An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 February 2016 07:25

Ko Kun San Na (342) 06 Ga Watan Esfan Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia.

Ko Kun San Na (342) 06 Ga Watan Esfan Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia.
Yau Alhamis 06 Ga Watan Esfan shekara ta 1394 Hijira Shamsia. Wacce ta yi dai dai da 16 ga watan Jamada-Ula Shekara ta 1437 Hijira Kamaria. Har'ila Yau wacce ta yi dai dai da 25 Febrerun shekara ta 2016 Miladia.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 62 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25 Febrerun shekara 1954 Miladia aka fara yakin basasa a kasar Siria wanda masu kishin kasa suka jagoranta kan gwamnatin soje ta Adib Sheshakli. Yan kishin kasar dai sun hada da ma'aikata yan makarantun Jami'a , sakandari da na Primari. Yankurin kifar da gwamnatin Sheshakli dai ya sami goyon bayan mafi yawan mutanen kasar. Don haka a karshen yakin dai an kifar da gwamnatin soje da Adin Sheshakli, sannan shugaban jam'iyyar masu kishin kasa Hashim al-Atassi ya hau kan kijerar shugabancin kasar.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 32 da suka gabata a ran airin ta yau wato

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Febrerun shekara 1991Miladia. Aka kawo karshen yerjejeiniyar tsaro ta WASO a tsakanin kasashe masu kawance da juna a gabancin Turai. An kafa kungiyar Tsaro ta WASO ne a ranar 14 ga watan Mayunnshekara 1955 don kalubalantar kungiyar tsaro ta NATO na kasashen yammacin Turai da Amurka. cibiyar kungiyar waso dai tana Mosco na tarayyar Soviet ta lokacin, kuma daga can ake gudanar da harkokinta. Kasashen kungiyar dai sun amince da cewa duk kasa daga cikin kasashen kungiyar aka kawowa hari hari sauran kasashen zasu shiga yakin don tallafawa kawarsu. Amma bayan wargajewar tarayyar Soviet a shekara 1991 Miladia. Ministocin tsaro na kasashen kungiyar wadanda suka hada da Poland, Hungry, Romania, Bulgeria, Chechslovakia, da kuma Tarayyar Soviet sun sanya hannu kawo karshen kungiyar ta tsaro. Har'ila yau sun wargaza rundunar sojojin kungiyar da komitin koli na tsaro na kungiyar.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 22 da suka gabata a ran airin ta yau wato 25 ga watan Febrerun shekara ta 1994 Miladia. Wani bayahuden Israi'a ya bindige masallata kuma masu azumi palasdinawa dake bada sallar magriba a cikin masallacin haramin annabi Ibrahim (a) dake garin Khalila a yankin yamma da kogin Jordan. Bayahuden ya yi amfani da wani bindiga mai sarrafa kansa wajen aiwatar da kisan. Harin dai ya girgiza kasashen musulmi da dama. Wannan harin dai ya fusata kasashen musulmi da dama. Sannan ya tilastawa kasashen larabawa dakatar da tattaunawan sulhu da yahudawan na wani lokaci. Har'ilayu yahudawan sun kama mutumin suka kama gabatar da shi a gaban kuliya wacce ta daga baya ta sallame shi wai daon tabebbe ne.

Add comment


Security code
Refresh