An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Labarai
Mujallar barkwanci ta kasar Faransa Charlie Hebdo ta yi dirar mikiya kan msuulmin nahiyar turai, makonni biyu bayan kai harin ta'addanci a birnin Brussels na kasar Belgium.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce kimanin mutane miliyan 19 daga cikin mutane kimanin miliyan 24 na kasar Yemen suna bukatar taimako, yayin da miliyan 14 kuma suke da bukatar taimako da ya hada har da bangaren kiwon lafiya, sakamakon yakin da Saudyya ta kaddamar kan kasar.
Ma'aikatar tsaron kasar Amurka, Pentagon, ta sanar da tusa keyar wasu 'yan kasar Libiya su biyu da sojojin Amurkan suke tsare da su a gidan yarin nan na Guantanamo da ke kasar Cuba na tsawon shekaru zuwa kasar Senegal don ci gaba da tsare su a can.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tura wasu dakarun sojojinta na kasa na musamman zuwa kasar Siriya a ci gaba da taimakon da Iran take ba wa sojojin Siriya a fadar da suke yi da kungiyoyin ta'addancin da aka shigo da su kasar daga kasashen duniya daban-daban.
A ci gaba da fatattakan mayakan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) da kuma nesata su daga kasar Labanon, dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar sun kai wasu munanan hare-hare a kan sansanonin 'yan kungiyar ta'addancin a yankunan da suke gabashin kasar ta Labanon.
Jami'an gwamnatocin kasashe da 'yan siyasa daban-daban na duniya suna ci gaba da mayar da martani da mafi girman tonon silili da bayyanar da takardun bayanan sirri da ke bayanin yadda wasu wasu attajirai da manyan masu fada aji na duniya ke boye dukiyoyinsu don guje wa haraji.
'Yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran sun sake jaddada goyon bayansu ga shirin makamai masu linzami na kariya na kasar suna masu yin watsi da ihuce-ihuce da wasu kasashe suke yi kan wannan shiri na Iran.
Wakilin Saktaren MDD kan 'yan gudin hijra ya ce mayar da 'yan gudun hijra zuwa kasar Turkiya ya sabawa dokar kasa da kasa
Al'ummar babban birnin Congo sun wayi gari cikin tashin hankali na musayar wuta tsakanin 'yan tawaye da jami'an 'yan sanda
Wasu 'yan bindiga sun bindige wani babban jami'in ma'aikatar leken asiri na kasar Somaliya