An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 20 January 2016 18:01

Ko Kun San (1-30) Day Shekara Ta 1394 Hijira Shamsiyya

Ko Kun San (1-30) Day Shekara Ta 1394 Hijira Shamsiyya
Yau Talata 01-Day-1394H.SH=10-R-Awwal-1437H.K.=22-Decemba-2015M.

Yau Talata 01-Day-1394H.SH=10-R-Awwal-1437H.K.=22-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1482 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-R-awwal-45H.K. Abdul-muttalib kakan manzon All…(s) ya rasu a Makka. Abdulmuttalib ya kasance daga cikin shuwagabanin quraishawa ya kuma kasance mai kula da rigar dakin kaaba da kuma ciyar da mahajjata. Ya shahara da fasaharsa da kuma karamcin. Abdlmuttalib yana da yaya da dama daga cikinsu akwai Abdullahi mahaifin manzon All.(s) da kuma Abu talin mahaifin Aliyu (a). Abdulmuttalib ya rasu manzon All..(s) yana dan shekara 8 a duniya. Bayan rasuwarsa renon manzon All..ya kuma ga amminsa Abutalib.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1465 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-R-awwal-shekaru 28 kafin hijira. Manzon Al…(s) ya auri matarsa ta farko kuma mahaifiyar yayansa gaba daya in anda Ibrahim (a). Hadiza ta kasance mce mai daukaka da mutunci a cikin makka a lokacin . sannan ta auri manzon All.(s) tana yar shekara 40 a duniya, sannan ta rayu tare da shin a tsawon shekaru 25. Hadiza ce ta fara karban addinin Musulunci sannan ta baje dukkan dunkiyan ta mallaka don yada addinin Musulunci da kuma kare al-ummar musulmi. Don matsayin wannan matar a wajen manzon Al..(s) ya kasance yana ambatonta da alkairi a duk sauran rayuwarsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 322 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Decemba-1693M. Girgizan kasa mafi muni a kasar Italia ta auku a tsibirin silil kusa da tekun medeteranian. Don tsananin girigizan kasar babu wani gini da ya rage a tseye a lokacin, sannan mutane dubu 80 suka rasa rayukansu a tsibirin.

================================================.

Yau Laraba 02-Day-1394H.SH=11-R-Awwal-1437H.K.=23-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 90 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Decemba-1925M. Birnin Jidda nab akin ruwa a kasar Hijas ya fata daga hannun sarki Husain sharifu makka yak ma hannun ali-saud. A shekara 1906 ne dangin Ali Saud suka kwace iko da garin riyad a kasar Hijas sunnan Abdulazizi bin Abdurrahman bin saud ya nada kansa a matsayin sarkin yankin. Sai kuma bayan faduwar daular Usmaniya abdulaziz ya fadada mulkinsa a hijas inda ya kwance yanking aba daya a hannun sharufu makka a ranar 23-Decemban-shekara 1925. Sai kuma a ranar 18-Decemban-1932M. Abdulaziz ya nada kansa sarkin kasar saudia a yanda take a halin yanzu.

**Masu saurare ko kun san cewa shekaru 83 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-R-Awwal-1354H.K. Aya. Sayyeed Hassan Sadr daya daga cikin manya manyan malamin mazhabar shia ya rasu a birnin Najaf na kasar Iraqi. An haifi Aya. Sadr a cikin dangi mai daraja a kasar ta Iraqi sannan ya zama mujtahidi tun yana matashi. Aya. Sadar yay i zurfi a ilmin fikihu, kalam, Usul da kuma hadisi. Banda karantarwa da tarbiyyan talaibai Aya. Sadar ya rubuta littafai da dama wadanda suka hada da «تاسیس الشیعه»، da kuma «تحصیل الفروع الدینیه فی فقه الامامیه».

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 67 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Decemba-1948M. Kotu ta musamman don hukunta manya manyan masu laifi a yakin duniya na biyu ta yanke hukuncin kisa kan manya manyan jami’an gwamnatin kasar Japan 7. Kotun na japan reshe ne na kotun Nurambug na kasar Jamus. Gaba daya mutane 25 aka gurfanar a gaban kotun na birnin Tokyo. Inda kotun ta yanki hukuncin daurin rai da rai ga mutane 18 daga cikinsu a yayinda sauram 7 kuma, wadanda suka hada da Priministan kasar ta Japan a yankin duniya na biyu aka yanke masu hukuncin kisa.

=======================================================

Yau Alhamis 03-Day-1394H.SH=12-R-Awwal-1437H.K.=24-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1490 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-R-Awwal-shekaru 53 kafin hijira. A bisa yadda malaman sunna suka tafi, aka haifi fiyayyen halitta manzon Al…Muhammad dan Abdullahi (s) a garin Makka. A bisa fahintar malaman mazhabar ahlulbaiti an haife shi ne a ranar Jumma’a 17-R-awwal-na shekara ta 53 kafin hijira. Don haka ne a nan JMI daga ranar 12-17 ga watan R-awwal na ko wani shekara ake kiransa makon hadin kai. Wato makon hadin kai tsakanin manya manyan mazhabobin Musulunci ta shia da sunna a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1436 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-R-awwal-shekara ta farko bayan hijira. Manzon All…(s). ya gina masallaci na farko a Musulunci a garin Koba kusa da garin Madina. Bayan hijiransa daga makka zuwa madina manzon Al…(s) ya tsaya a kauyen kuba inda ya ki shiga madina said an amminsa Aliyu dan abitalib (a) ya riskeshi a nan kuba tare da isauran yaya da iyalan gidansa. A nan ne jumma’a ta same shi sai ya gina masallaci na farko a muslunci sannan ya yi sallar jumma’a ta farko. Har yanzun masallacin Quba tana nan a cikin madina ga wadanda suke son ziyartarsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 64 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Decemba-1951M. Kasar Libya ta sami encin kanta daga hannun turawan Itali a yan mulkin mallaka. Hakan ya faru ne bayan da majalisar dinkin duniya ta kada kurei’ar amincewa da samun encin nata, sarki Muhammad Idris al-mahdi shi ne sarkin kasar n farko. Kasar Libya tana daga cikin kasashen da turawan Italia da britania suka yiwa mulkin mallaka na wani lokaci . kafin haka tana karkashin daular usmania tun karni na 15 miladiyya. Amma a shekara 1969 ma sojojin kasar karkashin jagorancin Muammar kazzafi sun kwace mulkim daga hannun sarki idris sannan kazzafi ya mulki kasar har zuwa shekara ta 2011 lokacinda yan tawaye masu samun goyon bayan turawa suka kasje shi. Libaya tana daga cikin kasashe masu dimbin arzikin man fetur a duniya.

========================================.

Yau Jumma’a 04-Day-1394H.SH=13-R-Awwal-1437H.K.=25-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 2016 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Decemba, rana ce ta haihuwar annabi Isa (a) daya daga cikin manya manyan manzannin All..a garin Bethlaham na kasar Palasdinu. Haihuwar annabi Isa (a) ya zo da mu’ajiza daga Al.. ta’ala, inda mahaifiyarsa mai tsarki Maryam yar Emrana ta haifeshi bata taba yin aure ba ku ba karuwa bace. Don kare haifinta daga zargi da kuma bayyana annabcinsa a cikin bani Isra’ila . Annabi Isa (a) tare da ikon Al.. yana magana lokacin kadan bayan haihuwarsa. Inda a cikin maganarsa ya tabbatar da tsarkin mahaifiyarsa ya kuma bayyana annabcinsa ga bani Isra’ila. Ya kasance yakan tada matattu, ya warkar da marasa lafiya ya yi huri cikin tabo ya zama tsuntsu tare da izinin Al..All.. ta’ala ya bashi littafin Injila , ya kuma sanar da shi attaura a na annabi Musa don shiryatar da mutane. Ayayin al-qur’ani da dama sun sauka kan rayuwarsa da matsayinsa a wajen All.. Mutane taya masu saurarommu musamman mabiyashi murnan ranar haihuwarsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 372 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Decemba-1643 M. Aka haifi Eshaq Newton wani masanin ilmin kimiyyar lissafi da lisafin a kasar Britani. Newton ya rasa mahaifiyarsa tun yana karami. Ya tashi yana sha’awar ilmin Physics. A lokacinda ya kammala karatu a jami’ar Cambrege ya shiga bincike da gwaje gwaje. Mafi muhimmancin a cikin abinda Eshaq yana gano dai sun hada da “karfin jazibiyarra kasa” ko kuma yadda kasa yake yan kome zuwa jikinta. Sannan ya tsara dokokin matsin abubuwa ya kuma samar da hanyanon lissafinsa. Newton ya rasu a ranar 20-Maris-1727M yana dan shekara 85 a duniya.

**Masu saurare ko kun san cewa shekaru 97 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Decemba-1918M. Aka haifi shugaba Anwar sadad na kasar Masar. Ya tashi a kasar ya kammala karatu ya shi aikin soja inda ya zama shugaban kasa na ukku bayan kawo karshen tsarin sarauta a kasar. Sadad shugaban kasar Larababawa na farko da ya amince da samuawar HKI ya kuma sulhunta da ita ya maida dangantar kasarsa da ita. Sadad ya yi mulkii tsakanin shekara 1970-1981. Amma sanadiyyar wannan ha’incin da yayiwa musulmi da kasashen larabawa wasu sojojin kasar suka bindige shi har larana a 06-Octobar-1981M.

