An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 03 February 2016 12:27

Ko Kun San (324) 18 Ga Watan Bahman Shekara Ta 1394 Hijira Kamariyya

Ko Kun San (324) 18 Ga Watan Bahman Shekara Ta 1394 Hijira Kamariyya
Yau Lahadi 18 ga watan Bahman shekara ta 1394 hijira kamaria wacce ta yi dai dai da 27 Rabi'uthani shekara ta 1437 hijira kamaria har'ila yau wacce tayi dai dai da 7 ga watan Febreru shekara ta 2016 Miladiyya

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 32 da suka gabata a rana irin ta yau wato 7 ga watan Rabi'uthani shekara ta 1405 hijira kamaria Aya. Uzma Hajj Sayyeed Ahmad Khunsari babba malamin mazhabar iyalan gidan manzon Al...(s) ya rasu a nan Iran. An haifi Aya. Khunsari a garin Khunsar a nan kasar Iran a shekara 1309 hijira kamaria sannan ya fara karatun sharar fage a mahaifarsa. daga baya ya je birnin esfahan don karin karatu. Daga can ya wuce birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai na lokacin. Bayan kaiwa ga matsayin mujtahidi Aya. Khunsari ya dawo kasar Iran a shekara ta 1335 hijira kamaria. Aya. Khunsari ya shahar da tsoron Al..da zuhudu. Sannan yana daga cikin malaman da suke goyon bayan yankurin Imam Khomaini (q) na kawo sauyi a kasar. Aya Khunsari ya rasu ne a ranar 29 ga watan Day na shekara ta 1363 hijira shamsiyya yana dan shekara 96 a duniya.

02- Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 32 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18 ga watan Bahman na shekara ta 1362 hijira kamaria. Gulam-Ali Uwaisi daya daga cikin yan siyasar kasar Iran kuma wanda ya haddasa shahadar da dama daga cikin mutanen kasar Iran a kokarinsa na kare sarautar sarkin ya mutu a hannun wasu mijahidan juyin juya halin musulunci a birnin Paris na kasar Faransa. Uwaisi ya ingiza mutanensa wajen murkushe juyin juya halin musulunci wata daya kafin arcewar sha daga kasar ran. Har'ila yau bayan samun nasara ma ya ci gaba da ingiza mutanensa don ganin bayan juyin amma ba tare da samun nasara ba. Bayan haka ne ya arce daga kasar Iran ya koma birnin Paris na kasar Faransa. Bayan wani lokacin an sami nasarar kasheshi a can birnin Paris.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 17 da suka gabata a rana irin ta yau wato 7 ga watan Febrerun shekara ta 1999 Miladiyya Sarki Husain na kasar Jordan ya mutu. An haifi sarki Husain na Jordan a shekara 1935 miladia ya kuma hau kan kujerar sarautar kasar Jordan ne bayan kisan kakansa Sarki Abdullah na daya da kuma sarutar mahaifinsa na yan watanni. Sarki Husain yana dan shekara 18 wato a shekara 1953 ya zama sarkin Jordan. Sarki Husain ya shiga yaki da HKi a yakinta da kasashen Larabawa a yaki na farko na biyu da kuma na ukku. Amma bayan haka a hankali a hankali ya zama abokin HKi ya ma maida hulda da ita. Daga nan kuma ya zama mai goyon bayan sulhuntawa da HKI da kuma goyon bayan kafa kasar Palasdinu a yankuna kafin yakin kwanaki 6 a shekata 1967. Kafin mutuwarsa da kadan ya tube dan uwansa Husanai Tala a matsayin yerima mai jiran gado ya dora dansa Abdullahu na biyu sai ya mutu yana dan shekara 64 a duniya.

Add comment


Security code
Refresh