Iran, Inda shugaban kasar Mahmud Ahmadi Najad ya bayyana cewa cin Nasarar da Kasar Iran tayi na mallakar fasahar nukuliya na zaman lafiya cin Nasarar ne babba, ba kwai ga Alummar Iran ba ga dukkan dan Adam ne baki daya. Bukin da aka gudanar ajiya da yamma a babban dakin taron na gidan Radio da na Talbijin din kasar Iran ya samu halartar manyan baki masana da kwararru, wanda nan ne shugaban iran din ya bayyana irin cigaban da kasar ta samu a bangarorin da suka shafi fasahar nukiliya domin ayyukan zaman lafya , ya cigaba da cewa Al'ummar Iran zasu cigaba da kokarin wajen mallakar fasahar nukikiya da dokokin kasa da kasa suka tabbatar mata babu gudu babu ja da baya, ya cigaba da cewa yana farin cikin shaidawa Alummar Iran dama duniya baki daya cewa Masana da kwararru na kasar Iran sun samu nasarar kafa sabbin na'urorin tace sinadarin yuraniyum har guda 6000 kari akan guda dubu 3000 da ake dashi a tashar nukiliyar ta na Natanz, kuma dukkan su manasana na kasar ne suka samar dasu batare da sa hannu wani daga waje ba, kuma wannan nasarar tazo ne adai dai lokacin da manyan kasashe ma'abota girman kai suke fadi rashi wajen ganin an harmatawa Iran hakkin ta na mallakar fashar nukiliya ta zamani, inda suke zargin Iran da kokarin mallakar makaman kare dangi a agefe guda kuma sune suke kera makaman nukiliya suke siyar dasu ga kasashen duniya . haka zalika shugaban ya zargi kasar Amurka da fakewa da harin 11 ga watan satumba da aka kai a cibiyar kasuwanci da kuma tagwayen gidaje, wajen kaima kasar Afganistan da kuma kasar Iraki harin Soji, inda ya sanya Alamar tambaya game da gaskiyar ruwayar da ka bayar a hukumance game da Jirgin da yakai harin.Shugaban ya bayana cewa kasashe Ma'abota girman kai na duniya bawai suna adawa da makaman kare dangi bane kamar yadda suke riyawa domin idan da da gaske ne to da tuni sun lalata kayukan makaman nukiliya da suka mallaka amma sai gashi sune ke kara ruruta wutar yaki da rikici tsakanin kabilu da A1'umomi a kasashen duniya daban daban, domin tallata makamansu da siyar dasu a kasashen, A yankin nahiyar Afrika ma domin kwadayin sace dinbin dukiyar da Allah ya fuwace musu suna kasashen ma'abota girman kai suan hada fada tsakanin kabilu da hakan ke jawo rasa rayukan dubban mutane da basu san hawaba balle sauka.Haka zalika a lokacin da yayi ishara game da irin barazanar da kasashe ma'abota girman kai sukeyiwa Iran kuwa ya nuna cewa duk wani parpaganda da barazana da sukeyi ta fuskancin tattalin arziki ko siyasa kan kasar Iran ba zai kai ga cin nasara ba domin kuwa Al'ummar Iran bisa dogaro da karfin Allah zasu murkushe duk wani makirci dazasu kulla, domin na gaba yayi gaba na baya sai labari. To sai dai jim kadan bayan da shugaban kasar Iran Mahmud Ahamadi Najjad ya sanar da cigaban da kasar Iran tadin samu ajiya na kafa sabbin na'urorin tace sinadarin uraniyom har guda 6000 a tashar nukiliyar ta dake Natanz sai gashi kasashen Amurka, Faransa da Birtaniya sun fito fili sun nuna bacin ransau game da wanan bayani inda ministan harkokin wajen faran sa a jiya yayi kira da a kara mastin lamba kan kasar Iran wajen yin aiki da takunkumin tattalin Arziki da aka kakaba mata. Domin wannan sanarwa ya kamata ta zama ta farkar dasu ne game da irin mataken da ya kamata su dauka ne kan iran, yayin da shi kuma jakadan kasar Amurka a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya nuna cewa hakika wannan sanarwar tana kara bayyan irin kunne uwar shegu da kasar Iran tayi ne game da kiraye - kirayen da duniya takeyi mata nata dakatar da shirin ta na nukiliya, sai dai a bangare kasar Rasha kuwa ministan harkokin wajen ta Sargi Lavrof bayyanawa yayi cewa a halin yanzu babu wani batun kara kakabawa Iran wani sabon ta kunkumi kamata yayi acigaba da bin hanyoyin diplomasiyya wajen ganin an warware takaddama dake tsakani kan batun domin duk wani matakin soji zai kara dagula yankin gabas ta tsakaiya ne wanda abinda zai biyo baya ba zai yiwa kowa dadi ba, To sai dai daga karshe shugaban kasar Iran a lokacin da yake kammala Jawabin sa a wajen taron ya nuna cewa canza wannan yanayi da ake ciki da samar da hanyar dacewa ga dan Adam shine bin Addinan da Annabawan Allah suka zo dashi sau da kafa, da kuma bayyanar kammalallan mutum da Allah ya zaba kuma yayi alkawarin tattabar da Adalci da gaskiya adoron duniya bayan ta cika da zalunci da rashin adalci, dakuma gushewar zalunci da azzalumai.