===============================================.

Yau Asabar 05-Day-1394H.SH=14-R-Awwal-1437H.K.=26-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Decemba-1979M. Sojojin tarayyar Soviet ta lokacin dubu 130 sun mamaye kasar Afganistan. Gwamnatin tarayyar Soviet ta lokacin dai ta bayyana cewa ta shiga kasar ne tare da bukatar shugaban kasar ta afganistan. Sai dai mayakan mujahidun na kasar , tare da karancin makamai a hannunsu sun fuskanci sojojin “read Army” na tsawon shekaru 10. Har’ila yau kasar ma ta ji tsaron mamayar Afganistan din ts shafi bukatunta a yankin don haka ta tallafawa mayakan mujahidon da kudade makamai da sauransu. Daga karshe sojojin T-Soviet sun fice daga kasar Afganistan bayan shekaru 10 da mamayarta a shekara 1989>.

**Masu saurare ko kun san cewa shekaru 12 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-day-1382H.SH. Girgizan kasa mai karfin ma’aunin Richter 6.8 ta aukawa garin tarihi na bam da gewayensa a nan kasar Iran. Karfin girgizan kasar ta rasu rabin garin sannan ta kashe mutane dubu 41, banda haka dubban dubatan mutanen suka ji rauni ko kuma suka bar garin. Bayan girizan kasar da kadan ne hukumomin taimakon gaggawa na cikin gida suka kai masu dauki, har’ila yau wasu kungiyoyin bada agajin daga kasashen waje ma sun tallafawa wadanda suka rasu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 11 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-adecemba-2004M. Aka girgizan kasa mai karfi a cikin tekun pecifi a kusa da kasashen kudu maso gabacin Asia mai karfin ma’aunin richte 9. Girgizan kasar wacce aka fi saninsa ta tsunami ta haddasa igiyoyin ruwa masu karfi da kuma sauri, wadanda kuma suka fadawa kasashen da suke bakin ruwa , wadanda suka hada da Indonasia, Malesia, Sirilanka, Tailand da kuma inda. Tsunami ta jawo asarorin rayuka kimani dubu 220, da na dukiya triliyoyin dalar Amurka. Kimanin mutane miliyon 2 ne suka kauracewa yankunan da abin yay a shafa.

===================== ==

Yau Lahadi 06-Day-1394H.SH=15-R-Awwal-1437H.K.=27-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1373 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-R-Awwal-63H.K. Yazid dan mu’awiya dan Abi sufyan ya halaka bayan shekaru 3 da watannin 9 kan kujerar khalifanci. A shekara ta farki yazid ya tura sojojin suka yaki Imam Husain (a) jikan manzon All…(s) a karbala ya kashe shi da sauran iyalan gidan manzon Al…(s) da sahabbansa. Sai kuma a shekara ta biyu ya aike sojojinsa suka gashe mutanen madina, a cikin abinda aka fi sani da waqi’ar hurrah. Sai kuma a lokacinda ya mutu sojojinsa suna can kaaba suna rusa shi. Yazid mutum ne wanda baisan wani abu a addini ba kuma yakan bayyana sabon All..a fila . Don zaluncinsa mafi yawan al-ummar musulmi basa sonsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-decemba-1945M. Aka kafa asusun lamuni na duniya wanda ake kira I.M.F (International Monitary Fun.) wanda yake wani bangaren ne na rassan majalisar dinkin duniya, amma kuma a lokacin duga mallakar kasshe wadanda suke da jari a cikinsa ne. Manufar kafa IMF dai ita ce daidaita darajar kudade a duniya, bada tallafin bashi ga kasashe memnobi a cikinta da kuma bude hanyoyin ci gaban tattalin arziki a kasashen membobi a cikinta. Sai dai kasashen yamma ne musamman Amurka suke da jari mai tsoka a cikin wannan asusun don haka sune suke sarrafa asusun kamar yadda suka ga dama. Suna bada basussuka masu kudaden ruwa mai yawa. Wanda ya kai ga duka manofofin kafa shi har yanzun bai kai nasara ba.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Decemba-1945M. Bayan yakin duniya na biyu manya manyan kasashen duniya sun rattaba hannu kan yerjejeniyar raba kasar Korea a birnin Mosco na tarayyar Soviet a lokacin.Wakilan kasashen Amurka Britania da kuma ita T-Soviet ne suka rattaba hannu kan wannan yerjejeniyar, wacce raba kasar Koria zuwa korea ta arewa mai bin tsarin gurguzu da kuma koria ta kudu mai bin tsarin jari hujja.

============================================.

Yau Litinin 07-Day-1394H.SH=16-R-Awwal-1437H.K.=28-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1436 da suka gabata a rana irin ta yau 16-R-Awwal-01H.K.Bisa wasu ruwayoyin tarihi a rana iran ta yau ce manzon All..(s) ya tsaida sallar Jumma’a ta farko a cikin kabilar Bani Saalim bin Auf da ke kuba kuda da Madina. Manzon All..(s) bayan hijirarsa daga Makkazuwa madina ya tsaya a wani wurida ake kira Kuba inda ranar Jumma’a tasame shi awurinsai a lokacin sallar Azahar ya yi khubobi biyu ya kuma jagoranci sallah mai raka’oee biyu. Wannan yana nuna muhimmancin sallar jumma’a a musulunci. Tunda manzon Al..(s) ya tsaida ita a sanda ya sami daman a farko don tsaida ita. A halinyanzu akwai masallaci a wurin don tunatarwa da wannan rana.

**Masu sauraro ko kun sacewa shekaru 37 da suka gabata aranairinta yau wato 07-Day-1357M. A dai dai lokacinda juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kusan kaiwa ga nasara,mutanen garin Qazwin sun gudanar da wata gagaruman zanga zanga ta nuna kiyayyarsu ga gwamnatin sarki sha sannan tare da yin jana’izar shahidansu.Amma sojojin sarkin sun yi kokarinhana hakan faruwa , inda suka bude masu wuta suka kara kasha wasu mutane 20. A rana tabiyu sukasake fita don yi wa shahidan su jan’iza sojojin suka sake bude masu wuta. Wannan halin ya ci gaba na wasu kwanaki. Inda mutanen sauran garuruwan masuka dauka .suma suka soma zanga zanga. Wata guda bayan haka gwamnatinsarki shata fadi.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Day- 1358H.K. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI ya bada umurnin kafa hukumar yaki da jahilci a kasar tayadda a cikin dan karamin lokaci kowa da kuwa zai iya rubutu da karatu na matakin farko. Don wannan umurnin ne aka kafa hukumar yaki da jahilci wanda don ci gaban da aka samu a halin yanzu hukumar UNESCO ta majalisar dinkin duniya ta fitarda kasar Iran daga cikinjerinkasashen da jahilci tayiwa katutu. Ta shiga cikin jerin kasashen da suka waye. A halin yanzu dai fiye da kasha 95% na mutanen Iran sun iya rubutu da karatu.Sanna mafi yawan daliban jami’a mata ne.

================================================================

Yau Talata 08-Day-1394H.SH=17-R-Awwal-1437H.K.=29-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1490 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-R-Awwal-Shekaru 53 kafin Hijira kamariyya. Aka haifi fiyayyen halittun Mohammad Dan Abdullahi (q) a birnin Makka. Bisa ruwayoyin daga iyalan gidan manzon Al..(s) an haifi shi maraya kuma ya tashi a hannun mahaifiyarsa da kuma kakansa Abdulmuttalib. Sannan yana dan shekara 6 a duniya ya rasa mahaifiyar. Sai kuma yanadan shekara 8 ya rasa kakansa . daga nan ya koma karkashin renon Amminsa Abutalib(s). Manzon All..(s) ya tashi yana son kebancewa. Don hakan je kogon hiri don bauta da kuma tunanin kan Halittun Al.. yana shekara 40 aka fara saukarasa da alqur’ani. Sanna bayan shekaru 13 da kira a makka ya kafa daular musulunci ta farko a Madina . Kafin Rasuwarsa ya kawo karshen bautar gumaka a mafi yawan kasashen larabawa. Muna taya masu saurarommu murnar ranar haihuwar fiyayyen halittu. Mohammad Dan Abdullah.(s) da fatan All. Ya bamu cetonsa da na iyalan gidansa a ranar kiyama.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1354 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-R-Awwal- 83H.K. Aka haifi tauraro na 06 limani daga cikin iyalan gidan manzon All..(s) Wato Imam Jaafar Bin Mohammad (a) wanda aka fi saninsa da Imam Sadik (a) a madina. Imam Sadik (a) ya gudanar da shekaru 12 na farko a rayuwarsa tare da kakansa Imam Aliyu Zainul-abideen (a) sannan bayan haka ya tafiyar da wasu shekaru 19 a gaban mahaifinsa Imam Mohammad Bakir (a) bayan shahadar mahaifinsa ya karbi ragamar jagorancin al-ummar kakansa. Imam Sadik (a) ya bude jami’a ta farko a Musulunci a madina inda ya tarbiyantar da dalibai a fanononin ilmi daban daban. Jabir bin Hayyan masanin ilmin kimiyyar sinadarai na daga cikin Dalibansa. Hakanan malaman tarihi sun tabbatar da cewa Imam Sadik(a) yana da dalibai wadanda suka kai 4000 a cikin . al-ummar Musulmi . Kuma don irin damar da ya samu na yada mazhabar ahlulbaiti (a) ana danganta mazhabar shia inthna-ashariya zuwa garishi wato mazhabar jaafariyya. Wani abin lura da rayuwar Imam Sadik (a) shine dukkan limaman sunnan sun dauki karatu a gabansa ko kai tsaye ko kuma ta hanyar dalibansa. Muna taya al-ummar musulmi murnar haihuwar limami na 6 wato Imam Sadik (a).

