An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 28 January 2016 06:31

Yantar Da Garin Sheikh Miskin Da Ke Lardin Dar'a Na Kasar Siriya

Yantar Da Garin Sheikh Miskin Da Ke Lardin Dar'a Na Kasar Siriya
Sojojin gwamnatin Siriya da dakarun sa-kai sun samu gagarumar nasarar yantar da garin Sheikh Miskin da ke kudancin kasar Siriya daga mamayar gamayyar 'yan ta'adda da suke samun goyon bayan wasu kasashen duniya musamman Amurka da 'yan koranta na kasashen Larabawa da kuma haramtacciyar kasar Isra'ila da Turkiyya.

Tun a ranar Talata da ta gabata ce rundunar sojin gwamnatin Siriya ta sanar da 'yantar da garin Sheikh Miskin da ke kudancin kasar daga gungun 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a cikin Siriya bayan halaka daruruwan 'yan ta'adda. Garin Sheikh Miskin shi ne gari mafi girma a lardin Dara'a da ke kudancin kasar Siriya kuma gari mafi muhimmanci da tasiri a yankin sakamakon kasancewarsa hadaka tsakanin Dara'a ta Yamma da Dara'a ta Gabas, kuma shi ne hanya daya tilo da 'yan ta'adda suke amfani da shi wajen jigilar makamai da na bukatunsu na yau da kullum tsakanin yankunan biyu, sannan 'yan ta'addan sun mai da garin a matsayin tungarsu saboda muhimmancinsa a yankin.

 

Har ila yau garin Sheikh Miskin yana matsayin mahada ne tsakanin lardunan Dara'a da Suwaida'u da Qanidarah da kuma birnin Damasqas ta shiyar kudu lamarin da ke bai wa 'yan ta'adda damar kai komo a tsakanin wadannan yankunan. Sannan a yayin gwagwarmayar 'yantar da garin na Sheikh Miskin, sojojin Siriya da dakarun sa-kai sun samu nasarar ganowa tare da rusa cibiyoyin sadarwa da 'yan ta'adda suke amfani da su wajen aikewa da bayanan sirri gami da rahotonni ga wasu gwamnatocin kasashen da suke goya musu baya a ayyukan ta'addancin da suke gudanarwa a kasar ta Siriya musamman haramtacciyar kasar Isra'ila.

 

Rahotonni sun tabbatar da halakar daruruwan 'yan ta'adda musamman 'yan kasashen waje tare da gano takardun 'yan kasa na wasu daga cikinsu ciki har da kasashen da suke makobtaka da kasar ta Siriya. Daga cikin kungiyoyin 'yan ta'addan da suke mamaye da garin na Sheikh Miskin sun hada da Jaishul-Hurr, Jubhatun-Nusrah, Kata'ibu-Balwa'i Bani-Umayyah da katibatul-Barmuk.

 

A bayan 'yantar da garin Sheikh Miskin, sojojin gwamnatin Siriya da dakarun sa-kai sun kuma samu nasarar yantar da sauran yankunan da suke makobtaka da garin a lardin na Dara'a musamman gefen birnin Damasqas da ke kudanci.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Add comment


Security code
Refresh