An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 03 February 2016 04:17

Duniya Tana Ci Gaba Da Nuna Damuwa Kan Rikicin Kasar Libiya

Duniya Tana Ci Gaba Da Nuna Damuwa Kan Rikicin Kasar Libiya
Hakika rashin samun nasarar kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Libiya da kuma yadda 'yan ta'addan kungiyar Da'ish ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a kasar matsaloli ne da suke ci gaba da daga hankalin duniya.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya Martin Kobler ya bayyana tsananin rashin jin dadinsa kan yadda Majalisar Dokokin Libiya ta ki kada kuri'ar amincewa da gwamnatin hadin kan kasa da fira minista Fa'iz Sarraj ya gabatar a gabanta, yana mai jaddada wajabcin samun hadin kai da fahimtar juna a tsakanin 'yan majalisun kasar ta Libiya da nufin hanzarta samar da gwamnatin hadin kan kasa da zata gudanar da hidima ga al'ummar kasar tare da kasancewar Tripoli a matsayin fadar mulkin kasar.

Har ila yau wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Libiya ya jaddada muhimmancin ganin an cimma daidaiton baki a tsakanin 'yan Majalisun Libiya domin samar da gwamnatin hadin kan kasa da nufin hanzarta warware tarin matsalolin da kasar ta shiga musamman matsalar tashe-tashen hankula da kuma uwa uba matsalar ta'addancin kungiyar Da'ish da ke neman mai da Libiya tungarta.

A gefe guda kuma wakilin Hukumar Kula da Ayyukan Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Libiya Ali Azza'atari ya koka kan matsalar dakatar da ayyukan jin kai a kasar ta Libiya, yana mai bayyana cewa; Shirin tallafawa al'ummar Libiya kimanin mutane miliyan daya da dubu dari uku da tashe-tashen hankulan kasar suka tarwatsa su tare da wurga rayuwarsu cikin halin kaka-ni ka yi ya tsaya cak tun bayan watanni biyu kacal da fara aiwatar da shirin, kuma kashi daya cikin dari na mutanen da suke cikin matsalolin ne kawai suka ci gajiyar shirin.

Haka zalika ministan tsaron kasar Faransa ya yi tsokaci da cewa; Sakamakon dambaruwar siyasar kasar Libiya, 'yan ta'addan kungiyar Da'ish suka samu damar yin kutse a cikin kasar lamarin da yake matsayin babbar barazana ga kasashen yammacin Turai saboda akwai yiyuwar 'yan ta'addan sun samu damar yin kutse a cikin kasashen yammacin Turai ta hanyar kasar ta Libiya musamman ganin yadda suke saurin samun nasarar mamaye yankunan kasar.

Add comment


Security code
Refresh