An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 02 March 2016 05:21

Mahangar Tsaigaita Wuta A Kasar Siriya

Mahangar Tsaigaita Wuta A Kasar Siriya
A yayin da tsagaita wuta a kasar Siriya Ya shiga cikin kwanakinsa na biyar, Al'ummar Siriya na da kyakyawan fata dangane da wannan yarjejeniya.

A ranar Assabar da ta gabata ce aka fara gudanar da yarjejjniyar tsakaita wuta, inda Al'ummar kasar da yaki ya daidaita suke da kyakyautar fata dangane da wannan batu, ko baya ga Al'ummar Siriyan, Kasashen Rasha da Amurka sun yaba da yadda yarjejjeniyar ke gudana. tsakaita wutar siriyan ta gudana ne bisa cimma yarjejjeniya tsakanin magabatan washinton da Masco, duk da irin konkonton dake ciki, Al'ummar kasar Siriya nada kyakyawan fata na dorewa da wannan yarjejjeniya. A cewar Stephan Dymistura wakilin musaman na babban saktaren Majalisar dinkin Duniya kan kasar Siriya, duk wasu hare-hare da aka zata a yayin gudanar da tsakaita wuta bai wakana ba, saidai aiyukan ta'addancin da kungiyoyin ISIS da Jabhatu Nusra ke yi babbar barazana ce ga yarjejjeniyar tsakaita wutar.

A nasa bangare babban sakataren Majalisar Dinklin Duniya Banki Moon ya bayyana cewa tsagaita wuta a kasar ta Siriya gudiri ne da duniya ta dauka,kuma duk da irin matslolin da aka samu da wasu gurare, har yanzu tsakita wutar na tsaye da kafafuwanta.

Banki Moon ya ce a tsawon shekaru biyar da suka gabata an yi ta kokarin gudanar da yarjejjeniyar tsagita wuta a kasar ta Siriya amma batun ya cutura, saboda kafin aje ko ina ake cin karo da matsalar karya yarjejjeniyar, amma a wannan karo muna kyakyawan fata na cewa yarjejjeniyar za ta dore domin share fage na fara tattaunawa tsakanin Gwamnatin Siriya da bangaren 'yan adawa a ranar 7 ga wannan wata na Maris da muke ciki.

Tsakaita wutar Siriya ba ta shafi kungiyoyin 'yan ta'addar ISIS da jabhatu Nusra ba, domin haka ne ma Jiragen yakin Rasha da na Siriya ke ci gaba da kai hare-hare ta sama kan guraren da wadannan kungiyoyi na ta'addanci ke rike da su.

matakin da magatan Damuscus tare da na Rasha suka dauka wajen yaki da 'yan ta'adda a kasar ya yiwa 'yan adawa masu samun goyon bayan kasashen Saudiya, Qatar, Turkiya da Amurka ya yi musu tsauri sosai,wajen tabbatar da yarjejjeniyar tsakaita wuta a kasar.

kungiyoyin 'yan tawayen da masu goya masu baya na zarkin magabatan Damuscus da Masco da amfani ta hanyar siyasa wajen cimma manufofinsu a yarjejjeniyar tsakaita wuta.

A halin yanzu Kasashen Duniya na iya kokarinsu wajen ganin an magance rikicin kasar Siriyan da ya kwashe shekaru biyar, bisa kudiri mai lamba 2254 na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya.

A halin yanzu tuni dai Al'ummar Siriyan sun fara amfana da wannan yarjejjniyar, inda kungiyoyin Agajin Duniya suka fara kai Agaji a yankunan dake cikin mawuyacin hali, kuma nan gaba za a gudanar da zabe cikin 'yanci da aminci domin Al'ummar kasar su zabi abinda ya fi dacewa da su da kuma makomar shugaba Bashar Al'asad.

 

Add comment


Security code
Refresh