An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Labarai
Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci Gwamnatin Tchadi da ta yi gaskiya wajen kilga kuri'un da aka kada na zaben shugaban kasa.
Kimanin Mutane 5 ne suka rasa rayukansu sannan kuma wasu 7 suka jikkata sanadiyar tashin wata Mota shake da bama-bama a gaban ofishin Gwamnatin kasar Somaliya dake birnin Magadushu.
Ma'aikatar cikin Gidan Jamus ta sanar da cewa a shekarar 2015 kimanin 'yan gudun hijra masu karamcin shekaru 5800 ne suka yi batan laya a kasar
Wasu daga cikin sojojin 'yan tawayen Sudan ta kudu sun shiga birnin Juba fadar mulkin kasar a yau, bisa yarjejeniyar sulhu da aka cimmawa a tsakaninsu da bangaren gwamnati.
Shugaban majalisar kungiyar tarayyar turai ya fadi a yau cewa, tun bayan da fira ministan kasar Arseniy Yatsenyuk ya yi murabus, kasar ta kara shiga cikin wani hali na rashin tabbas.
Babban manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Syria Staffan de Mistura ya gana da jami'an gwamnatin Syria a yau a birnin Damascus.
Shugaban kasar Kazakhstan Nur Sultan Nazarbayev ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a yau a birnin Tehran, domin bunkasa alaka da kasar Iran a dukkanin bangarori.
Jami'an 'yan sanda na farautar wanu mutum da ya kai hari a jiya a kan wata makarantar muuslmi a garin malmo da ke kudancin kasar.
Yan adawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congon sun jaddada goyon bayansu ga kudurin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan kasarsu musamman kiran da ya yi kan gudanar da zaben shugaban kasa a kan lokaci.
Asusun Kula da Mata da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya {UNICEF} ya bayyana cewa; Yawan kananan yara da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin masarautar Saudiyya suke kai wa kan kasar Yamen sun haura 900 a cikin shekarar ta da gabata ta 2015.
Page 2 of 2063