An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 16 February 2016 07:58

Ko Kun San Na (337) 01 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia

Ko Kun San Na (337) 01 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia
Yau Asbar 01 ga watan Esfand Shekara ta 1394 Hijira shamsia. Wacce ta yi dai dai 11 Jamada -Ula shekara ta 1437 Hijira Kamaria. Har'ila yau wacce ta yi dai dai da 20 ga watan Febrerun shekara ta 2016 Miladia.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 839 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11 ga watan Jamada -Ula shekara ta 597 Hijira Kamaria. Aka haifi Khoja Nasiruddeen Toosi a garin Toos daga arewa maso gabacin kasar Iran. Toosi ya fara karatu a gaban mahaifinsa sannan saurin ilmi kuma a gaban sauran malamai. Wani abu mai muhimmanci a rayuwar Khoja Nasiruddeen Toosi shi ne ya rayu zamanin sarki Holokukhon na mongolawa. Ya kuma gina dakin gwaje gwaje da kuma hangen taurare a garin Maroge a shekara ta 657. Khoja Nasiruddeen Toosi ya samar da wasu sabbin hanyoyi na karatun ilmin taurari. Kuma bayansa da shekaru kimani 300 babu irinsa a kasashen yamma. Banda wannan Khoja Toosi ya gina dakin ajiye littafai wanda ya tattara littafai kimani 4000 a cikinsa. daga karshe a shekara ta 672 ya rasu kuma a ka yi masa kabari a Kazimai na kasar Iraqi. Littafan «اوصاف الاشراف» و «شرح اشارات ابن سینا» na daga cikin ayyukan Khoja nasirddeen toosi.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01 ga watan Esfan shekara ta 1358 Hijira shamsia. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa jumhuriyar musulunci ta Iran ya zabi malamai 6 da zasu kasance cikin majalisar kare kundin tsarin mulkin kasar a marhala ta farko. Banda malaman akwai lauyoyin zamani 6 wadanda alkalin alkalan kasar yake zaba ya kuma gabatar da su ga majalisar dokokin kasar don tantancewa. Ayyukan majalisar dai sun hada da sanya ido a kan dokokin da majalisar shoora Islami take samarwa, don kada su sabawa addinin musulunci da kuma kundin tsarin mulkin kasar. Banda haka majalisar ce take gudanar da dukkan zabubbuka a kasar ko wace iri ce.

03- Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01 ga watan Esfand shekara ta 1366 Hijira shamsia. Jiragen yakin kasar Iraqi a yakin shekaru 8 da ta dorawa jumhuriyar Musulunci ta cilla makaman linzami kan jirgin fasinja na jumhuriyar Musulunci ta Iran dauke da Hajjatul Islam fadlullahi Mahallati, wakilin Imam Khomaini (q) a cikin dakarun kare juyin juya halin musuluncin kasar, da kuma wasu jami'an gwamnati da kuma wasu yan majalisar dokokin kasar su 39. Jirgin ya tarwatse ya kuma kashe dukkan wadanda suke cikinsa. Wannan ba shine karon farko wanda sojojin Iraqi ta lokacin suke kashe fararen hula a yakin ba. Imam Khomaini (q) ya roki All..ta'ala ya rahamcesu ya kuma riskar da su da magabatan da suka raya addinin musulunci tun farkon bayyanarsa.

Add comment


Security code
Refresh