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 109 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Day-1285H.SH. Sarki Mazuffaruddeen Kajar daya daga cikin sarakunan kajarawa a nan Iran ya sanya hannu ta amincewa da kundin tsarin mulki na farko a Iran wanda ake kira –mashrudiyya- Majalisar mutanen kasar Iran ce ta rubuta kundin tsarin mulkin bayan gwagwarmaya na shekaru masu yawa. Kundin yana da bangarori na asasi guda 50 daga baya an kara wasu 107. Wani abin lura a nan shi ne sarakunan kasar Iran daga suka zo daga baya sun gabatar da sauye saye masu yawa a cikin kundin musamman sarakunan Palawi, inda suke ciccire dokokin Musulunci suka maye su da wadanda suke karfafa mulkinsu.

================================================================

Yau Laraba 09-Day-1394H.SH=18-R-Awwal-1437H.K.=30-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1436 da suka gabata a rana irin ta yau 18-R-Awwal-01H.K. Aka fara ginin masallacin manzon All..(s) a Madina. Bayan yayi hijira daga makka zuwa madina abu na farko da ya fara yi shi ne gina masallaci da kuma gidansa. Manzon Al…(s) da kansa ya taimaka wajen gina masallacin, wanda shi ne masallaci mafi muhimmanci a Musulunci bayan masallacin kaaba. An gina masallacin da duwatsu da kuma bolo na tabo. Manzon All.. (s) yakan yi amdani da masalaci don gudanar sa ibada, shawarori, ilmintarwa, alkalanci da sauransu. Yin sallah a cikin masallacin yafi salla a wasu masallatan in banda masallacin kaaaba. A halin yanzu dai miliyoyin musulmi ne daga dukan adin duniya suke ziyartar masallacin da kuma kabarinsa da ke cikinsa a ko wace shekara.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 68 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-adecemba-1947M. Wasu kungiyoyin yan ta’adda na yahudawan Isra’ila sun kai faraki kan wasu kauyukan Palasdinawa da nufin korarsu daga kasasrsu. Da farko wato kungiyar ta kashe palasdinawa 60 a kauyen Balad sheikh . Sai kuma wasu sun jefa bom kan palasdinawa a kauyen inda suka kashe mutane 17. Yahudawan sun yi haka ne a karshen shekara 1947 da kuma farkon shekara ta 1948 don shirin shelenta kafuwar HKI a cikin watan mayun shekara ta 1948.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-day-1357H.SH . Sojojin sarki sha sun yi dirar mikiya kan masu zanga znaga nuna kiyayya ga gwamnatinsa da kuma nuna goyom baya ga Imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a lokacin. Imam khomani (a_ ya aike da sako na goyon bayan mutanensa da kuma karfafasu na ci gaba da zanga znafar har zuwa faduwar sarkunan azzalumai na kasar

Yau Alhamis 10-Day-1394H.SH=19-R-Awwal-1437H.K.=31-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 501 da suka gabata a rana irin ta yau 31-Decemba-1514M. Aka haifi Andreas Vesalius wani sanenne kuma kwarerren likita dan kasar Beljika a birnin Brussels.Vesalius ya shahara ne saboda kokarin da yayi gano yadda jikin mutum yake aiki ta hanyar rabbabesu zuwa gabbai. Da haka ne ya samar da wani sashe na ilmi mai matukar muhimmanci a ilmin likitanci. Dr Andreas Vesalius ya rubuta littafi mai suna “Ma’aikatar jikin bil’adama” inda yay i bayanin wannan ilmin.Dr Vesalius ya rasu a shekara 1564.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 324 da suka gabata a rana irin ta yau wato 31-Decemba-1691M. Robert Boyle masanin ilmin kimiyar lissafi da kuma kimiyar sinadarai dan kasar Island ya rasu. An haife shi a shekara ta 1627M, sannan ya tashi a karkashin kula na mahaifinsa wanda shi ma masanin ilmin kimiyar lissafi ko physics a kasar Britania. Robert Boyle ya sami ci gaba da sauri a lokacinda yake karatu. Sannan ci gaban ya kai ga ya gano wasu dokokin halayen iska musamman idan an takurasu. Ya kuma samar da ka’ida ta lissafinsu. Wadan nan dokoki ana kiransu da sunansa. Robert Boyle ya samar da dakin gwaje-gwaye da bincike na ilmin kimiyar sinadarai ya kuma gano muhimmancin iskar Oxsigen wajen samarda harshen wuta.

**Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 16 da suka gabata a rana irin ta yau wato 31-Decemba-1999M. Boris Yeltsin ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar Rasha sannan Vlademir Putin yam aye gurbinsa. Yeltsin ne babban sakataren jam’iyyar gurguzu a tarayyar Soviet kafin faduwarta. Yeltsin ya sauka daga mukamin babban sakataren jam’iyyar gurguzu a shekara 1987M sannan aka zabeshi kan kujerar shugaban kasar Rasha a shekara 1991. Yeltsin yayi kokarin tada komatsan tattalin arzikin Rasha tare da tainakon kasashen yamma amma hakan bai samu ba har zuwa saukarsa daga kujerar shugaban kasa.

=======================================================

Yau Jumma’a 11-Day-1394H.SH=20-R-Awwal-1437H.K.=01-Decemba-2015M.

**Yau ce daya ga watan Jeneru shekara ta 2016 Miladiyya. Mafi yawan kasashen duniya suna amfani da calendar miladiyya ne wajen irgen lokuta a shekara. Kuma na fara amfanin da kalandar miladiyya tun kimanin shekaru 700 da haihuwar annabi Isa (a). Banda haka saren daya ga watan Decemba na ko wace shekara ita ce ranar 7 ta haihuwar annabi Isa (a) a wajen kiristoci. Don haka sukan sabonda bukukuwa a cikin daren a dai dai karsfe 12 dare.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 101 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Day-1293H.SH. A dai dai lokacinda aka fara yakin duniya na daya, sojojin daular Usmania sun mamaye wasu yankunan kasar Iran wadanda suka hada da Tabriz da kuma Arumiyye. Hakan ya faru ne duk da cewa gwamnatin Kajarawa na lokacin ta shelanta cewa bata goyon bayan wani bangare. Sai dai ba’a dadeba sojojin Rasha suka shigo Iran suka kori sojojin daular Usmania sannan suma suka ci gaba da mamayar kasar Iran har suka zo kusa da birnin Tehran babban birnin Kasar. Amma juyin juya halin gurguzu da ya auku a kasar Rasha a shekara 1917M ya tilastawa sojojin Rasha janyewa daga kasar Iran.

**Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 57 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Jenerun-1959M. Juyin juya halin gurguzu ya kai ga nasara a kasar Cuba.Jagoran masu gwagwarmayan kauda gwamnatin shugaba Batisto shi ne Fudel Castro. Kasar Cuba ta zama kasa tilo mai bin tsarin siyasa na akidar gurguzu a Nahiyar Amurka kuma kusa da tarayar Amurka. Daga nan ne kasar Amurka ta dorawa kasar Cuba takunkumai daban daban wanda ya sanya mutanen kasar cikin takura da matsatsi. Hatta bayan faduwar tarayyar Soviet a shekara ta 1991 kasar Cuba ta cigaba da riko da akidar gurguzu. Wannan halin ya ci ga har zuwa karshen shekara ta 2015 da ta shude kasashen biyu suka maida huldan jakadanci .sai dai duk da haka dage takunkuman da Amurka ta dorawa cuba yana tafiyar hawainiya.

=======================================================

Yau Asabar 12-Day-1394H.SH=21-R-Awwal-1437H.K.=02-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 194 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-R-Awwal-1243H.K . Garin Irawan ya fada karkashin ikon kasar Rasha a cikin yaki na biyu tsakanin gwamnatin iran ta lokacin dakuma sojojin Rasha. Wannan yakin ya faru ne a lokacin sarki fath-Ali kajar . Shan kaye da iraniwa suka yi a wannan yakin ya kai ga yerjejeniyar da ake kira Turkemon-shay inda kasar Iran ta rasa wani yankin mai yawa daga arewacin lardin azarbajan da kuma qufqaaz.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 96 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Jeneru-1920M. Aka haifi Isaac Asimoov marubuci kuma masanin ilmin kimiyar sinadarai dan asalin kasar Rasha amma mazaunin kasar Amurla. Abinda fito da Isaac Asimoov daga cikin malamai shin korewa wajen bayani da kuma karnatarda ilmi ga dalibansa da harshe mai sauki da kuma bayanai masu gamsarwa. Asimoov yana da shahadar doktora a ilmin kimiyan sinadarai sannan ya rubuta littafai wadanda yawansu ya kai 270 daga cikinsu akwai “Jagora zuwa samaniyan dare” , duniyar da aka hukunta mata bacewa” da kuma “tafiya cikin tunani”. Isaac Asimoov ya rasu a shekara 1992M.

**Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 74 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Day-1320H.SH. Aya.Faiz Zanjoni ya rasu a nan kasar Iran. Da farko Aya. Zanjoni ya fara karatu a gaban mahaifinsa wanda shima marjaee ne. a mahaifarsa Zanjon. Daga baya ya dawo nan Tehran inda yayi karatu a gaban manya manyan malamai na zamaninsa wadanda suka hada mirza Mohammad Hassan Ostiyani da kuma mirza Abul Hassan Joloh. Bayan kamala karatu Aya. Zanjoni ya kuma garin Zanjon da zama inda ya zama marjaee ga mutanen wancan yankin a shekara 1287H.SH. Aya. Zanjoni ya yi shekaru fiye da 20 yana karantarwa kafin rasuwarsa a rana irin ta yau.

=======================================================

Yau Lahadi 13-Day-1394H.SH=22-R-Awwal-1437H.K.=03-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1433 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-R-Awwal-04H.K, Bayan da yahudawan da ake kira “Bani Nazir” suka karya alkawalinda suka kulla da manzon All..(s) bayan hijirarsa zuwa madina , manzon All..(s) da sahabbansa sun fara yiwa ganuwar bani Nazir kawanya. Bani Nazir dai daya ne daga cikin kabilun yahudawan madina wadanda suka kulla yerjejeniya da manzon Al.. (s) kan baza su yake ko cutar das hi da sauran musulmi ba kuma bazasu taimakawa wani akansu ba, sai sai gashi sun yi kokarin kasha shi. Bayan kawanya na kimani makonni biyu yahudawan basu ga taimakon da munafukai cikin musulmi suka yi masu ba sai suka mika wuya ga hukuncin manzon All..(s). suke bar garin madina da dukiyan da rakumi guda yake iya dauka.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Day-1367H.SH. Aka isar da sakon Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI ga shugaban tarayyar Soviet na karshe wato Mikail Gorbachev. A cikin sakon wanda tarihi ba zai manta das hi bay a ce “matsalarku ba ta mallaka da kuma tattalin arziki bane, a’a matsalarku itace ta yaki da ubangiji wanda ya halicci kome da kowa. Imam ya kara da cewa yanzu ina son in shaida maka cewa akidar gurguzu sai dai a nemeshi a kondon sharer tarihi. Banda haka ina kiranka da ka yi nazarin addinin musuluni da kyau, wannan ba wai don musulunci da musulmi suna bukatarka bane, a’a sai don irin kimar da addinin musulunci yake das hi na warware matsalolin bil’adama. Sai dai rashin karbar nisihar Imam Khomaini(q) tarayyar Soviet ta wargaje shekaru biyu kacal bayan wannan sakon.

**Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 23 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Jeneru-1993M. Shuwagabannin kasashen Amurka da Rasha na lokacin wato Boris Yelson da kuma George Bush (uban) sun rattaba hannu kan yerjejeniyar rage makaman nucliya ta suka mallaka. Bayan faduwar tarayyar Soviet a shekara 1991M Amurka ta zaci cewa Rasha zata mika mata kai, ta kuma zama wacce ba zata zama barazana a gareta ba. Amma gwamnatin Amurka bata wargaza ko da guna daya na makaman nukliyar da ta mallaka ba. Da kasar Rasha ta fahinci haka ita ma ta dakatar da wargaza natan. Sai dai kasashen sun sake kulla wata yerjejeniyar a cikin watan Afrilun shekara ta 2010 a wannan karon na wacce kasa zata wargaza makaman nucliyarta wanda suka fi 1550. Sai har yanzun bamu ji doriyar sun aiwatar da wannan alkawarin ba.

=======================================================

Yau Litinin 14-Day-1394H.SH=23-R-Awwal-1437H.K.=04-Decemba-2015M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1236 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-R-Awwal-201H.K. Fatima diyar Imam Musa alkazim (a) sannan kanuwar Imam aliyul Rida (a) ta isa birnin Qum a kan hanyarta ta zuwa garim Maru fadar mulkin sarki Mamoon daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa. Bayan da sarki ma’amoon dan haruna Rasheed ya tilastawa yayanta Imam Rida (a) hijira daga Madina zuwa Maru a yankin khurasan na kasar Iran da shakara guda sai Fatima (s) ta kama hanyar Maru don ziyartar yayanta Imam Rida (a). Amma da tai so garin Sawata da ken an kusa da birnin Tehran a halin yanzu sai wasu makiya suka fermata da yaki. Bayan da ta sami sarari sai tace a kaita garin Qum don taji mahaifinta Imam Musa (a) yace garin qum ta masoya iyalan gidan manzon Al..(s) ne. Amma bayan shigarta garin Qum mutanen garin sun girmamata matuka. Sai dai bata wuce kwanaki 17 da isa garin ba sai ta rasu. A halin yanzu hubbaren nata ya zama wurin ziyara da miliyoyin masoya iyalan gidan manzon Al..(s) da kuma cibiyar yada ilmin mazhabar su zuwa duk fadin duniya.

**Masu saurare ko kun san cewa shekaru 55 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Jeneru-1961M . Aka gudanar da wani taro a birnin "دارالبیضاء" na kasar Morocco, taro wanda ya hadashuwagabbanin kasashen Algeria, Ghana, Guinea, Mali, Morocco, Syria, Yemen da kuma Masar da manufar samarda wata rundunar hadin guiwa irin ta NATO don kare bukatun wadan nan kasashe a duniya. Har’ila yau akwai shirin samarda babbar kasuwa tsakanin wadan nan kasashe. Sai dai turawan yan mulkin mallaka wadanda suke jujjuya shuwagabbannin wasu da cikin wadan nan kasashe sun jefa sabani a tsakanin wandaya kaiga burinsu bai tabbata ba.

**Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irion ta yau wato 14-Day-1357H.SH. General Robert Haize mataimakin komandan sojojin sama na kasar Amurka a nahiyar Turai ya shiga kasar Iran a boye a dai dai lokacinda juyin juya halin musulunci karkashin jagorancin Imam Khomaini(q) ya kusan kaiwa ga nasara. A cikin kwanaki kimani 30 da ya zauna a Tehran General Robert Haize ya gana da sarki sha sau guda. Sanna a ganarwar ne suka bukace shi ya bar kasar sanna a kafa gwamnati mai karfi karkashin Priminister Bakhtiyar. Idan hakan bai kai ga nasara ba zasu shirya juyin mulki wanda zai donkofar da mutane. Sai bayan kwanaki kimani 30 sun yi kokarin aiwatar da dukkan zabin guda biyu amma ba wanda ya kai ga biyan bukata. Imam ya dawo daga gudun hijira ya kuma kifar da gwamnatin shay a kuma karbi ikon kasar gaba daya a karshen watan Bahman na wancan shekara.

===============================================

Yau Talata 15-Day-1394H.SH=24-Ra-Awwal-1437H.K.=05-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 325 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Jeneru-1691M. Aka buga takardun kudi na farko a duniya a birnin stokhom na kasar Sweden a nahiyar Turai. Kafin haka dai ana amfani da kudaden karfe ne masu kusruwa 4 manya da kanana. A halin yanzu kudaden na farko suna ajiye a gidan tarihi na bankin Stoklhom a kasar na Sweden.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 207 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Jenerun- 1809M. Daular Usmania ta lokacin ta kulla yerjejeniyar zaman lafiya tare da mutunta hakkin diblomasiyyar juna. Yerjejeniyar wacce ake kira “yerjejeniyar Dordonil” har’ila yau ta bukaci turawan ingila su fice daga dukkan yankunan daular Usmania ta ta mamaye, daga ciki har da kasar Masar. Sannan a nata bangaren daular Usmaniya zata hana jiragen yaki wucewa a mashigar ruwa ta Dardonil da kuma ta Bisfar. A lokacin dai kasar Ingila tana tsoron farmaki daga kasar Rasha ta lokacin, amma hakan ba zata samu ba matukan an hanata shiga tekun medeteranian.

**Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Day-1357H.SH. Daliban Jami’a a duk fadin kasar Iran sun fara wani yajin shiga aji don nuna rashin amincewarsu da ziyarar aiki wanda shugaban kasar Amurka na lokacin Jimy Cater ya kawo nan Tehra. Kasar Amurka tana riya kare hakkin bil’adama, harma tana cewa bazata kulla yerjejeniyar sayarwa shuwagabannin azzalumai makamai ba. Amma take hakkin bil’adama wanda sarki sha yake yi bai yi wani tasiri a wajen shuwagabannin Amurka. Don sun kulla yerjejeniyar sayarwa sarki sha makamai wadanda da su ne yake kashe mutanensa. Sai dai bayan ziyarar Jimy carter da watanni 13 Kacal aka kifar da gwamnatin sha sannan Iran ta zama jumhuriyar Musulunci.

