An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 26 January 2016 05:55

Rushewar Yarjejeniyar Sulhu A Sudan Ta Kudu

Rushewar Yarjejeniyar Sulhu A Sudan Ta Kudu
Madugun ‘yan tawayen kasar Sudan ta kudu, ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka kulla ta sulhu domin kafa gwamnatin hadin kan kasa, ta ci kasa. Reikh Machar wanda ya gabatar da taron manema labarai a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, ya bayyana cewa; “Matukar shugaban kasar Silva Kir bai yi watsi da shirinsa na kirkiro sabbin jahohi a kasar ba, to ba za a kafa gwamnatin hadin kai a cikin kasar ba.”   A cikin watan oktoba na shekarar da ta gabata ne dai shugaba shugaban kasar ta Sudan ta kudu, silva Kir ya sanar da shirinsa na maida jahohin kasar 10 zuwa 28, saidai madugun ‘yan tawayen kasar Reik Machar ya bayyana shirin da cewa ya sabawa yarjejeniyar watan Augusta da bangarorin biyu su ka rattaba hannu akai.   Amma duk da haka shugaban kasa Silva Kir ya aiwatar da shirin nasa inda ya ayyana sabbin gwamnoni da su ka fito daga soja a cikin sabbin jahohin.   A cikin watan Augusta ne bangarorin gwamnati da kuma ‘yan tawaye sun rattaba akan yarjejeniya ta tsagaita da kuma sulhu, duk da cewa tashe-tashen hankula sun biyo baya. Bayan samun saukin fada a tsakanin bangarorin biyu, an sake kulla wata yarjejeniyar a cikin watan Janairu nan da ake ciki, inda su ka amince da kafa gwamnartin hadin kan kasa.   Abinda ‘yan tawayen su ke fada a yanzu shi ne cewa; batun da shugaban kasar ya ke yi na kirkiro sabbin jahohi ya ci karo da abinda su ka cimma yarjejeniya akansa a watan Augusta.   Kakakin kungiyar ‘yan tawaye Mabiro Garang, ya bayyana cewa da akwai masu tsattsauran ra’ayi a cikin gwamnati, sannan ya ce; an cimma yarjejeniya ne akan tsoffin jihohi 10 da ake da su, ba jahohi 28 ba da aka kirkiro.   Har ila yau, Garanga ya ce; ‘yan tawayen suna son ganin cewa sulhun da aka yi ya dore, kuma basu da sha’awar komawa yaki.   A gefe daya, shugaban kasar Silva Kir ya nemi gafarar mutanen kasar saboda yakin da ba ya bayyana da cewa; ba shi da wata ma’ana.   A yanzu, da sulhun da aka yi na shirin kafa gwamnatin hadin kan kasa ya ke fuskantar barazana, yana dauke da wani sako maras dadi ga al’ummar kasar.   Tare da cewa masu bin diddigin abinda ya ke faruwa a cikin kasar Sudan ta kudu, suna bayyana shi a matsayin musifa ga al’ummar kasar,sai dai dukda haka suna fatan cewa a wannan karon, za a sami mafita da tsira.                      

Add comment


Security code
Refresh