An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 06 March 2016 05:50

Ziyarar Firayi Ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu, Zuwa Iran

Ziyarar Firayi Ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu, Zuwa Iran
A daren shekaran jiya Juma'a ne firayi ministan kasar Turkiyya Ahmet Davutoglu tare da wata babbar tawaga ta 'yan siyasa da 'yan kasuwa ya iso nan Tehran, inda a jiya Asabar ya gana da shugaban kasar Iran da mataimakinsa bugu da kari kan wasu manyan 'yan kasuwa na kasar.

A ganawar da yayi da firayi ministan na Turkiyya a yammacin jiya Asabar, shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar wajibi ne kasashen Iran da Turkiyya su hada kai waje guda don fada da ta'addanci a matsayinsa na babbar ga dukkanin al'ummomi wanda yin hakan zai taimaka wajen tabbatar da tushen sulhu da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya. Shugaba Ruhani ya kara da cewa kasashen waje dai ba da gaske suke yi kuma ma ba a shirye suke su magance matsalolin da yankin Gabas ta tsakiya take fuskanta face dai babban abin da ya fi damunsu shi ne cimma manufofinsu. Don haka sai shugaba Ruhani yayi kiran da a yi amfani da damar da aka samu wajen fadada alakar da ke tsakanin kasashen biyu don amfanuwar dukkanin bangarorin.

Shi ma a nasa bangaren firayi ministan kasar Turkiyyan Ahmet Davutoglu ya bayyana cewar kasarsa ta kuduri aniyar bude sabon shafi a fagen alakarta da Iran a dukkanin fagage.

Tun da fari dai firayi ministan na Turkiyya ya fara ziyarar tasa ne da ganawa da mataimakin shugaban kasar ta Iran Ishaq Jihangiri wanda ya bayyana fatan cewa wannan ziyarar da kuma abubuwan da za a tattauna kansu za ta kasance mafarin kara kyautatuwar alaka tsakanin kasashen biyu. Mataimakin shugaban na Iran ya kara da cewa duk da akwai bambancin mahanga tsakanin Iran da Turkiyya kan wasu batutuwa da suka shafin yankin Gabas ta tsakiya, to amma wajibi ne a bi ta hanyoyin da suka dace wajen magance su.

Shi ma a nasa bangaren firayi ministan Turkiyya ya ce kasarsa a shirye take ta aikata duk wani abin da zai taimaka wajen kara karfafa alakar da ke tsakaninta da Iran.

Kasashen Iran da Turkiyya dai suna kokari ne wajen karfafa alaka ta tattalin arziki da kasuwanci da ke tsakaninsu ta yadda musayen kayayyaki na kasuwanci tsakanin kasashen biyu zai iya karuwa har zuwa dala biliyan 30, wanda hakan yana daga cikin manufofin wannan ziyara ta firayi ministan kasar Turkiyyan a daidai wannan lokaci da kasashen biyu suke ci gaba da yin tururuwa zuwa kasar Iran bayan cimma yarjejeniyar nukiliyar da ta gudana tsakanin kasar Iran da manyan kasashen duniya da kuma dauke wa kasar takunkumin da aka sanya mata dangane da shirin nukiliyanta na zaman lafiya.

Add comment


Security code
Refresh