An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 08 March 2016 05:26

Zaben Shugaban Kasar Benin

Zaben Shugaban Kasar Benin
A Ranar Lahadin da ta gabata ce Al'ummar kasar Benin suka kada Kurunsu na zaben sabon Shugaban kasa da zai maye gurbin Boni Yayi.

Kimanin 'Yan kasar miliyan 4 da dubu dari takwas ne suka cancanci kada kuri'ar, inda 'yan takara 33 suka fafata a zaben da ya gabata, kamar yadda yake a wasu kasashe, babbar kotun kare kundin tsarin milkin kasar ce ke da hurumin tattance 'yan takarar shugaban kasar, a wannan karo 'yan takara 48 ne suka ajiye takardunsu na neman tsayawa takarar shugaban kasar inda kotun ta tantance Mutane 33 daga cikin su, bayan da ta yi watsi da takardun 'yan takara 15 saboda rashin cikin ka'idodin da ya kamata ace sun cika.kamar yadda yake a kundin tsarin milkin kasar shugaba na da izinin tsayawa takarar shugabanin kasar har so biyu, bayan ga haka doka ba ta bashi izinin tsarcewa ba, da hakan ya sanya shugaba Boni Yayi da wa'adin milkinsa zai kare a ranar 6 ga watan Avrilu mai kamawa bai tsaya takarar shugabancin kasar ba.wannan mataki da shugaba ya yi ya dauka abin a yaba ne saboda wasu daga shugabanin kasashen Afirka idan wa'adinsu ya kare su kan yi wa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima da zai ba su damar ci gaba da dawwama a kan karagar milki.

daga shahararun 'yan takarar da aka ganin za su lashe zaben, Firaminista Liknel Zinsou da ke da goyon bayan shugaban kasar mai barin gado Boni Yayi , yayin da yake gudanar da yakin neman zabensa ,mista Zinsou ya yi alkawarin inganta harakokin Noma da samarwa matasan kasar aiki yi .saidai ya fuskanci caccaka daga abokin hamayarsa saboda a cewarsu mista Zinsou siyasarsa da kuma al'adunsa ya dogara ne katsokau ga kasar Faransa domin mafi yawan rayuwar sa ya gudanar da ita ne a kasar Faransa, kuma a halin da ake ciki Mista Zinsou nada Pasport din kasashen Faransa da Benin baya ga haka jawabin da ya gabatar na shekarar 2011, inda ya ce Nahiyar Afirka ta dogara da tarayyar turai , ya kasance babban makami ga 'yan adawar wajen ceccekarsa a yayin yakin neman zaben.

Baya ga Mista Liknel Zinsou, Dan takarar da ake ga ya taka muhimiyar rawa a wannan zabe shine Houngbedji Dan takarar babbar jam'iyar adawar kasar da magoya bayansa ke ganin cewa idan ya lashe zaben zai sabunta tafarkin democradiyar kasar.

A yayin yakin Neman zaben, 'yan takarar sun fi meda hankalinsu ne kan batun samar da ayyukan yi ga Matasa,yaki da masu bata dukiyar Gwamnati, inganta harakokin kiyon Lafiya da Noma.

A halin da aka cikin Jam'iya mai milki ta fi yawan kujeru a Majalisar dokokin kasar, inda su keda kujeru 41 daga cikin kujeru 83 da Majalisar dokokin ke da ita, su kuma gamayar jam'iyun adawa mai suna Amana sun samu kujeru 33 sai kuma kananen Jam'iyun dake goyawa Gwamnati baya suka samu kujeru 9 a zaben 'yan Majalisun da ya gudana a shearar da ta gabata.

Yanzu haka dai 'yan kasar na dakon sakamakon zaben inda ake sa ran Firaministan kasar zai Lashe zaben. saidai idan babu dan takarar da ya samu kashi 50% to wajibi ne a gudanar da zaben zagaye na biyu tsakanin 'yan takarar da suka samu nasarar matsayin farko da na biyu a ranar 20 ga wannan wata na Maris da muke ciki.

Add comment


Security code
Refresh