An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 30 January 2016 05:49

Ziyarar Shugaban Kasar Iran Zuwa Kasashen Turai Guda Biyu Bayan Dage Takunkumai

Ziyarar Shugaban Kasar Iran Zuwa Kasashen Turai Guda Biyu Bayan Dage Takunkumai
Gwamnatin kasar Faransa da Jumhuriyar muslunci ta Iran sun maida hulda a bangarori

Gwamnatin kasar Faransa da Jumhuriyar muslunci ta Iran sun maida hulda a bangarori da dama bayan dagewa Iran din takunkumai tattalin arzki, musamman a bangaren kasuwarci da kuma bunkasa tattalin arziki.

Sheikh Hassan Ruhani shugaban kasar Iran ya kamala ziyarari aiki na farko kuma na kwanaki hudu zuwa kasashen turai guda biyu bayan dage kasarsa takunkuman tattalin arziki kan shirinta na makamashin Nuklia. Shugaban ya kula yerjejeniyoyi masu muhaimmanci da kasashen Itala da kuma Faransa a bangarorin da dama wadanda suka hada da bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu da kuma kyautata harkokin kasuwanci.

A cikin kwanaki biyu da ya yi a kasar Italia dai an kulla yerjeniyoyi da dama wadanda suka kai dalar Amurka billion $18.4.

A kasar Faransa kuma shugaba Ruhani ya kulla yerjejeniyoyi 20 tare da kamfanonin kasar Faransa da dama. Banda ganawa da shugaban kasar Faransa Sheikh Ruhani ya gana da shuwagabannin manya manyan kamfanonin sifira wadanda suka hada da kamfanin Airbus mai kera jiragen sama, inda kasar Iran ta bukaci sayan jirgaen fasinja 118 wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka billion $27. Shugaban kamfanin Air Bus yace kamfanin zai mikawa Iran jirage 17 a cikin wannan shekara da muke ciki.

Har'ila yau shugaban kamfanin motoci na Peugoet ya gana da shugaban inda aka kulla yerjejen iya ta dawo da aikin harhada mutocin Peugoet a birnin Tehran, sannan zasu maida kasar Iran cibiyar saida motocin Fransa a yankin gabas ta tsakiya.

Banda haka kamfanin Total masu haka da kuma sarrafa man fetur da gas ya nuna kodayinsa da dawawa kasar Iran don ci gaba da aikin makamashi a kasar.

A wani jawabin hadin guiwa wanda shuwagabnnin kasashen biyu suka yi a gaban yan jaridu shugaba Hassan ruhani ya ce zamanin takurawa kasashe ta hanyar kakaba masu takunkumai ya wuce a duniya. Ya kuma kara da cewa a cikin takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar Iran bangarorin biyu duk sun cutu. Don haka yay i kira ga manya manyan kasashen duniya da suke irin wannan ra'ayin da su dawo cikin hayyacinsu su san abin da yaka mata su yi.

A nashi bangaren shugaban kasar Faransa fransua Holand ya bayyana dangandakar kasar Iran kasar Faransa a matsayin wanda ya dade a tarihi, yama kuma fatan kasashen biyu zasu yi aiki tare don fadada dangantakar. Daga karshe shugaba Runaha ya bayyana cewa kasar Iran zata ci gaba da kiyayen alkawulan da ta daukawa kanta kan shirin makamashin nukliaryar matukan dayan bangare ya kiyaye abinda yah au kanta.

A cikin watan Jeneru da muke ciki ne manya manyan kasashen duniya wadanda suka hada da Rasha, China, Amurka, Brirania Faransa da kuma kasar Jamus suka dagewa Iran takunkuman tattalin arziki wadanda suka shafi shirinta na makamashin nuklia.

Add comment


Security code
Refresh