Yau Laraba 16-Day-1394H.SH=25-Ra-Awwal-1437H.K.=06-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1001 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-R-Awwal-436H.K. Sayyeed Alamul Huda babban malami a mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) kuma fitaccen dalibin Allama Mufid ya rasu yana dan shekara 80 a duniya. An haifi sayyeed murtada, wanda aka fi saninsa da Alamul huda a shekara 355 H.K. a birnin Bagdaza na kasar Iraqi. Kakanni 5 ne tsakaninsa da limami na 7 wato Imam Musal Kazim (a). Alamul huda tare da dan uwanda sayyeed Radi sun fara karatu a gaban allama mufid ne bayan wani mafarki da yayi da cewa ya ga Zahra (s) ta kawo masa yayanta biyu ya karantar da su ilmi. Alamul huda ya maida gidansa wajen zuwan kowa daga cikin musulmi da wadanda ba musulmi ba, kuma daga ko wace akida don yin muhawara. Har’ila yau ya rubuta littafai sun kai 85 sannan yana da dakin ajiye littafai wanda yake dauke da littafai dubu 80. A takaice ana kiran Alamul huda a maysayin mujaddadin ilmin iyalan gidan manzon All..(s) a karni na 4 kamariyya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 97 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Jeneru-1919M. ThTheodore Roosevelt shugaban kasar Amurka na 26 ya rasu yana dan shekara 62 a duniya. An haifi Roosevelt a ranar 27 –Octoban- 1857M. Kuma ya zama shugaban kasar Amurka ne bayan kissan da aka yiwa shugaba William McKinley wanda mutu a shekara 1901M. Abubuwan masu mihimmanci da suka auku a lokacin shugabancin Roosevelt sun hada da raba kasar Panama daga Colombia da kuma fara aikin gina mashigar ruwa ta Panama. Sai kuma rushewar birnin sanfransisco sanadiyyar wata girgizan kasa wacce ba’a taba ganin irinta ba.

Roosevelt ne ya kama sansanonin sojojin Amurka na Gwantanamo bay a kasar Cuba, sannan ya kara yawan sojojin Amurka a kasar Cuba don kare gwamnatin kasar. Roosevelt ya shahara da wani karin magana da take cewa “Yi magana a hankali, sannan ka rike babbar sanda z aka ci gaba”. Wannan yana nuna irin yaudara da munafurcin da shugaban ya shahara da shi a mu’amalarshi da kasashen duniya.

**Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Day-1359H.SH. Sojojin Sadam Husain na kasar Iraqi wadanda suke mamaye da wasu sassan kasar kasar Iran sun kashe daliban jami’a masu masu kokarin kare huwaiza. Tare da komandarsu alamul huda.

Sojojin kasar Iraqi sun yi amfani da makamai masu karfi a kan rundunar Alamul huda wadanda mafi yawansu daliban jami’a ne. Kuma dukkaninsu sun yi shahada. Sojoojin Iraqi sun rusa garin Huwaiza bayan samun wannan nasara a farko farkon kallafeffen yakin da Iraqi da dorawa jaririyar jumhuriyar Musulunci ta Iran. Ranar 16-Day na ko wace shekara a nan Iran itace ranar shahidan daliban jami’a a yakin kare Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

==============================================================

Yau Alhamis 17-Day-1394H.SH=26-Ra-Awwal-1437H.K.=07-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 80 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Day-1314H.SH. Sarki Shan Raza Khan na kasar Iran ya bada umurnin cewa mata a duk fadin kasar su daina sa hijabi na Musulunci. Sarkin ya dau wannan matakin ne bayan da ya kai ziyara a kasar Turkiyya ya ga kuma yassa shugaban kasar Mustafa kamal Ataturk ya hana mata sanya hijabin Musulunci ya kuma tilastawa mazaje sanya kayakin al-adar turawa a kasar. Da farko sarkin ya fara ne da hana maza sanya tufafi na al-ada, sannan ya dawo kan mata. Bayan wannan umurnin jami’an tsaron sarkin sun fara wulakanta mata masu hijabi a kan titunan dukka birane da kauyukan Iran. Sai dai irin maida martani mai tsananin da malaman addini da wasu masu rajin kare hakkin mutane suka yi bayan wani lokaci sarkin ya janye umurnin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 38 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Day-1356H.SH. Wata jarida mallakin gwamnatin kasar Iran ta buka wani labarin na wulakanta Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da nufin kaskanta shi. Sarki sha ya yi haka bayan ya san irin yadda mutanen Iran suka karkata wajen son Imam. Amma bayan buga wannan wannan makalan a ranar 17-Day-1356H.SH a rannan mutane suka fara zanga zanga nuna goyon bayansu ga Imam da kuma yin Al… wadai da wulakanta shi. Wannan halin ya ci gaba har zuwa faduwar gwamnatin sarkin a a ranar 22-Bahman-na shekaran da ta biyu wato 1357H.SH. Imam ya dawo Iran ya kuma rusha gwamnatin sarkin sannan ya kafa Jumhuriyar Musulunci. Wacce har yanzun mutanen kasar Itan suke kanshi.

**Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 30 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Jenerun-1986M. Wani dansandan kan iyaka na kasar Masar mai suna Sulaiman Khadir ya halaka yahudawa masu yawa a yankin hamadar syna na kasar Masar don nuna rashin amincewarsa da yerjejeniyar Camp Devid wacce gwamnatin kasar ta kulla da HKI. Bayan kama shi da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. An yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Amma bayan wani lokacin sai labari ya fito kan cewa sulaiman khatir ya rataya kansa a cikin dakin bada magani na kurkukun da ake tsare da shi a kasar ta Masar. Daliban da jami’an da kungiyoyi daban daban a kasar Masar sun fito zanga zangar yin Al..wadai da kisan matashi.

=======================================================

Yau Jumma’a 18-Day-1394H.SH=27-Ra-Awwal-1437H.K.=08-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 374 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Jeneru-1642M. Wani masanin ilmin taurari dan kasar Italia mai suna Galileo Galilei ya rasu yana dan shekara 78 a duniya. Galileo ya tashi da karatun adabin harshen Italiyanci. Amma da ya kai shekara 19 a duniya sai ya shiga neman ilmin taurari inda ya gina madubin hangen nesa na farko ya kuma gano wasu abubuwan masu ban mamaki wadanda suka hada da cewa duniyar da muke ciki tana zagaya rana kuma akwai taurari masu yawa wadanda suke zagaye ranar. Kuma duniyar tana juyawa sau guda da kanta sau guda a ko wace rana da yini. Ko da yeka kafinsa Abu Raihan Biruni wani masanin ilmin taurari msusulmi ya gano hakan karnuka da dama kafin sa. Sai dai malaman kiristoci sun yi ca a kansa wanda ya kaiga aka gurfanar da shi a gaban kuliya inda ya karyata kansa don tsira da ransa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 83 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Jeneru-1932M. Sarki Abdul aziz tare da taimakon turawann Britania ya kafa daular mai suna sa’udiyya a kasar Najadu da Hijas. Kafin haka dai Abdulaziz ya bella yakin Hijas daga daular Usmaniyya a karshen karni na 19 da kuma farkon karni na 20 miladiya. Sannan bayan faduwar daular Usmaniyya a karshen yakin duniya na daya . Abdulaziz tare da taimakon turawan Ingila ya kwace yankin Hijaza wadanda suka hada da makka da madina daga ikon Husain Bin Ali wanda aka fi saninsa da sharifu Makka. Sai kuma a shekara 1932M bayan wata yerjeejniya da suka kulla da turawa a Jidda, Abdulaziz ya shelanta kafuyar kasar Saudia a yankunan Najad da kuma Hijaz. Sannan shine sarkinta. Tun lokacin ne kasar saudia ta fara tilastwa sauran musulmin yankin da kuma duniya akidar wahhabiyanci na kafirta duk wanda baya binsu.

**Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 47 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-R-Awwal-1390H.K. Aya. Uzama Sayyed Muhsin Hakim babban marja’ee na mabiya mazhabar ahlulbaiti ya rasu a kasar Iraqi. An haifi Aya. Hakima a kasar Iraqi a shekara 1306H.K. ya tashi ya fara karatu a gaban manya manyan malamai wadanda suka hada da . Aya. Okhunde Khurasani, Aya. Mirza Na’eenee da kuma Aya. Diya’u Iraqi. Daga karshen Aya. Muhsin Hakim ya zama babban marjanee na duniyar shi’a . inda ya himmatu da harkokin siyasa , wanda suka hada da jagorancin boren shekara 1920 kan turawan ingila yan mulkin mallaka. Sannan bayan da jam’iyyar Bath ta irazi ta hau kan kujerar sarauta. Ta yi kokarin wulakanta shi ta hnayar kai hare hare a kan gidajen sa da dalibansa. A cikin wannan wahalhalun ne bayan wata yar rashin lafiya sai ya rasu yana dan shekara 84 a duniya.

==============================================.

