An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 16 February 2016 05:26

Ziyarar Shugaban Kasar Ghana A Iran

Ziyarar Shugaban Kasar Ghana A Iran
Ziyarar da shugaban kasar Ghana ya kawo a jamhuriyar muslunci ta Iran domin kara fadada alaka a tsakanin kasashen biyu.

A ranar Lahadin da ta gabata ce shugaban kasar Ghana Dramani mahama ya gana da manyan jami’an jami’an gwamnatin kasar Iran, a wata ziyara ta wuni biyu da ya gudanar a kasar Iran.

Shugaba Hassan Rauhani ya tarbi shugaban na kasar Ghana Dramani Mahama a fadarsa da ke birnin Tehran, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwa na kasa da kasa.

Shugabannin kasashen biyu sun jaddada cewa alaka da za ta ci gaba da kara karfafa atsakanin kasashensu a dukkanin bangarori, kamar yadda kuma aka sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi na yin aiki tare a bangarori daban-daban, musamman ta fuskar bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu, da kuma bunkasa harkokin noma ta hanyoyi na zamani, kamar yadda kuma bangarorin biyu suka cimma yarjejeniya kan wasu batutuwa da suka shafi tsaro, inda kasar ta Iran za ta taimaka ma Ghana da wasu dubaru da kuma kayan aiki na musamman a wannan bangare.

Bayan kammala ganawa da shugaba Rauhani, shugaba Dramani Mahama tare da shugaba Rauhani sun nufi gidan jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khameni a gidansa da ke Tehran, inda shugaban na Ghana ya tattauna tare da shi, a ganawar tasu sun tabo batutuwa da suka shafi alakar Ghana da Iran wadda dukkanin bangarorin biyu suka bayyana ta da cewa ta tarihi ce, kamar yadda kuma suka tabo batutuwa da suka shafi a halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya da kuma wasu yankuna na Afirka, musamman batun ta’addanci da sunan addini da ya addabi al’ummomi.

Jagoran juyin Islama na Iran Ayatollah Khamenei ya bayyana abin da ke faruwa da cewa salon siyasa ne na kasashe masu girman kai, da ke danne al’ummomi raunana da kuma masu tasowa, da kuma kitsa makirci ga al’ummomi masu ‘yancin siyasa, inda ya buga misali da abin da yake faruwa a halin yanzu a kasar Syria, ya kuma ce Amurka ko kasashen turai ba su da hakkin fayyace ma al’ummar Syria makoma, al’ummar Syria ne kawai suke da hakkin yin hakan ba wata kasa daga waje ba, kamar yadda kuma ya bayyana zaluncin da yahudawan sahyuniya suke kan al’ummar Palastinu da cewa abin kunya ne ga dukkanin al’ummomin duniya, ta yadda suka kasa taimakon al’ummar Palastinu da suke fuskantar zalunci da kisan gilla daga yahudawan sahyuniya.

A nasa bangaren shugaban kasar Ghana Dramani Mahama ya bayyana jin dadinsa matuka dangane da abin da ya kira rawar da Iran take takawa wajen ci gaban kasarsa ta fuskar ilimi da kiwon lafiya, da kuma ayyukan jin kai da gina kasa, kamar yadda kuma ya yi fatan ganin an kawo karshen matsalolin da ake fama da su a yankin gabas ta tsakiya, musamman ma yakin da aka haddasa a Syria, da kuma fatan ganin an warware matsalar Palastinawa da yahudawan Isra’ila tare da kawo karshen matsalar da Palastinawa suke ciki kusan shekaru 70 a jere.

Wanann dai ita ce ziyara ta farko da wani shugaban kasar Ghana ya gudanar a kasar Iran tun fiye da shekaru 37 da suka gabata, kasar ta Ghana dai tana daya daga cikin kasashen da suke da kyakkayawar alaka da kasar Iran a tsawon shekarun da Iran din ta yi tana fama da takunkumi, inda a halin yanzu Iran ta bayyana kasar ta Ghana a matsayin daya daga cikin kasashen Afirka da za ta kara bunkasa alaka da ita a dukkanin bangarori bayan janye takunkumi a kanta.

 

Add comment


Security code
Refresh