An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 08 February 2016 05:38

Gwamnatin Saudiyya Da Batun Tura Sojojinta Zuwa Kasar Siriya

Gwamnatin Saudiyya Da Batun Tura Sojojinta Zuwa Kasar Siriya
Har ya zuwa yanzu ana ci gaba da samun mabambanta ra'ayuyyuka dangane da sanarwar da gwamnatin Saudiyya ta yi na shirin da take da shi na tura sojojinta zuwa kasar Siriya, lamarin da gwamnatin Amurka ta yi maraba da shi a daidai lokacin da wasu a Turai kuma suke ci gaba da nuna dari-darin su kan hakan.

Babbar tambayar da take ci gaba da yawo ita ce cewa mene ne dalilin daukar wannan matsaya ta tura sojoji zuwa Siriya, sannan me ya sa sai a yanzu? Yayin amsa wannan tambayar dai, wajibi ne a yi ishara da cewa a halin yanzu dai abin da ke faruwa a fagen daga a kasar Siriya lamari ne da ke nuni da irin nasara bayan nasara da sojojini Siriyan suke samu. Daya daga cikin irin wadannan nasarori kuma ita ce nasarar da sojojin Siriyan suka samu a yankunan da suke kan iyakar kasar da kasar Turkiyya da kuma kawo karshen killacewa ta sama da shekaru uku da 'yan ta'adda suka yi wa garuruwan Nubbul da Al-Zahra masu matukar muhimmanci.

Gwamnatin Saudiyyan dai ta bayyana fada da kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) a matsayin dalilin wannan shiri na ta na tura sojoji zuwa Siriyan, to amma da dama suna ganin irin gagarumin shan kashin da 'yan ta'adda suke yi a hannun sojojin Siriya da kuma ci gaba da fatattakansu daga yankunan da suke rike da su, shi ne babban dalilin da ya sanya gwamnatin Saudiyyan daukar wannan matsaya na tura sojoji Siriyan da nufin taimaka wa 'yan ta'addan wadanda shekara da shekaru suke samun goyon baya da taimakon gwamnatin Aal Sa'ud din.; lamarin da wasu suke ganinsa a matsayin cakka wa ciki wuka ne matukar dai gwamnatin Saudiyyan ta aiwatar da wannan kuduri nata a aikace.

Ko shakka babu hadin gwiwan Saudiyya da kasar Turkiyya a wannan bangaren, wanda kamar yadda jaridar Guardian ta bayyana, akwai wani shiri da gwamnatocin kasashen biyu suke da shi na kara kulla wata alaka ta soji a tsakaninsu don cimma wannan manufar, wani lamari ne da ke nuni da abin da aka jima ana fadi na hannun da gwamnatoci biyun suke da shi kai tsaye cikin rikicin da ke faruwa a kasar Siriya, sannan kuma wani lamari ne da ke nuni da bakin cikin da suke ciki dangane da irin nasarorin da sojojin Siriyan suke samu a kan 'yan ta'adda.

Wani lamarin kuma shi ne cewa irin nasarorin da da sojojin Siriyan suke samu musamman a yankunan da suke kan iyakan kasar Turkiyya da kuma shan kashin da 'yan ta'addan suke fuskanta lamari ne da ke kara karfi ga siyasar gwagwarmaya da tsayin daka wanda gwamnatocin kasashen Iran, Siriya, Iraki suka rika a yankin Gabas ta tsakiya wanda kuma tsawon shekarun nan Saudiyya da Turkiyya suke ta kai gwauro su kai mari wajen ganin hakan ba ta faru ba.

Wani abin lurar kuma na daban shi ne irin yadda gwamnatin Amurka ta yi na'am da wannan matsaya ta Saudiyya duk kuwa da cewa tsawon shekarun nan gwamnatin Amurka ta ki amincewa da bukatar da wadannan gwamnatoci suke mata na shiga cikin yakin kasar Siriyan kai tsaye da nufin kifar da gwamnatin Bashar al-Asad ta kasar.

Abin tambayar a nan ita ce me ya sa gwamnatin Amurkan yin na'am da wannan matsaya ta Saudiyya? Ko shakka babu daya daga cikin dalilan marabar da Amurka ta yi da wannan matsayar, shi ne cewa idan har Saudiyya ta aike da sojojinta zuwa Siriya, za ta zamanto ta sake kaddamar da wani yaki ne na daban don cimma manufofin wasu na daban, wanda kuma ko shakka babu Amurka za ta samu damar cimma manufofinta ba tare da ta yi amfani da kudi ko kuma sojojinta ba.

To koma dai mene ne wani abin da babu kokwanto cikinsa shi ne bisa la'akari da irin goyon bayan da kasashen Iran da Rasha suke ba wa gwamnatin Siriya, don haka da wuya gwamnatin Saudiyya ta iya cimma manufarta ta kifar da gwamnatin Bashar al-Asad ta hanyar wannan matsaya ta tura sojoji zuwa Siriya, hakan ne ya sanya wasu suke ganin wannan matsaya a matsayin wani cakka wa ciki wuka.

Add comment


Security code
Refresh