An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 21 August 2015 13:13

Yau Laraba 01-Murdod-1394H.SH=06-Shawwal-1436H.K.=23-Yuli-2015M.

Yau Laraba 01-Murdod-1394H.SH=06-Shawwal-1436H.K.=23-Yuli-2015M.
Yau Laraba 01-Murdod-1394H.SH=06-Shawwal-1436H.K.=23-Yuli-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 63 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Yuli-1952M. Wasu matasan sojojin kasar Masar sun kifar da sarautar Sarki Faruk na kasar. An haifi Sarki Faruk a shekara ta 1920M. Mahaifinsa Ahmad Fu’ad Pahsa ya rasu yana dan shekara 16 a duniya. Amma duk da jaka ya gaje shi, sai dai harkokin gudanar da mulki ya koma ga wata majalisa da aka nada don yin hakan. Sai kuma bayan nasara da HKI ta samu kan kasashen larabawa a yaki na farko da ya hadasu a shekara 1948M, ya fusata mafi yawan mutanen kasar ta masar musamman wasu matasan sojojin kasar , wanda Jamalbdunnasir yake jagoranta. Don haka a shekara ta 1952 suka yiwa sarki Faruk juyin mulki suka kuma tilasta masa yin ritaya suka kuma yi watsi da tsarin sarauta a kasar. Bayan haka Gen. Mohammad Najib ya zama shugaban kasar na farko, amma shima bayan shekaru biyu ya mika iko ga Jamal Abdunnasir. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 186 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Yuli-1829M. Wani inginia dan kasar Amurka ya sami nasarar kirkiro na’urar typrater ta farko a duniya. William Bird dan jihar Michigan na kasar Amurka ne ya kirkiro ingin rubutu na farko a duniya, wanda wani kamfanin kera makamai a jihar ya fara kerawa da kuma saida shi. Daga baya dai wasu masanin da suka zo baya sun kara kyautata ingin na rubutu har ya zama abin amfani a duk fadon duniya. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 21 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Yuli-1994M. Wasu sojojin kasar Gambia a yammacin Afrika sun yiwa shugaba Dawda Jarara juyin mulkin a dai dai lokacinda yake ziyarar aiki a kasar Britania. Kasar Gambia dai ta sami kwarya kwaryan encin kai ne a shekara ta 1962M kuma tun lokacin ne shugaba Dawda Jawara yake iko da kasar. Sai kuma shekara guba bayan haka turawa suka bawa kasar cikekken encin kai. wato a shekara 1965M inda Dawda Jawara ya zama Priministan kasar. Sai kuma a shekara 1970 bayan ya sauya tsarin siyasar kasar zuwa tsarin jumhuriyya sai aka zabe shi a matsayin shugaban kasa. Sai kuma a shekara ta 1981 sojojin kasar suka yi masa juyin mulki a lokacin da yake ziyarar aiki a kasar Britamnia, amma tare da taimakon sojojin kasar Senegal suka murkushe juyin mulkin suka dawo da shi kan kujerar shugabancin kasar. Sau kuma a shekara ta 1984 kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta zabe shi a matsayin shugaban kungiyar, sannan ta bashi damar shiga tsakani don sasanta yakin da ke tsakanin iran da kasar Iraqi. Daga karshe an sake masa juyin mulki na biyu a ranar 23-Yuli-1994M. ************************************************************. Yau Alhamis 02-Murdod-1394H.SH=07-Shawwal-1436H.K.=24-Yuli-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1433 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Shawwal-03H.K. Aka yi yakin Uhud tsakanin Musulmi karkashin jagorancin manzon All,,,(s) da kuma mushrikan Makka. Murikan Makka sun sha kaye a yaki na farko a Badar don haka yi shirin yakin Uhudu don daukar fansa. Sun fito da mayaka 3000 tare da cikekken tanajin yaki. Musulmi kuma sun fito da mayaka 700 bayan da ya shawarci sahabbansa kan yadda za’a yi yakin, inda suka zabi fita wajen madina. Da farko dai musuli sun sami nasara kan Mushrikai, amma jim kadan bayan haka sanadiyar gafalar da wasu mayakan musulmi suka yi na sabawa manzon All… da barin inda ya umurcesu da tsayawa sai mushrikai suka zo masu ta wurin suka kashe musulmi kimani 70 daga cikinsu har da Hamza ammin manzon Al…(s) sannan sun yi barazana ga ran manzon Al..