An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 11 February 2016 05:59

Alkawarin Da Shugaban Kasar Chadi Ya Dauka Idan Ya Lashe Zaben Shugabancin Kasar

Alkawarin Da Shugaban Kasar Chadi Ya Dauka Idan Ya Lashe Zaben Shugabancin Kasar
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya yi alkawarin cewa; Idan har al'ummar kasar suka sake zabensa a matsayin shugaban kasa zai dauki matakin kyaiyade wa'adin shugabancin kasar.

A furucin da ya fito daga bakin shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya yi alkawarin cewa; Idan al'ummar kasar suka sake zabensa a matsayin shugaban kasa a zaben da za a gudanar a ranar 10 ga watan Aprilun wannan shekara ta 2016, to zai dauki matakin kyaiyade wa'adin shugabancin kasar ta hanyar sake farfado da tsohuwar dokar da ta kyaiyade tsawon wa'adin shugabancin kasar ta Chadi.

Idriss Deby ya dare kan karagar shugabancin kasar Chadi ne tun a watan Disamban shekara ta 1990 ta hanyar gudanar da juyin mulki ga shugaba Husaini Habre, inda bayan tsawon shekaru shida a kan mulkin kasar ya shirya zabe a shekara ta 1996 kuma ya lashe zaben, sannan aka sake zabensa a shekara ta 2001 a matsayin karshen wa'adin mulkinsa, amma sakamakon gudanar da kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar ta Chadi, Idriss Deby ya sake samun damar tsakewa takarar shugabancin kasar, kuma ya lashe zaben shugabancin kasar a shekara ta 2006, haka nan zaben shekara ta 2011.

Shugaban Kasar Chadi Idriss Deby da wa'adin mulkinsa ke shirin kawo karshe ya yi amfani da magoya bayansa wajen neman gudanar da kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a, kuma magoya bayansa suka samu nasara, don haka Idriss Deby zai sake tsaya takarar shugabancin kasar a cikin watan Aprilun wannan shekara.

Masharhanta da masu bakin baki kan siyasar Afrika suna da imanin cewa bukatar shugaban kasar Chadi Idriss Deby na dawo da tsarin takaita wa'adin shugabancin kasar lamari ne da zai bashi damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar a nan gaba ba tate da bukatar sake yin kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar ba.

Add comment


Security code
Refresh