An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 27 February 2016 06:05

Zaben Nijar 2016 : Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasa

Zaben Nijar 2016 : Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasa
A jamhuriya Nijar, bayan shafe kusan kwananki biyar na dakon sakamakon zabe, yanzu dai ta tabbata cewa za'a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a ranakun Lahadi da Litinin.

Sakamakon da hukumar ta CENI ta fitar da yammacin jiya Juma'a, ya nuna cewa babu wani dan takara da ya samu sama da kaso 50% na kuri'un da aka kada, duk da cewa shugaba Alh. Mahamadu Issufou mai barin gado na kan gaba da tazara mai yawa, amma bai samu adadin kason da ake bukata ba da zai ba shi damar lashe zaben kai tsaye.

Issufou mai shekaru 63 ya samu kashi 48.41 %, yayin da yake neman wa’adi na biyu domin ci gaba da zama akan karagar mulki.

Jim kadan bayan sanar da sakamakon Shugaban kasar Nijar kuma dan takara a zagaye na biyu wato Issufou Mahamadou yayi jawabi inda ya jinjina wa abokan hamayyarsa da hukumar zabe.

Shugaba Mahamadu Isufu ya kara da cewa lalle yayi hasashen lashe zaben tun zagayen farko, saidai a cewar sa Allah bai tabbatar da hakan ba, aman yayi murna sosai da sakamakon da ya samu cikin 'yan takara 14 wanda yace abun jinjinawa ne don babu tamakar sa.

Dan takara jam'iyyar Moden Lumana, Mal. Hama Amadu kana tsohon firaministan kasar wanda ke garkame a gidan kurkuku bisa zargin safara jarirai, shi ne ya zo na biyu a zaben inda ya samu kashi 17.41% a zagayen farko yayin da zai sake karawa da Issoufou a cikin watan Maris mai zuwa.

Tun daga gidan kason garin Fillingue inda ya ke tsare Mal. Hama Amadou, ta shafinsa na facebook ya yaba wa al'umma da ta kai shi ga wannan matsayi.

Idan ana tune dai Hama Amadu bai samu damar yin yakin nemen zaben ba kasancewrsa a rufe a gidan kurkuku, kuma a lokacin ya ayyana kansa a masatyin dan fursinan siyasa.

Alh. Seyni Omar shi ma tsohon firaministan kasar wanda ya tsaya takara a zaben karkashin inuwar jam'iyyar MNSD-Nassara, ya samu kaso 12.11% a cikin jimilar kuri'un da aka kada.

Mai biye masa dai she ne tsohon shugaban kasar Alh. Mahamane Usman karkashin jam'iyyar MNRD-hankuri wanda ya samu kaso 6.25%, a bayansa kuma Ibrahim Yacouba tsohon darakta a fadar shugaban kasa da ya raba gari da jam'iyyar PNDS-tarraya mai mulki, wanda ya kashi 4.34%.

Kamar dai yadda ta riga ta tabbata sai an je zagaye na biyu, yanzu ayar tambaya da mafi yawancin al'ummar kasar ke azawa kan su ita ce ko 'yan adawar kasar da sukayi fatali da sakamakon zaben tunda farko zasu amince da wannan sakamakon, ko kuma A'A zasu je zagaye na biyu su marawa abokin kawacen su Hama Amadu baya, kamar yadda sukayi alkawari na cewa duk wanda ya zo na biyu za su jefa masa kuri'a ?

Sanan wai Hama Amadu zai samu beli domin yin kamfe a zagaye na biyu ?

Wannan dai lokaci ne kawai zai fayyace haka, a yayin da bayanai ke nuna cewa zaben ya yi armashi kuma ya samu jinjina daga kungiyoyin kasa da kasa da ma wasu kasashen duniya, koda ya ke 'yan adawa a wannan kasa sun kalubalanci sakamakon zaben tun da farko da cewa an tafka kura-kurai da dama da magudi.

Add comment


Security code
Refresh