Rahotonni da suke fitowa daga kasar Masar suna nuni da cewa zaben kananan hukumomi da aka gudanar a kasar a jiya bai yi armashi ba sakamakon rashin fitowar Jama'a saboda kaurace wa zaben da wasu manyan jam'iyyun siyasa kasar Masar din suka yi. Kungiyoyin kare hakki bil-Adama sun bayyana cewa 'yan sandan kasar Masar sun hana masu sanya ido da suke zaman kansu da kungiyoyin kare hakkin bil Adama isa zuwa wajajen da ake kada kuri'ar. Mutane sun kauracewa zabukan kananan hukumomin ne sakamakon kaurace wa zaben da kungiyar 'yan uwa musulmai ta Muslim Brotherhood tayi ne saboda gwamnatin kasar ta hana membobinta da dama tsayawa takarar.A yau Laraba ne dai ake sa-ran za'a bayyana sakamakon zaben wanda Jam'iyya mai mulki a kasar zata lashe mafi yawan kujerun ba tare da hamayya ba
Gwamnatin kasar Libiya ta bada sanarwar sakin mutane casa'in daga cikin 'yan kungiyar Alqa'ida da suke dauke da makamai a kasar da take tsare dasu a gidajen kurkukunta. Cibiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Ghazzafi ta fitar da bayani a birnin Tarabulus fadar mulkin kasar Libiya cewa bayan zaman tattaunawa da aka gudanar tsakanin Jami'an cibiyar da wakilan 'yan kungiyar ta Alqa'ida a watan Fabrairun da ya gabata an cimma yarjejjeniyar sakin 'yan kungiyar ta Alqa'ida da suke dauke da makamai su casa'in wato kashi daya cikin uku na wadanda ake tsare dasu a gidajen kurkukun kasar, kuma mahukunta a kasar ta Libiya a shirye suke su kara sakin wasu daga cikin 'yan Alqa'idan anan gaba.A farko farkon shekara ta 1990 ne dai wasu 'yan kasar Libiya suka kai dauki zuwa kasar Afganistan da nufin yaki da tsohuwar tarayyar Soviet data mamaye kasar ta Afganistan wanda suka ci gaba da zama a kasar bayan janyewar rundunar Sojin tsohuwar tarayyar ta Soviet, sannan a shekara ta 1995 suka bayyana samuwarsu a matsayin kungiya da take yaki domin kafa gwamnatin musulunci a kasar Libiya, wanda a shekara ta 2007 kungiyar ta bada sanarwar hadewarta da kungiyar Alqa'ida ta Usamah bn Ladan karkashin jagorancin Abu-Laisi Allibi da aka halakashi a kasar Pakistan a watan Fabrairun wannan shekara
'Yan takaran neman shugabancin kasar Amurka karkashin jam'iyyar dimocrate Hillary Clinton da Barak Obamah sun kara bayyana matsayinsu na yin suka kan matakin ci gaba da jibge sojojin mamayan Amurka a kasar Iraki. A zantawar da tayi da tashar talvijin din I.B.S. a jiya Talata 'Yar takarar neman shugabancin kasar Amurka karkashin jam'iyyar dimocrate Hillary Clinton ta jaddada cewa matakin soji ba shi ne zai warware rikicin kasar Iraki ba, kuma matukar ta samu nasarar dare kan karagar mulkin kasar Amurka zata dauki matakin janye sojojin Amurka daga kasar ta Iraki, Clinton ta kuma bayyana kara yawan sojojin Amurka a Iraki da cewa babu abin da ya tsinana domin har yanzu ana ci gaba da samun tashe tashen hankula a kasar ta Iraki.Anashi bangaren Barak Obamah ya bayyana cewa sojojin Amurka bazasu zauna har abada ba a kasar Iraki, domin ci gaba da mamaye kasar ta Iraki na tsawon lokaci bazai taba haifar da Da mai ido ba ga kasar Amurka ta fuskar Soji dana tattalin arziki. Wannan suka na Hellary Clinton da Barak Obamah sun zo ne a jiya Talata a daidai lokacin da babban kwamandan rundunar sojin mamayan Amurka a kasar Iraki da Jakadan Amurka a kasar suke bada bahasi a gaban majalisar dokokin kasar Amurka kan halin da ake ciki a kasar Iraki da Amurka ke mamaye da ita tsawon shekaru biyar.
Mutane tara ne suka jikkata a farkon harin kunan bakin wake da aka kai kan dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika dake kasar Somaliya tun bayan kawar da jagororin 'yan kotunan shari'ar Musulunci na kasar. Kakakin rundunar sojin kasar Burundi dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya karkashin dakarun kungiyar tarayyar Afrika ya bayyana cewa wani Dan kunan bakin wake da ya cika wata mota da bama bamai ya tunkari kofar sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika dake Magadisho fadar mulkin kasar Somaliya wanda motar ta gwambari kofar shiga sansanin da haka yayi sanadiyyan tarwatsewarta tare da mutuwar fararen hula bakwai da sojoji biyu.Kungiyar Samari ta Mujahideen dake karkashin kungiyar kotunan musulunci ta dauki alhakin kai harin, kuma daya daga cikin manyan Jami'an kungiyar Samari ta Mujahideen Mukhtar Rumobo ya bayyanawa manema labarai cewa an kai harin kunan bakin waken ne da wata karamar motar bus da suka makareta da bama bamai, kuma sunyi niyyar kai harin ne kan dakarun kungiyar tarayyar Afrika da sukazo kasar ta Somaliya domin taimakawa sojojin mamayan kasar Ethopiya da suka mamaye kasar a watan maris din shekara ta 2007 data gabata
Page 2063 of 2063