Yau Asabar 19-Day-1394H.SH=28-R-Awwal-1437H.K.=09-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 94 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Jeneru-1922M. Aka haifi Ahmed Seko Ture na kasar Guinea. Ahmed ya shahara tun yana matashi kan ikidarsa ta gwagwarmaya da turawan Faransa yan mulkin mallaka wadanda suke mamaye da kasarsa. Wannan ya kais hi ga kafa jam’iyyar kare democradiyya Guinea a shekara 1952, ya kuma zama shugabanta. Wannan hali ya ci gaba har zuwa shekara 1958M a lokacinda Turawan Faransa suka ga ba sarki sai Al.. suka mikawa mutanen kasar Guinea encin kasu. Shekara guda bayan haka ne aka zabi Ahmed Seko Ture a matsayin shugaban kasar Guinea. A bangaren siyada dai seko Ture ya fi karkata da ikidar gurguzu. Kuma an yi ta zabensa a matsayin shugabar kasar Guinea har sau biyar, a karo na biyar ne bai kammala ba sai ya rasu a shekara 1984M. A lokacinda ya rasu dai Ahmed Seko Ture yana rike da shugabancin kungiyar Hadin kan kasashen Afrika.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 56 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Jeneru-1960M. Aka fara gina madatsar ruwa ta Aswan a kan kogin nilu a kasar Masar. Shugaban kasar Masar na Lokacin Jamal Abdunnasir ne ya fara aikin gina madatsar, wanda ya kasance shiri mafi muhimmanci da ya yi na bunkasa tattalin arzikin kasar. Shugaba Abdunnasir ya bayyana wannan shirin ne a shekara 1953M, inda kasashen yamma sun bayyana anniyarsu ta taimakawa don ganin hakan ya tabbata. Amma bayan da Abdunnasir ta shelanta mashigar ruwa ta swiz ta zama ta kasa a shekara 1956M, da kuma yakin da ya shiga tare da kasashen Faransa, Ingila da HKI , kasashen yamma sun juya masa baya. Daga nan ne Tarayyar Soviet bejewa Masar kudade da kwararru don ginin madatsar.

Madatsan Ruwa ta Aswan dai tana da tsawon mita 114 sannan tana da fadin mita 3,600. Sannan tana tsare ruwa mai yawan cubic mita 21,000. Tana samat da wutan lantarki da kuma ayyukan noma.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 29 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Day-1365H.SH. Sojojin kasar Iran a lokacin kallafeffen yaki na shekaru 8, sun aiwatar da wani farmaki a gabacin birnin Basra, birni na biyu mafi girma a kasar Iraqi. Inda suka lalata jiragen yaki 80. Motocin yaki da tankoki kimani 700. Har’ila yau sun yi asasar duban daruruwan sojoji, tsakanin wadanda aka kashe ko aka raunata ko kuma aka kama da ransu. Wannan farmaki mai suna karbala 5 ya girgiza gwamnmatin kasar Iraqi ta Lokacin.

=======================================================

Yau Lahadi 20-Day-1394H.SH=29-R-Awwal-1437H.K.=10-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 96 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Jeneru-1920M. Majalisar kasashen duniya wacce ake kira “Leaque of Nation “. Ta fara aiki a birnin Geneva na kasar Autria. Manya manyan kasashen duniya a lokacin dai sun amince da kafuwar majalisar a bake ne kawai. Don kasashen Amurka, Britania da Faransa duk sun taimaka da kafuwar majalisar ammam basa da wakili a cikinta. Wannan ya kai ga duk abinda majalisar ta tsayar baya aiwatuwa hatta a cikin kasashen da suke da jakadu a cikin Majalisar. Banda haka kasashen Afrika gaba daya basa da wakilai a majalisar. Bil’hasali ma suna karkashin mulkin mallaka na kasashen Turai. Wannan halin ya sa a farkon yakin duniya na biyu kasashen Jamus da Italia suka fice daga majalisar sannan suka soma yakin duniya na biyu. Bayan yakin duniya na biyu ne aka kafa Majalisar dinkin duniya ta yanzu a cikin watann Afrilun-1946. Wacce itama take da matsaloli cikin tsarin gudanarwanta.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Jenerun -1963M. Wasu masana ilmin kimiyar lissafi bangaren lantarki , Titus, da Solvil. Sun kere agogo mai aiki ta wutan lantarki na farko a duniya. Masanan guda biyu dai sun yi ta kokarin hakan har na tsawon shekaru 12 kafin su kai ga nasara kere shi a rana irin ta yau. A cikin agogon mai aiki da batiri ko lantarki dai mutsawar electron ne suke tura hannayen agogon babba da karami. Kuskuren agogi mai amfani da batiri dai kadan ne sosai.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Day-1360H.SH. Wasu yan ta’adda daga cikin kungiyoyin masu adawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a nan Tehran sun yi kokarin kashe Hujjatul Islam Sayyeed Muhammad Khaminaee kani ga Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran, amma basu sami nasarar kashe ba. A farko farkon juyin juya halin Musulunci dai kungiyoyin masu adawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kashe fitattun malamai musamman wadanda suke gudanar da harkokin gwamnati a kasar. A wannan karon dai Hujjatul Islam Mohammad Khaminaee dan majalisar shoora Islami ne, a dai dai lokacinda ya ke shirin fita zuwa majalisa ne yan ta’addan suka kai masa hari suka ji masa ciwo a hannu, ama suka kashe masu gadinsa su biyu.

==============================================.

Yau Litinin 21-Day-1394H.SH=30-R-Awwal-1437H.K.=11-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 24 da suka gabata a ran airin ta yau wato 11-Jeneru-1992M. Shugaban kasar Algeria na lokacin shazili bin Jadid ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar. Shazili yah au kan kijerar shugabancin kasar Algeria ne tun shekara 1978 M, sannan a shekara ta 1988 ya yi alkawarin kawo gyare gyare a tsarin siyasar kasar bayan boren da mutanen kasar suka yi. Sai kuma a shekara 1998 aka kafa Jam’iyyar FIS (islamin salvation Front ) ta masu kishin addini. Sai kuma a zaben larduna da aka gudanar a shekara ta 1990 jam’iyyar Fis ta kwace iko da mafi yawan lardunan kasar daga hannun jam’iyyar mai mulki fiye da shekaru 30. Sai kuma a shekara 1991 M yajin aikin da mutanen kasar suka yi ya tislatawa shazili gudanar da zaben majalisar dokokin na kasar a cikin watan Decembar shekar, wanda har’ila yau jam’iyyar fis ta lashe mafi yawna kujerunsa. Wannan ya tsoratar da sojojin kasar suka tilastawa Shazili sauka daga kujerar shugabancin kasar suka kwace mulki suka kuma yi watsi da sakamakon zaben.

**Masu sauraro ko kun san shekaru 4 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Day-1390H.SH. Mustafa Ahmad Rushan injiniyan makamashin Nuclear ya yi shahada sanadiyyar bom wanda wasu ma’aikatan hukumar Mosad ta HKI suka likawa motarsa a wani wuri a nan birnin Tehran. Enginea Ahmad Rushan shi masanin ilmin fasahar nuklia na 4 wanda yahudawan suka kashe don gurgunta shirin nucliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

An haife shi a shekara 1358 a wani kauye kuda da garin Hamedan. Ya kammala digirinsa na farko a fannin kimiyyar sinadarai. A rana irin ta yau ne ya fita zuwa wajen aikinsa, inda ma’aikatan Mosad suka makala Bom a jigin motarsa wanda ya yi sanadiyyar shahadarsa da kuma direbansa Rida Kashqayee.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 2 da suka gabata arana irin ta yau wato 11-Jenrun -2014M. Ariel Sharon dan siyasa kuma sojan HKI yam utu. An haife Sharon shekara 1928 a wani kauye a kasar Palasdinu wacce take karkashin renon turawan ingila a lokacin. Mahaifinsa yayi hijira ne daga kasar Rasha zuwa Palasdinu a cikin shirin da suke yin a kafa HKI a Palasdinu. Sharon ya shiga wata kungiyan yan ta’adda wacce ake kira Hogono wacce aikinta shi ne kashe Palasdinawa da kuma korarsu daga kasarsu don tabbatar da gurinsu na kafa HKI a kasar ta Palasdinu.

A shekara 1948M bayan shelanta kafa HKI Sharon komanda ne na sojojin yahudawan HKI a yaki na farko tsakanin Larabawa da yahudawan . Sai kuma a shekara 1970 ya zama dan majalisar dokokin HKI ( Kenst). Har’ila yau ya taba zama ministen yakin haramtacciyar kasar. Sannan shi ne ya jagoranci kisan Palasdinawa 3300 a sansanoninsu da ke Sabra da Shitali a cikin kasar Lebanon a shekara 1982M. Sharon a matsayinsa na Priministan HKI daga Jam’iyyar Lekut ya shiga masallacin al-aqsa a shekara ta 2000 wanda ya yi sanadiyyar boren Palasdinawa na farko . Sai kuma a shekara 2005 an tilasta masa jenye sojojinsa daga yankin Gaza. Daga karshe ya sami bugon kwokwalwa a shekara 2006 wanda ya maida shi asbiti a kwance har zuwa halakarsa a rana irin ta yau. Ba’a taba samon ba yahuden da yafe Sharon kekeshewar zuciya ba.

