An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 23 February 2016 06:04

Bukatar 'Yan Adawar DR Congo Ta Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Gwamnati

Bukatar 'Yan Adawar DR Congo Ta Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Gwamnati
Gamayyar jam'iyyun adawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta G7 ta bukaci gudanar da zaman tattaunawa na kai tsaye tsakanin 'yan siyasar kasar ciki har da jam'iyya mai mulki ta shugaban kasar Joseph Kabila.

Gamayyar jam'iyyun adawar ta G7 da ta kunshi manyan jam'iyyun siyasa bakwai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta jaddada cewa; Gudanar da zaman tattaunawa na kai tsaye a tsakanin jam'iyyun siyasar kasar ciki har da bangaren gwamnati hakan zai taimaka wajen ganin an gudanar da ingantaccen zabe a kasar karkashin doka.

 

Har ila yau gamayyar jam'iyyun adawar ta G7 ta fitar da bayani da a ciki ta jaddada yin kira ga shugaban kasar Joseph Kabila kan ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar amfani da dokar da ta takaita tsawon shekarun da shugaban kasa zai yi a kan karagar mulkin kasar wato wa'adin mulki sau biyu na tsawon shekaru biyar biyar.

 

Shugaba Jaseph Kabila dai ya dare kan karagar shugabancin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ne tun a ranar 17 ga watan Janairun shekara ta 2001 a bayan kashe mahaifinsa Laurent Kabila, sannan a shekara ta 2006 ya shirye zaben shugaban kasa inda ya samu nasarar lashe zaben, sannan a zaben ranar 28 ga watan Nuwamban shekara ta 2011 Joseph Kabila ya sake samun nasarar lashen zaben lamarin da zai kawo karshen wa'adinsa a kan karagar shugabancin kasar cikin wannan shekara ta 2016, amma sai jam'iyyar mai mulki a kasar ta fara bijiro da batun yin kwaskwarima a kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da nufin bada damar yin tazarceb shugaba Joseph Kabila lamarin da ya janyo mai da martani mai gauni daga jam'iyyun adawar kasar a watan Satumban shekara ta 2015.

 

'Yan adawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo dai suna da ra'ayin cewa; Rashin mutunta kundin tsarin mulkin kasa zai haifar da babban gibi a harkar gudanar da tsarin dimokaradiyya a kasar lamarin da zai janyo mulkin kama karya a nan gaba, don haka suka aike da sakon wasikar gargadi ga shugaba Joseph Kabila kan ya nisancin daukan matakin yin tazarce a kan karagar mulkin kasar tare da wajabcin gudanar da zabe a daidai lokacin da doka ta shimfida.

 

Masharhanta suna da tabbacin cewa; Duk wani shirin mahukuntan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na kokarin ganin Joseph Kabila ya yi tazarce a kan karagar mulkin kasar lamari ne da zai janyo rikici da tashe-tashen hankula irin wanda a faru a Burkina Faso da ya kai ga al'umma sun kawo karshen shugabancin Blaise Compaore ta hanyar yin bore a kasar.

Add comment


Security code
Refresh