An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 19 February 2016 05:08

Damuwar MDD kan ci gaba da yaki a kasar Yemen

Damuwar MDD kan ci gaba da yaki a kasar Yemen
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da wasu kasashen Larabawa kalkashin jagorancin masarautar Ali sa'oud ke kaiwa kan Al'ummar kasar yemen ya kai matsayin laifin kisan kiyashi ko kuma kisan kare dangi.

A yayin wani rahoto da ya gabatar ga kwamitin tsaro na MDD, Manzon musaman kan harakokin kasar Yemen Isma'il wul shekh Ahmad ya bayyna cewa bayan rushe-rushen cibiyoyin kiyon Lafiya, ma'aikatun Gwamnati, Makarantu da sauren guraren amfanin Al'umma , ci aba da hare-haren wuce gona da iri da wasu kasashen Larabawa kalkashin jagorancin masarautar Ali sa'oud ke kaiwa kan Al'ummar kasar yemen ya kai matsayin laifin kisan kare dangi.

Wul shekh Ahmad ya ce yadda gumurzu ke kara tsanani a yankunan Adan, Lahaj, Shabwa da babban birnin Sana'a da kuma yadda ake ci gaba da hare-hare a guraren bincike da gidajen manyan jami'an tsaro gami da jami'an Gwamnati zai sharewa kungoyoyin 'yan ta'adda fage su kara samun gindin zama a kasar ta yemen.

Wannan rahoto na zuwa ne yayin da masarautar Ali sa'oud tare wasu kasashen Larabawa ke ci gaba da tsananta kai hare-haren wuce gona da iri kan Al'ummar kasar ta Yemen, inda a Makun da ya gabata mahukuntan birnin Riyyad suka bukaci kungiyoyin bada Agajin kasa da kasa su fice daga kasar ta yemen, alhali bisa dokar kasa da kasa wajibi ne magabatan na saudiya su kare dukkanin kungiyoyin kasa da kasa, daga cikin su harda kungiyoyin kai Agaji a kasar ta Yemen.

A wata wasika da suka aikawa kungiyoyin kai Agaji, magabatan saudiya sun bukacedu da su fice daga yankunan dake kalkashin ikon 'yan husi, saidai kungiyoyin sun watsi da wannan bukata, inda suka ce hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa kuma duk irin matsin lambar da za su fuskanta daga magabatan saudiya ba za su bar aiyukan da ya rataya a kansu ba.

Ci gaba da hare-haren wuce gona da iri tare da killace Al'ummar yemen daga masarautar Ali sa'oud ya sanya kungiyoyin kasa da kasa musaman babban saktaren MDD Banki Moon yin kira da a gaggauta kawo karshen wannan bala'i.

tun daga ranar 26 ga watan Maris din shekarar 2015 din da ta gabata ce mahukuntar Saudiya tare da goyon bayan kasar Amurka gami da wasu kasashen Larabawa da kuma taimakon magabatan Haramcecciyar kasar Isra'ila suka fara kai hare hare wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar duban 'yan kasar daga cikinsu a kwai Mata da kananen yara,har ila yau wannan hari yayi rusa gidagen fararen hula, ma'aikatun gwamnati, makarantu,gidajen asibiti da saurarensu da dama inda wasu rahotanin ke cewa kashin 80% na ma'aikatun Al'ummar an rusa shi.

Add comment


Security code
Refresh