An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 13 February 2016 05:29

Zartar da yarjejjeniyar Sulhu a kasar Sudan ta Kudu

Zartar da yarjejjeniyar Sulhu a kasar Sudan ta Kudu
Bisa yarjejjeniyar sulhun Sudan ta kudu, An nada Riek Machar madugun 'yan tawayen kasar a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Wannan mataki da shugaba Salva Keir ya dauka na a matsayin zartar da yarjejjeniyar sulhun da aka cimma tsakanin Gwamnati da 'yan tawaye a watan Augustan shekarar da ta gabata.

shi kuma mista James Wani Igga mataimakin shugaban kasar an nada shi a mikamin mataimakin shugaban kasa na biyu.

Bisa yarjejjeniyar sulhun da aka cimma,kashi 53% na madafun ikon jihohin Jongulai,Nil Aliya da Yunity za su kasance ga hanun tsofin 'yan tawayen inda kashi 33% zai kasance a hanun mabiya shugaban kasar Salva keir

A ranar 9 ga watan yunin shekarar 2011 ne Sudan ta sudu ta balle daga kasar Sudan, inda ta zamanto kasa mai cikekken 'yanci.

An fara yakin cikin gidan ne a ranar 15 ga watan Decembar 2013, bayan da aka hana Mataimakin shugaban kasar Riek Mashar da magoya bayansa halartar taron jam'iyyar mai milki tare da korar su daga cikin gwamnati .har ila yau shugaban kasar ya bukaci babban kwamandan sojin kasar da ya kwacewa dukkanin sojojin dake goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar makamansu.

Bayan aukuwar hakan, Sojojin kabilar Nuer sun dauki makamai, inda suka shelanta yin tawaye kalkashin Jagorancin Janar Marial.

Wannan mataki da 'yan kabilar Nuer suka dauka, ya sanya gwamnati tsarkake duk wani jami'in tsaro dan kabilar Nuer da suka kasance 'yan kabilar tsohon mataimakin shugaban kasar daga birnin Juba.

Baya ga birnin Juban, kisan killar da ake yiwa 'yan kabilar Nuer ya fadada har zuwa yankunan Jongulai, Malaka da kuma Nil Aliya, bisa rashoton da kungiyoyin kasa da kasa suka fitar cikin watan Avrilun shekarar 2014, yakin cikin gidan ya yi sanadiyar mutuwar Mutane kimanin dubu 10.

Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva keir ya zarki Riek Mashar tsohon mataimakin nasa da yunkurin yi masa juyin milki wanda hakan ne ma ya sanya shi daukan matakin koransa daga cikin gwamnatin.

ganin cewa shugaba Salva keir dan kabilar Dinka ne, yakin ya sake rikicewa tsakanin kabilar Dinka da kabilar Nuer, inda kabilun biyu suka dinga kaiwa juna hari.

A shekarar 2014,so da dama,Gwamnatin sudan ta kudu da kuma bangaren 'yan taswayen sun shelanta cimma yarjejjeniyar tsagita wuta tare da kafa Gwamnatin hakin kan kasa saidai rashin cimma matsaya kan rabon mukamai ya sanya aka kasa gudanar da yarjejjeniyar.

Daga karshe a watan Augustan shekarar 2015 da ta gabata, bisa shiga tsakanin kungiyar bunkasa tattalin arzikin gabashin Afirka wato IGAD, bangarorin biyu sun cimma matsaya na kawo karshen rikicin A Adis Ababa babban birnin kasar Habasha.

Duk da cewa bayan cimma yarjejjeniyar, bangarorin biyu sun zarki junansu da karya yarjejjeniyar amma hakan ya sanya hare-haren da ake kaiwa juna ya ragu sosai a cikin kasar.

A halin yanzu nadin da shugaban Keir ya yi Riek Mashar a matsayin mataimakin sa na farko shi ke tabbatar da fara zartar da yarjejjeniyar.

A bangare guda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa sama da Mutane dubu 40 ne ke fama da matsalar karamcin Abinci sakamakon fari da kuma yakin cikin gida da kasar ta fuskanta cikin shekaru da suka gabata, kuma idan ba a dauki matakan gaggawa ba, Mutane da dama ne za su fuskanci barazanar rasa rayukansu.

Masana harakokin siyasar kasar, sun bayyana cewa zartar da yarjejjeniyar sulhun zai taimakawa kungiyoyin kasa da kasa isar da Abinci a yankunan kasar musaman ma mutanan da suke cikin bukata matuka.

Add comment


Security code
Refresh