An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 26 February 2016 19:11

Zaben Majalisar Shawarar Musulunci A Iran

Zaben Majalisar Shawarar Musulunci A Iran
A yau juma'a, 26 ga watan nan na Febrairu ne al'ummar Iran su ke fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin kada' kuri'a a zaben 'yan majalisar shawarar musulunci da kuma majalisar kwararru. Al'ummar ta Iran dai za su zabi mutane 290 da za su wakilce su a majalisar shawara da kuma wasu 88 a majalisar kwararru.   Kowace daya daga cikin wadannan majalisun suna da muhimmanci a karkashin tsarin jamhuriyar musulunci ta Iran. Kuma kamar yadda jagoran juyin musulunci ya bayyana ne cewa; wadannan zabukan suna nuni ne da cewa tsarin jamhuriyar musulunci yana nan a raye, kuma al'ummar Iran ta san abinda ta ke yi domin karfafa tsarin.   Al'ummar Iran a cikin birni da kauye kuma daga kowa ce kabila sun hade a wurin guda domin kada kuri'unsu su yi zaben da zai kara daukaka jamhuriyar musulunci ta Iran a gaban makiyanta.   Ministan harkokin cikin gida ya bayyana cewa; Da akwai mutane miliyan 55 da su ka cancanci kada kuri'a a Iran. Adadin wadanda su ka tsaya takarar majalisar shawarar musulunci kuwa sun kai 4979. Sai kuma mutane 159 da su ke takara akan kujerun majalisar kwararru.   Wannan kididdigar ta nuna cewa akan kowace kujera daya ta majalisar shawarar musulunci da akwai mutane 17 da su ke takara akanta. Matan da su ke takarar kuwa sun kai 1700, wato kaso 10% na jumillar 'yan takara.   Makiyan jamhuriyar musulunci ta Iran sun bude parpaganda domin kashewa mutane guiwa kada su fito wajen yin zaben. Suna kokarin bayyana zaben a matsayin wata gogayya a tsakanin bangarori biyu , sanann kuma da sanya alamar tambaya akan ingancin zaben.   Saboda wannan shi ne zabe na farko da za a gudanar bayan cimma yarjejeniyar Nukiliya a tsakanin jamhuriyar musulunci ta Iran da kasashen yamma, sannan kuma da dage takunkuman da aka kakabawa Iran, wadanda ba su kan doka, kasashen na yamma musamman ta kafafen watsa labarunsu sun zage wajen yin sharhi da bijiro da nazarce-nazarce.   Sai dai a hakikanin gaskiya, wannan irin Parpaganda babu wani abu da za ta sauya a kasa, domin kawo ya zuwa yanzu rumfunan zabe, sun cika da mutane domin kada kuri'arsu. Mutane za su ci gaba da fitowa domin ayyana da makomarsu da kansu, kamar yadda su ka saba yi a baya.

Add comment


Security code
Refresh