An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 28 December 2015 07:15

Hasarar Hare-Haren Wuce Gona Da Irin Masarautar Saudiyya Kan Kasar Yamen

Hasarar Hare-Haren Wuce Gona Da Irin Masarautar Saudiyya Kan Kasar Yamen
Tun bayan da masarautar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen daga watan Maris na wannan shekara zuwa yanzu ta kashe mutane fiye da 7,000 musamman mata da kananan yara.

 

Cibiyar Kare Hakkin Bil-Adama da Bunkasa Kasa ta Kasar Yamen ta fitar da rahoton cewa;Yawan mutanen da suka rasa rayukansu tun bayan da masarautar Saudiyya da kawayenta suka fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen a cikin watan Maris na wannan shekara zuwa yanzu, mutane fiye da 7,000 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu fiye da 14,000 suka samu raunuka kuma mafi yawansu mata da kananan yara da tsofaffi.

Rahoton ya kara da cewa: Daga cikin mutane 7,000 da suka rasa rayukansu, kimanin 2000 kananan yara ne, yayin da yawan matan da suka bakwanci lahira sakamakon hare-haren zaluncin suka haura 1000, sannan daga cikin mutanen da suka samu raunuka da yawansu ya haura 14,000, mata da kananan yara ne masifar tafi ritsawa da su.

Har ila yau luguden wuta da jiragen saman yakin masarautar Saudiyya da kawayenta suke yi kan yankuna daban daban na kasar Yamen, ya tilastawa mutane fiye da 900,000 barin gidajensu musamman sakamakon rushewar gidajen ko kuma a kokarin tsira da rayuwa.

Haka zalika hare-haren wuce gona da irin jiragen yakin masarautar Saudiyya kan sassa daban daban na kasar Yamen ya janyo rushe-rushen ma’aikatu da cibiyoyi gami da masana’antu da jami’o’i, asibitoci, Masallatai, makarantun gwamnati da na masu zaman kansu, kafofin watsa labarai da duk wani abu mai amfani a kasar.

Rahoton Cibiyar Kare Hakkin Bil-Adama da Bunkasa Kasa ta Kasar Yamen ya kara da cewa; Karacin magunguna da wajajen kula da marassa lafiya gami da rashin hasken wutan lantarki sun wurga harkar kiwon lafiya a Yamen cikin mawuyacin hali, lamarin da zai iya janyo habakar mutuwar mutane tare da karin bullar cututtuka a kasar.

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta kasa da kasa ta Human Rights Watch ta bayyana cewa; Hare-haren wuce gona da irin masarautar Saudiyya kan kasar Yamen shi ne laifin cin zarafin bil-Adama mafi girma da aka tafka a duniya a cikin wannan shekara ta 2015 da muke ciki musamman a fagen kashe fararen hula marassa galihu.

Mahukuntan Saudiyya dai sun shelanta yaki kan kasar Yamen ne da sunan tabbatar da dimokaradiyya ta hanyar dawo da shugaban kasar mai murabus Abdul Rabbu Hadi Mansur kan karagar shugabancin kasar, duk da cewa kasar Saudiyya bata taba shakar iskar yancin tsarin dimokaradiyya ba a tsawon tarihinta, don haka masu iya magana ke cewa; Duk wanda bai mallaki abu ba, to babu kanda zai iya bada shi. Sakamakon haka kasar da bata san mene ne tsarin dimokaradiyya b aba zata iya wanzar da shi a kan wata kasa ba, kawai dai akwai mummunar manufar da mahukuntan Saudiyya ke son cimmawa kan kasar ta Yamen, don haka mahukuntan kasar suka halatta wa kansu aiwatar da kisan gilla kan al’ummar Yamen.

Add comment


Security code
Refresh