=======================================================

Yau Talata 22-Day-1394H.SH=01-R-Thani-1437H.K.=12-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 351 da suka gabata a ran airin ta yau wato 12-Jeneru-1665M. Pierre de Fermat wani masanin ilmin lissafi dan kasar Faransa ya rasu. An haifi shi a shekara 1601 sannan ya fara karatun lissafi tun yana karimi. Abinda ya fito da Pierre de Fermat shine nasarar da ya sanu ba warware matsalolin lissafi wadanda suka hada da Difrancial. Inda ya samar da ka’idoji na lissafinsa da kuma wasu da dama. Pierre de Fermat ya rubuta littafai da dama kan ilmin lissafi daga cikinsu muna iya ambaton –Dangane da Maximom da Minimum.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Day-1357H.SH. A dai dai lokacinda juyin juya halin Musulunci a nan Iran ya kusan kaiwa ga nasara Imam Khomaini (q) wanda a lokacin yake gudun hijira a birnin Paris na kasar Faransa ya bada umurnin kafa majalisar juyin juya hali wacce zata kula da yadda ake gudanar da zanga zanga da kuma tsara duk abinda yakamata a yi a kokarin kawo karshen gwamnatin sarki sha. Imam ya bayyana cewa majalisar ce zata kula da kafa gwamnatin wucin gadi da kuma tsara dokoki na wucin gadi kafin a zabi majalisar dokokin kasar. Majalisar ta kawo karshen ayyukanta ne bayan kafa majalisar shoora Islamy wacce wakilanta mutanene suka zabesu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 6 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Jeneru-2010M. An yi wata girgizan kasa mai kirfin ma’aunin Richter 7 a kasar Haiti wanda yake yankin carabian a nahiyar Amurka. Girgizan kasar dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 300.sannan ya rusa kusan dukkan gine gine masu amfani a kasar. Daga cikin fadan shugaban kasar na Haiti shi ma ya rushe. An dade dai da aukuwar irin wannan gargizan kasa a duniya. Bayan girgizan da kadan ne masu ceto daga ciki da wajen kasar suka fara aiki sannan taimakon gaggawa na tsugunar da wadanda suka rasa gidajencu duk suka fara aiki.

==============================================.

Yau Laraba 23-Day-1394H.SH=02-R-Thani-1437H.K.=13-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a ran airin ta yau wato 23-Day-1357H.SH. A dai dai lokacina Sarki Sha ya debe tsammanin daga murkushe masu zanga zangar kinsa da kuma goyon bayan Imam Khomaini (q) sai ya kafa wani komiti na shirya sauya mulki daga hannunsa zuwa dansa don kada mulkin Iran ya fita daga hannun dangin Pahlawi. Amma bayan da labarin ya wastu mutane sun fito kan tituna suna nuna goyon bayansu ga Imam Khomai(a). Sannan Imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a birnin Paris na kasar Faransa ya bada sanarwan cewa zai kafa gwamnati na juyin juya hali ne bayan faduwar gwamnatin sarki sha. Bayan haka ne shugaban komitin sarkin ya mika don mika mulki ga dansa Jalaluddeen Tehran ya kama hanyar Paris inda ya nemi ganin Imam Khomani(q). Sai Imam ya ce ba zai zauna da shi ba sai ya sauka daga shugabancin komitin da kuma bayyana rashin halaccinsa. Da haka ne jalaluddeen ya bayyan saukarsa da kuma rashin halaccin komitin. Da haka aka kawo karshen komitin.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Day-1357H.SH. A dai dai lokacinda juyin juya halin Musulunci a nan Iran ya kusan kaiwa ga nasara. Daliban jami’oee da dama a iran sun tsaida shawarar shiga cikin mutanen Iran wajen nuna rashin amincewarsu da gwamnatin sarki sha da kuma bukatar Imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a birnin Paris na kasar Faransa da ya dawo gida. Sannan a rana irin ta yau ce Imam ya aika da wani sako wanda a cikin ya bukaci mutane su yi hankali da makircin gwamnatin sarkin su bude idanunsu da hankalinsu don fahintar duk wani makircin da zasu kulla don raba kan mutane.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Day-1359H.SH. Sojojin Sadam Husain na kasar Iraqi sun fara amfani da makaman guba a karon farko kan sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wani wuri mai tazaran kilomita 50 daga garin Ilam daga yammacin kasar, kuma watanni 4 kacal da fara kallafeffen yaki na tsawon shekaru 8.

Duk da cewa an haramta amfani da makaman guma a yaki, amma kasashen duniya musamman masu kojerun din din din a komitin tsaro na majalisar dinkin duniya sun yi shiru kan wannan ta’asan. Wannan kuma ba kome bane don su suka tallafawa sadam Husain wajen samar da makaman na gubu da kuma ingiza shi ya yi amfani da su kan iraniywa sojojinsu da farar hula. Kafin a kare yakin mutane nan kimani dubu 10 suka yi shahada sanadiyar makaman guba sannan wasu dubu 130 kuma suka ji rauni sanadiyyarsu.

=======================================================.

Yau Alhamis 24-Day-1394H.SH=03-R-Thani-1437H.K.=14-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 74 da suka gabata a ran airin ta yau wato 14-Jeneru-1942M. Wasu shuwagabannin kasashe masu kawance a yakin duniya na biyu sun gudanar da wani taro mai muhimmanci a birnin casablanka na bakin ruwa a kasar Morocco. Shugaban kasar Amurka Roservel, Priministan kasar Britania Chesil, da shugaban kasar Faransa Digol da kuma wakilan kasashen Tarayyar Soviet da sauransu sun halarci wannan taron na kwanaki 10. Inda a karshen taron suka fidda rahoton hadin guiwa na cewa zasu ci gaba da yakar bangaren kasashe masu hadin kai wato Jamusa da kawayenta har sai sun mika kai ba tare da wani sharadi ba.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Jenerun-1991M. Hukumar leken asiri Mosad ta HKI ta kai hari a cikin kasar Tunisia inda ta kashe Salah Khalaf wani jigo a cikin komitin koli kuma jami’an tsaro a kungiyar PLO ta gwagwarmayan kwatar encin Palasdinawa. Ba wannan ne karon farko wanda Mosad take kashe jagororin PLO ba, amma a wannan karon sun shiga wata kasa ba tare da kiyaye dokokin kasa da kasa na mutunta kasashen duniya ba, sannan ta aikata wannan laifin. Sai dai a bin mamaki shi a cikin watan Octoba na wancan shekaran wato 1991 sai aka fara wai tattaunawar sulhu tsakanin kungiyar ta PLO da kuma HKI.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 5 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-ajenerun -2011M. Shugaban kasar Tunisia Zainul –abiden bin Ali bayan ya kasa kwanatar da zanga zangar kin gwamnatinsa wanda mutanen kasarsa suke yi ya arce daga kasar ya sami mafaka a kasar saudia. Bin Ali yah au kan kujerar shugabancin kasar Tunisia ne a shekara 1987 a bayan wani juyin mulkin da ya jagoranta wanda kuma ya kifar da gwamnatin Habib Bogiba na tsawon shekaru 33. Masomin boren mutane a kasar Tunisia dai shi ne wani matashi mai saida kayan miya wanda ya gaji da zaluncin shuwagabannin kasar sai ya kona kansa da wuta. Faduwar gwamnatin bin Ali na shekaru 23 ya farkar da mutanen kasashen Larabawa wanda ake kira “farkawar Musulmi” a yankin gabas ta tsakiya.

==========================================================.

Yau Jumma’a 25-Day-1394H.SH=04-R-Thani-1437H.K.=15-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1264 da suka gabata a ran airin ta yau wato 04-R-Thani-173H.K. Aka haife Sayyeed Abdul azeem Alhasani daya daga cikin manya manyan malaman shi’a wanda ya kasance jikan Imam Hasan al-mujataba (a) a garin Madina. Sayyeed Abdul azeen alhasani ya ruwaito hadisai kai tsaye daga Limamai ukku wato Imam Aliyu bin Musa(a), Mohammadul Jawad (a) da kuma Imam Aliyul Hadi (a). A lokacin limamancin Imam Hadi ne , tare da umurninsa Sayyeed Abdul-azeem alhasani ya yi hijira zuwa garin rai wanda yake kusa da birnin Tehran a halin yanzu inda ya ci gaba da shiryatar da mutane. Sayyed Abdul azeem ya yi shehada a shekara ta 250 H.K. a halin yanzu akwai hubbarensa a garin rai inda miliyoyin masoyan iyalan gidan manzon All..(s) suke ziyartarsa.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Day-1357H.K. A dai dai lokacinda juyin juya halin Musulunci a nan Iran ya kusan kaiwa ga nasara, wasu bangare na sojojin kasar Iran sun arce daga barikokinsu sun kuma shiga cikin mutane masu zanga zangar yin All… wadai da gwamnatin sarki sha. Tun lokacin ne sojojin kasar suka fara barin barikokinsu suna shiga cikin mutane masu zanga zanga. Wanda ya kara bawa mutanen kasar Iran karfin guiwa na ci gaba da zanga zangarsu. A dayan bangaren kuma bayan da labari ya isa kunnen Imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a kasar faransa a lokacin ya aike da sako zuwa sojojin kasar Iran da su bar nuna goyon bayan da tagutu su dawo cikin sahun mutane su kare addinin Musulunci.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 15 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Jeneru-2001M. Aka bude shafin yanar gizo ta Wikipedia wanda ya tattara rumbuna ilmi da bayanai cikin harsuna daban daban a duniya. Wani abinda ya kebenci Wikipedia da sauran shafuffukan ilmi shi ne kowa yana iya kara labarai a cikinsa sannan ya taba dukkan bangarori na rayuwa. Sai dai wani abin lura a nan shi ne shafin Wikipedia yana dauke da asirin wasu kasashen musamman Amurka da HKI wadanda basa son duniya ta sani. Wannan ya sa wadanda kasashe basu ji dajen wannan rumbun ilmin da bayanai ba. Cibiyar Wikipedia dai tana birnin Florida na kasar Amurka.

