An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 06 February 2016 06:31

MDD Ta Damu Kan Yaduwar Cutar Zika

MDD Ta Damu Kan Yaduwar Cutar Zika
Kawo yanzu cutar Zika ta bazu a wasu kasashe da yankuna 32 dake nahiyar Amurka da yammacin tekun Fasific, da nahiyar Afrika, da Asiya inji WHO

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar cewar, tun daga shekarar 2015, cutar Zika ta bazu a wasu kasashe da yankuna 32 dake nahiyar Amurka da yammacin tekun Fasific, da nahiyar Afrika, da Asiya.

Hukumar WHO ta ce, cutar Zika tana bazuwa ne ta hanyar cizon sauro, kuma abinda ya fi muhimmanci shi ne a magance yaduwar cizon sauro ta hanyar kare al'ummar daga cizon sauro.

Ye zuwa yanzu MDD ta bukaci kasashen da aka samu bullar cutar da su bai wa mata damar amfani da kwayoyin hana haihuwa da kuma damar zubar da ciki don kaucewa haihuwan yara masu nakasa.

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar ta ce, hana mata daukar ciki da wasu kasashen da ke fama da cutar suka yi, bai wadatar ba, ya kamata a bai wa matan zabi na amfani da kwayoyi ko matakin zubar da ciki a lokacin wannan annoba.

Tun bayan bullar zazzabin Zika a wasu kasashen duniya ne aka soma bai wa mata shawarar kaucewa daukar ciki don hana su haihuwar yara masu kananan kai ko nakasa.

Saidai babban kaluballe da wannan kiran na MDD ke cin karo da shi ne mafi yawancin kasashen kudancin Amurka da cutar tafi shafa basa amuncewa nda duk wani mataki na zumar da ciki ko kuma amfani da kwayoyin hana dokar ciki.

A hannu daya kuma Hukumar lafiya ta duniya WHO ta gargadi kasashe kan kaucewa karbar gudunmuwar jinni daga mutanen da suka fito daga balaguro a kasashen da ke fama da cutar .

Hukumar ta ce saboda matakan kaucewa yaduwar cutar akwai bukatar a kauracewar karbar jinni daga wani mutun da ya je kasashen da cutar Zika ta bulla.

Tuni dai kasashen Canada da Birtaniya suka fara daukar matakin haramta karbar jinni har sai mutum ya kai tsawon wata guda da dawo wa kasashen da ke fama da cutar

Zika dake haddasa haihuwar Jarirai da Nakasa na cigaba da Yaduwa a Latin Amurka da Yankunan Turai, inda yanzu haka aka kuma bankado labarin cewa cutar na iya yaduwa ta jima'i.

A kwanan baya dai ne hukumar ta WHO ko kuma OMS ta kaddamar dokar ta-baci domin dakile yaduwar Cutar da ta fi yin illa ga jarirai wadanda ake haifuwa da karamin kai.

Hukumar Lafiya dai na fuskantar matsin lamba ne kan gano illolin cutar da hanyoyin magance ta, a yayin da ta ke ci gaba da fama da cutar Ebola a kasashen Afrika.

Tuni dai Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa za a samu karuwar masu kamuwa da cutar a bana wanda ya zama wajibi a dauki matakan dakile yaduwarta.

wata damuwa kuma da ake da ita, ita ce ta Kasar Brazil mai karbar bakuncin gasar wasanin Olympique inda milyoyin al'umma zasu hadu, sanan Allah kawai yasan a cikin irin halin da zasu koma kasashen su, duk kuwa da cewa kasar ta Brazil ta ce tana daukan kwararren matakai na hana yaduwar cutar ta hanyar kashe sabro dake yada ta.

kawo yanzu dai cutar ba tada magani bale riga kafi, aman tuni kwararu akan sha'anin kiwan lafiya suka fara binciken hada maganin cutar.

 

 

Add comment


Security code
Refresh