An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 29 February 2016 05:36

Hadin Gwiwan Saudiyya-Isra'ila Da Nufin Kifar Da Gwamnatin Siriya

Hadin Gwiwan Saudiyya-Isra'ila Da Nufin Kifar Da Gwamnatin Siriya
A daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin tsagaita wuta da kawo karshen rikicin kasar Siriya, a bangare guda kuma kasar Saudiyya da H.K. Isra'ila suna ci gaba da kokarin da suke yi wajen ganin sun kawar da shugaban kasar Siriyan daga kan karagar mulkin kasar.

Jim kadan bayan sanar da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar Siriya da aka cimma tsakanin Amurka da Rasha, wasu kafafen watsa labaran sun ba da rahoton kan ziyarar da wasu manyan jami'an Saudiyya suka kai H.K. Isra'ila a boye da nufin tsara hanyoyin da za su bi wajen cimma manufofinsu a Siriyan.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya ba da rahoton kan wata ziyara ta sirri da ministan harkokin wajen Saudiyya Adil Al-Jibair da shugaban hukumar leken asirin Saudiyyan Khalid al-Hamidan suka kai Tel'Aviv don ganawa da manyan jami'an HKI ciki kuwa har da firayi minista Benjamin Netanyahu da shugaban kungiyar leken asirin Isra'ilan (MOSSAD). Rahoton ya kara da cewa babbar manufar wannan ziyara ta jami'an Saudiyyan ita ce rokon jami'an yahudawan su kaddamar da harin soji ta sama kai tsaye Kudancin Siriya a daidai lokacin da su kuma Saudiyya suke shirin fara kai hari ta kasa, duk dai da nufin kara matsin lamba kan gwamnatin Siriyan.

A makon da ya wuce ma dai jarifar Financial Times ta kasar Ingila ta rubuta cewa Saudiyya da taimakon kasar Turkiyya suna shirin kaddamar da wasu hare-haren soji cikin kasar Siriyan.

Gwamnatocin Saudiyya da Turkiyya sun jima suna ta maganar wajibcin kawar da shugaba Basshar al-Asad daga mulkin kasar Siriya da karfin tuwo ba tare da riko da hanyoyi na siyasa da tattaunawa ta sulhu ba. Hakan kuwa wani lamari ne da tun da jimawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi na'am da shi, sannan kuma tana ganinsa a matsayin wani shiri da ta jima tana da shi, wanda hakan a tunaninta zai kawo mata karshen babbar barazanar da take fuskanta, musamman ganin irin rawar da gwamnatin Siriya take takawa a fagen karfafa kungiyoyin gwagwarmaya na kasashen larabawa masu neman kwato kansu daga mamaya da kuma barazanar yahudawan sahyoniya.

Wannan ziyara ta manyan jami'an Saudiyya zuwa Isra'ila, da kuma maganar sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry na baya-bayan nan da yake cewa Amurka tana da wata hanyar ta daban ta magance rikicin Siriya matukar yarjejeniyar tsagaita wutar ta gagara kai wa ga gaci, wasu batutuwa ne guda biyu da suke nuni da wani sabon makircin da wannan sansani na larabawa-Turawan yamma karkashin jagorancin Amurka da Saudiyya suke da shi a kan al'ummar Siriyan.

Masana dai suna ganin daya daga cikin hanyoyin da Amurkawa da kawayensu na larabawa suke da shi, idan har yarjejeniyar tsagaita wutar ba ta haifar da da mai ido ba, shi ne kaddamar da harin soji. Abu na biyu kuma wanda shi ma ba za a iya kore shi ba, shi ne kokarin da suke yi wajen karfafa kungiyoyin 'yan ta'adda a bangarori daban-daban na kasar Siriya musamman a kudancin kasar a yankin Jorlan, a daidai lokacin da ake ci gaba da aiwatar da shirin tsagaita wutan ma, wanda ake ganin daya daga cikin manufofin ziyarar manyan jami'an Saudiyyan zuwa H.K.Isra'ila shi ne wannan batu na karfafa 'yan ta'addan.

To sai dai da dama daga cikin masanan suna ganin, cimma wannan manufar musamman batun kawar da shugaba Asad daga karagar mulki ba zai zamanto cikin sauki ba ga wadannan kasashe bisa la'akari da kokari makamancin hakan da suka yi tsawon shekaru biyar din da suka gabata amma sun gaza wajen kifar da gwamnatin Siriyan.

Add comment


Security code
Refresh