==========================================================.

Yau Asabar 26-Day-1394H.SH=05-R-Thani-1437H.K.=16-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 170 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Jeneru-1846M. Amurka ta soma kaiwa kasar Mexico hare hare. Dalilan da Washington ta bayar na soma yaki fin karfi shi ne wai ana cutar da yan kasar Amurka mazauna cikin kasar Mexico. Daga karshe dai Amurka ta kwace iko da wasu yankuna na kasar Mexico ta shigar da su cikin kasarta. Yankunan dai suna hana da jihohin Texas, Kalifonia, Nawado, Yuto, Arizona da kuma New Mexico.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 109 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-R-Thani-1328H.K. Sattar Khan da kuma Bakir Khan daga cikin shuwagabannin gwagwarmayan da ake kira "Mashrudiyya anan Iran sun jagoranci mayakansu daga birnin Tabriz zuwa Tehran tare da samun nasara waje kwace Tehran daga hannun sarakuna na lokacin. Kafin haka dai sojojin sarakunan kajarawa sun killace Sattar Khan da mayakansa a cikin garin Tabriz na tsawon watanni 11 da nufin murkushe yunkurinsu na samar da tsarin mulki na farko a iran don rage zaluncin da sarakuna suke yiwa mutanen kasar Iran. Tare da taimakon mutanen garin na Tabriza sun sami nasara a kan sojojin sarakunan Kajar sannan daga karshe sun kwace iko da Tehran, wanda ya tabbatar da nasara a garesu.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Day-1357H.SH. Sarki Muhammad Riza Khan ya arci daga kasar Iran da sunan zuwa neman magani a kasashen waje. Kafin haka dai sarkin ya kasa murkushe borin da mutanen kasar suke yiwa gwamnatinsa da kuma goyon bayan da suke bawa Imam Khomaini (q). Bayan arcewarsa daga Kasar Mutanen sun ji dadi, sannan Imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a birnin Paris na kasar Faransa a lokacin ya aike da sako kan cewa arcewar sha daga Iran ba tare da ya bayyan saukar da daga kujerar sarautar kasar ba, bai zai tsinana kome ba.

Mohammad Riza Pahlawi dai yah au kan kujerar sarautar kasar Iran ne bayan da turawan ingila suka mamaye kasar Iran a cikin yakin duniya na biyu suka tube mahaifinsa daga kujerar sarautar kasar suke kore shi daga kasar sannan suka nada Muhammad riza dansa a matsayin magajinsa.

==========================================================.

Yau Lahadi 27-Day-1394H.SH=06-R-Thani-1437H.K.=17-Jeneru-2016M.

**Masu sauararo ku kun san cewa shekaru 1312 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-R-Thani-125H.K. Hisham dan Abdulmalik dan Marwan dan Hakam khalifan na 10 daga cikin khalifofin bani umayya ya mutu. An haife shi a shekara ta 72 H.K. kuma ya hau kan kujerar khalifanci ne a shekara ta 105H.K. Hisham ya shahara da rowa, kekashewar zuciya da kuma zalunci musamman kan iyalan gidan manzon Al..(s) da mabiyansu. Hisham ya hada zamani da Imam Mohammad bin Ali (a) wanda aka fi saninsa da Imam Bakirul-Ulum. Jikan manzon All..(a) na ukku. Hisham ya takura masa har ya kai daga karshe ya bada umurnin kasha shi. Ban haka Hisham ya murkushe yunkurin Zaid dan Ali (a) ya kasheshi sannan yasa aka kona gawarsa. A karshen mulkin sa anyi ta samun yan tawaye don yawan zaluncinsa, wanda ya kai ga shekaru 7 kachal da mutuwarsa Abbasiyawa suka kawo karshen mulkin bani umayya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 60 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Day-1334H.SH. Sayyeed Mustafa Nawwab Safawi daya daga cikin fitattun malaman addini masu gwagwarmaya da sarakun palawi a nan Iran ya yi shahada. An haifi Nawwab Safawi a cikin dangi na malaman addini a nan Iran a shekara ta 1305H.SH. Sayyeed Safawi ya yi karatu ne a makarantar hauda da ke birnin Najaf na kasar Iraqi. bayan kamala karatunsa ya dawo Inya, inda ya kafa wata kungiyar ta gwagwarmaya da azzaluman sarakunan kasar wacce ake kira "Fi'daeyyuna Islam". A cikin wannan halin ne jami'an tsaron sarki sha suka kama shi tare da wasu abokan aikinsa su hudu. Bayan an gurfanar da su a gaban kotun soje an yanke masu hukuncin kisa an kamu zartar da shi a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Day-1366H.SH. Sayyeed Mahdee Hakim da ga sayyeed Muhsin Hakim babban marja'een shia a kasar Iraqi ya yi shahada. Sayyed Mahdee Hakim memba ne a cikin Majalisar Koli ta addinin Musulunci a kasar Iraqi. Kuma dalibi ne ga shaheed Aya. Bakir Sadar. Bayan da jam'iyyar Baath mai mulkin kasar Iraqi a lokacin karkashin shugabancin Sadam Husain ta yi barazanar kashe shi ya yi hijira zuwa birnin Karthun na kasar Sudan. Sai dai bayan wani lokaci Jami'an liken asiri na gwamtanin Iraqin sun bishi har sudan suka kashe shi a rana irin ta yau.

=============================================.

Yau Litinin 28-Day-1394H.SH=07-R-Thani-1437H.K.=18-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 97 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Jeneru-1919M Aka gudanar taron sulhu na farko bayan yakin duniya na daya a Fadar Waso na kasar Faransa. Wakilan kasashe 27 ne suka samu halattan taron, sannan kasashe biyar da suka sha kaye a yakin, wato daular Usmania, Bulgeria, Hungary Jamus da kuma Austria basu halarci taron ba. A karshen taron dai an dorawa kasar Jamus diyya mai nauyi sanya an tilasta mata mika wasu yankuna na kasar ga hadakar kawancen da suka sami nasara a kansu. Bayan yankin da kadan ne daular Usmaniyya ta wargeje sannan a taron ne aka fara zancen kafa majalisar kasashen duniya wacce ake kira Leaque of Nation.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 12 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-R-Thani-1425H.K. Aya. Sayyeed Abul-Hassan Maulan daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan kasar Iran ya rasu. Aya. Maulana ya fara karatu a gaban malaman zamaninsa. Sannan yana dan shekara 19 a duniya yak aura daga mahaifarsa zuwa birnin Qum inda ya kamala karatunsa a gaban manya manyna malamai a birnin. Bayan shekaru 14 Aya. Abul-Hasan maulana ya kamala karatunsa ya kuma fara karantarwa da bincike da kuma rubuce rubuce. Aya Maulana ya ci gaba ta karantarwa har zuwa rasuwarsa a rana irin ta yau.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 10 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-R-Thani-1427H.K. Aya. Nimatullah Salihi Najaf0abadi wani babban malamin addini ya rasu a nan Iran. Aya. Najaf-Abadi yana daga cikin daliban Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI. Da kuma Allamah Taba tabai. Yana daga cikin malaman da suke goyon bayan Imam (q). Bayan nasaral juyin juya halin musulunci ya ci gaba da karantarwa a birnin Qum har zuwa rasuwarsa a rana irin ta yau. Littafi mai syna "ولایه الفقیه" na daga cikin littafansa da suka shahara.

================================================Yau Talata 29-Day-1394H.SH=08-R-Thani-1437H.K.=19-Jeneru-2016M.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1205 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-R-Thani-232H.K. Aka haifi limami na 11 daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All…(s) a madina. Imam Hassan al-askari (a) yana karamin yaro sarakunan Abbasiyawa na lokacin suka tilastawa mahainsa Imam al-hadi (a) hijira daga Madina zuwa cibiyar mulkinsu dage Samira na kasar Iraqi. Imam Hassan Al-askari ya share shekaru 13 yana karatu a gaban mahaifinsa. Imam Hassan al-askari (a) yana dan shekara 27 a rayuwarsa mahaifnsa imam al-hadi (a) yay i shahada sannan jagorancin al-ummar kakansa ya koma kansa. A cikin shekaru biyar da ya jagoranci al-ummar kakakansa ya kammalasu a cikin kora ko kuma cikin kurkukun sarakunan Abbasiyawa. Muna taya al-ummar musulmi murnan haihuwar Imam Hassan Al-askari (a).

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 280 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Jeneru-1736M. Aka haifi James Watt wani masanin ilmin kimiyyar lissafi dan kasar Britania. Watt ya tashi da sha'awar karatun ilmin kimiyyar lissafi don haka bayan kamala karatunsa ya shiga cikin binncike har zuwa lokacinda ya kirkiri inji mai amfani da tururi wajen motsa jiragen ruwa. Ko kuma locomotive wato jiragen kasa masu amfani da tururi. Watt ya rasu a shekara ta 1819M yana dan shekara 81 a duniya.

**Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 6 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Jeneru-2011M. Jami'an hukumar liken asiri na haramtacciyar kasar Isra'ila sun kashe Mahmood Mabhooh wani jigo a cikin kungiyar Hamas wacce take gwagwarmaya da makamai don kwatar encin Palasdinawa a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar daular larabawa.

Jami'an Mos

Add comment


Security code
Refresh