An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 28 February 2016 05:40

Mece Ce Manufar Hare-Haren Amurka A Libya?

Mece Ce Manufar Hare-Haren Amurka A Libya?
A ranar Juma’a da ta gabata ce jiragen yakin Amurka suka kaddamar da wasu hare-hare kan birnin Sabrata na kasar Libya, inda suka kasha wasu daga cikin mayakan kungiyar Daesh (ISIS) da suka kwace iko da birnin.

Wadannan hare-hare na Amurka dai sun zo ne a matsayin wani riga malam masallaci, a shirin da kasashen turai suke da shi na kaddamar da hari kan kasar Libya da sunan yaki da kungiyar Daesh, wadda ta mamaye wasu daga cikin yankunan gabashin kasar Libya, da suka hada da wasu yankuna da suke da arzikin danyen man fetur da iskar gas.

Sai dai abin tambaya a nan shi ne, mene ne dalilin da yasa hare-haren na Amurka suka takaita kawai a kan Sabrata? alhali kuwa akwai wasu wuraren da Daesh ta kame tun fiye da shekara guda da ta gabata musamman birnin Sirte, wanda shi ne birni na uku a kasar Libya bayan Tripoli da Benghazi, wanda kuma nan mahaifar tsohon jagoran kasar marigayi kanar Gaddafi.

Wadanda suke da cikakkiyar masaniya kan abin da yake faruwa a kasar Libya suna bayyana cewa, ‘yan ta’addan da suke rike da birnin sabrata sun hada har da wadanda Amurka take zargi da kai hare-hare kan ofishin jakadancinta a Benghazi, tare da kashe jakadanta Chris Stevens a cikin watan Mayun 2012.

Wannan ya sanya wasu masana yin shakku kan manufar Amurka ta kai hare-haren riga malam masallaci a kan birnin Sabrata, inda suke ganin cewa hakan ba shi da wata alaka da yaki da kungiyar ISIS, domin kuwa da haka ne, to da ya kamata Amurka ta fara kai hari ne kan birnin Sirte, wanda ya zama babbar tungar ‘yan ta’addan ISIS a kasar ta Libya.

A kan haka masu wanann ra’ayi ke ganin cewa manufar kai harin ita ce daukar fansa kan kisan Amurkawan da aka yi da suka hada da jakadan Amurka a shekara ta 2012, ba murkushe ISIS ko tabbatar da tsaro kan iyakokin kasar Libya da Tunisia ba kamar yadda Amurka ta shelanta.

Kuma har wala yau masu wannan ra’ayi suna kara danganta shakkun nasu a kan ikirarin da Amurka take yi na yaki da kungiyar ta ISIS a kasashen Syria da Iraki, domin kuwa tun bayan da ta kafa kawancen kasashe fiye da kasashe 40 domin yaki da ISIS, har yanzu kawancen Amurka bai kwato ko daya daga cikin garuruwan da ISIS take iko da su a Iraki da Syria ba, kamar yadda Amurka ba ta taba kaddamar da wani farmaki na a zo gani kan birnin mausil na Iraki ko Raqqah na kasar Syria ba, wadanda su ne manyan muhimman wurare da suke a hannun kungiyar a cikin kasashen Syria da Iraki, kamar yadda birnin 3 a Libya wato Sirte yake a hannun a halin yanzu.

Ko shakka babu kafa kungiyoyin ‘yan ta’adda ta hanyar yin amfani da kasashe da suke yada akidar nan ta kafirta musulmi tare da rarraba kansu da kuma hada su fadace-fadace saboda banbancin fahimta, babbar manufar hakan ita ce tarwatsa kasashen musulmi tare da raunana su, domin kuwa wadannan kuniyoyi na ‘yan ta’adda dukkanin ayyukansu sun kare ne a kan kasashen musulmi, kamar yadda kuma hakan ya zama wata hanya mafi sauki wajen bata sunan musulunci da musulmi a idon duniya, babban abin takaicin shi ne yadda kasashen da suka fi kowa zakewa wajen bayyana kansu a matsayin jagororn musulmi a duniya, suka zama kuma su ne kan gaba wajen aiwatar da wannan bakar manufa ta makiya musulunci a duniya, da yin amfani da kudaden man fetur da suke sayarwa domin kawai su dadawa Amurka da sauran kasashen yammacin turai.

 

Add comment


Security code
Refresh