An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 15 February 2016 05:41

Ziyarar Shugaban Kasar Ghana A Iran

Ziyarar Shugaban Kasar Ghana A Iran
A Yayin ziyara ta sa Shugaba John Dramani Mahama ya Gana da takwaransa Hassan Rohani da Jagoran Juyin Juya Halin musulunci na Iran Ayatullah Khamenei

Da yammacin Ranar Asabar din nan ne shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya fara wata ziyarar aiki anan Birnin Tehran na jamhuriya musulinci ta Iran.

A yayin ziyara ta sa shugaba Mahama ya gana da takwaransa na Iran Hassan Rohani, inda bayan ganawar shugabannin biyu suka jagoranci wani taron manema labarai a jiyya Lahadi.

A yayin wannan taron manema labarai shugaba Rohani ya sanar da cimma yarjejeniyoyi da dama tsakanin kasashen biyu, a bangarorin da suka shafi noma, man fetur, makamashi, harkokin shari'a, da sarafa koko, al'adu, kimiya da dai sauran su.

A hannu daya kuma shugabannin kasashen biyu sun tabo batutuwan da suka shafi tsaro da yaki da ta'adanci.

A nasa bangare shugaba Mahama ya jinjinawa Iran kan rawa data ke takawa a fannin diflomatsiya tsakanin ta da kasashen duniya.

A yayin ziyara ta sa kuma shugaba Mahama ya kuma gana da jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Da yake bayani a yayin ganawar Jagoran juyin juya halin ya bayyana cewar kasashe 'yan mulkin mallaka ma'abota girman kai su ne ummul aba’isin mafi yake-yake da rikice-rikicen da ke faruwa a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

Inda yayin da yake ishara da siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kokarin karfafa alakarta da kasashen Afirka tun farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, Jagoran ya bayyana cewar: Kasashen ‘yan mulkin mallaka dai suna adawa da kyautatuwar alaka tsakanin Iran da kasashen Afirka.

Har ila yau kuma yayin da yake jinjinawa gwagwarmayar da wasu shugabannin Afirka suka yi wajen samar wa kasashen nahiyar da ‘yancin kansu daga wajen ‘yan mulkin mallaka, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Wadannan fitattun mutane sun daga mutumcin nahiyar Afirka a duniya.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban kasar Ghanan John Dramani Mahama ya jinjinawa irin rawar da Iran take takawa wajen tabbatar da sulhu da zaman lafiya a duk fadin duniya bugu da kari kan rawar da take takawa wajen fada da ayyukan ta'addanci.

Har ila yau kuma shugaba Mahama ya mika godiyarsa a madadin al’ummar Afirka ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda irin rawar da ta taka wajen goyon bayan kungiyoyin neman yancin kai a nahiyar Afirka musamman kungiyar fada da wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu.

Add comment


Security code
Refresh