An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 04 March 2016 05:45

Karshen Taron Koli Na Kungiyar Kasashen Gabashin Afrika EAC Karo Na 17

Karshen Taron Koli Na Kungiyar Kasashen Gabashin Afrika EAC Karo Na 17
A ranar Larabar data gabata ce aka rufe taron koli na kungiyar kawancen kasashen gabashin Afrika EAC a birnin Arusha dake arewacin kasar Tanzaniya.

Taron wanda shi ne karo na 17 ya samu halartar shugabannin kasashen Tanzaniya, Kenya, Uganda da kuma Ruwanda .

Daga cikin batutuwa da taron ya maida hankali akwai bukatar kasar Sudan ta kudu na zama mamba a kungiyar da kuma rikicin kasar Burundi, baya ga hakan kuma akwai batun nada sabon shugaban karba-karba da kungiyar.

Saidai a wannan karo saboda ganin mawuyancin hali da kasar Burundi ke ciki a halin yanzu, taron ya yanke shawarar tsawaita wa'adin shugabancin kasar Tanzaniya John Magufuli zuwa shekarar 2017.

kazalika shugabanin kasashen mambobin kungiyar sun nada tsohon shugaban kasar ta Tanzaniya Benjamin Mkapa a matsayin mai shiga tsakani a rikicin siyasa kasar Burundi.

Nauyin da kungiyar ta dorawa Mr Mkapa shi ne tattaunawa da dukkan 'yan siyasa kasar ta Burundi domin samun mafita a rikicin kasar da yaki-ci yaki cinyewa.

tunda farko dai shugaban kasar Uganda ne Yoweri Museveni ke rike da mukamin, koda yake kungiyar ta ce har yanzu shi ne mai maganar karshe a shiga tsakanin rikicin kasar ta Burundi.

Rikicin Burundi dai ya kara dagulewa ne tun bayan da masu mulki a wannan kasa suka ki amuncewa da zaunawa tanurin tattaunawa da 'yan adawa, da kuma tsaiko da aka samu a kwanakin baya kasancewar mai shiga tsakanin a rikicin Yoweri Museveni bai samu dama sosai ba saboda shirye-shiryen zaben shugaban kasar sa daya gabata.

Kasar Burundi dai ta yi marhabin da ayyana sabon mai shiga tsakani da nufin taimakon warware rikicin kasar.

babbar jam'iya mai milki a kasar Burundi ta yi marhabin da nada tsohon shugaban kasar Tananiya Benjamin William Mkapa a matsayin sabon shugaban gungun da za su taimaka wajen warware rikicin kasar.

Tun bayan da shugaba Pierre Nkurinziza ya bayyana aniyarsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar a farkon watan Avrilun shekarar da ta gabata, aka fara fuskatan rikici a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar lakume rayukan mutane kimanin 400 yayin da wasu sama da dubu 240 na daban suka bar mahalinsu.

A hannu daya kuma shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli mai rike da shugabancin karba-karba na kungiyar ya sanar a taron cewar, kungiyar ta shigar da kasar Sudan ta kudu don zama mambarta ta shida.

Sudan ta kudu ta gabatar da bukatarta ta shiga kunigyar ne, bayan da ta samu 'yancin kanta a shekarar 2011, daga bisani kungiyar ta kafa wani kwamitin ministoci don yi mata bincike.

Kungiyar kasashen da ke yankin gabashin Afrika EAC ta karbi sabuwar kasar Sudan ta kudu a matsayin mamba a kungiyar da ke bunkasa dangantaka da kuma kasuwanci tsakanin mambobin ta.

kungiyar da ke da cibiya a birnin Arusha na kasar Tanzaniya yanzu dai ta kunshi mambobi shida da suka hada da Burundi da Kenya da Rwanda da Tanzania da Uganda, wanda a jimilce yawan al'ummar kasashen suka tasa sama da miliyan 150.

Sudan ta Kudu wadda ta sami 'yancin kai a shekarar 2011 daga Sudan, ta fada cikin rikici ne a watan Disamba ne shekara 2013 bayan da shugaban kasar Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakin sa Riak Machar da yunkurin kifar da mulkin sa, al’amarin da ya kai ga rasa rayukan dubban mutane tare da tilasta wa sama da miliyan 2,3 tserewa daga gidajensu, baya ga ragargaza tattalin arzikin kasar da karya darajar kudin ta, tare da haifar da koma baya a arzikin man fetur kin da Allah ya hore mata.

Add comment


Security code
Refresh