(s) a lokacin. Sai dai basu sami cikekken nasara ba don sun kasa shiga madina suka koma makka. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 52 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Murdod-1342H.SH. Bayan kama Imam Khomaini (q) wanda ya’assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda jami’an tsaron sarki sha suka yi, manya manyan malaman addinin kasar Maraja’ai daga biranen Mashad Qum , Esfahan shiraz da sauran sun sun taru a birnin Qum inda suka rubuta wasiqa suka ga sarkin don tabbatar da mar’jaiyyarsa da kuma bukatar a sake shi. Wannan ya hadu da zanga zangar da magoya bayansa suke yi a duk fadin kasar. Bayan haka dai sarkin ya bada umrnin a maida shi wani gina a birnin na Tehran, amma a hana shi haduwa damutane. Hakan ma bai kwantar da hankali ba. Daga karshe sarkin tare da shawarar wasu shuwagabannin kasashen duniya ya yanke shawarar korarsa daga kasar Iran inda da farko suka kai kasar Turkiyya sannan bayan kimani shekaru 2 zuwa kasar Iraqi inda ya ci gaba da zama har zuwa shekaru 14, suka sake korarsa daga kasar ta Iraqi daga nan ya zabi zuwa Faransa inda ya zauna na wtannin sannan ya dawo gida ya karasa jagorantar juyin muusulinci zuwa ga nasara da kuma korar gwamnatin sarkin a 22-Bahman-1357H.SH. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 232 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Yuli-1783M. Aka haifi Simon Bolivar dan siyasa kuma madugun gwagwarmayan neman encin mutanen nahiyar Amurka ta kudu a birnin Caracas na kasar Vemezuela. Simon Bolivar ya taimaka wajen samarwa kasashen kudancin Amurka da dama encin kai daga hannun turawan espania yan mulkin mallaka. Da farko dai ya jagorancin juyin juya halin birnin Caracas na kasar Venezuela, sannan tare da taimakon soji ya kwace birnin Buguto na kasar Colombia. Daga baya wata majalisa da suka kafa a yankin ta zabi Bolivar a matsayin shugaban kasar Colombia babba, wanda ya tabbata bayan samun encin kasashen Venezuela. Colombia da kuma Panama. Sai kuma a shekara 1822 simon Bolivar ya entar da kasar Ecwado wacce ita ma ta shiga cikin kasar Colombia babba. Sai kuma a shekara ta 1822 mayakan simon bolivar ya sami nasarar samarwa kasarsa Bolibia encin kai bayan gwagwarmaya na shekaru 17. Shekara guda bayan haka ya samarwa kasar Pero encin kai. Simon Bolivar dai yana da gurin entar da dukkan kasashen kudancin Amurka da kuma kafa dunkulayyar jumhuriyar kasar kudancin Amurka, amma bai sami damar hakan ba har zuwa mutuwarsa a shekara 1930M. ======================================================= Yau Asabar  03-Murdod-1394H.SH=08-Shawwal-1436H.K.=25-Yuli-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 22 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Yuli-1993M. Sojojin HKI sun soma kai hare hare ta sama da kasa da kuma kan kudancin kasar lebenon da nufin shafe kungiyar hizbulla wacce take gwagwarmaya da ita kan mamayar da takewa kasar daga samuwa. A wannan karon dai yahudawa sun kashe mutane 128 farare haula, saun raunata 500 sannan sun tilastawa wasu dubu  400 kauracewa gidajensu. Amma mutanen kasar sun ci gaba da goyon bayan wannan kungiyar har sai da ta tilastawa HKI barin kasar a cikin watan mayun -2000M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 121 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Yuli-1894M. Aka fara yaki tsakanin China da Japan, wanda ake kira yakin china/Japan. Sanadiyyar wannan yakin shi ne kasar Japan  ta ke son mamaye tsibirin Korea ta arewa wacce take karkashin kasar China. A kasar yakin dai Japan ta sami nasarar korar china daga korea ta arewa, kuma a wata yerjejeniya da suka kulla na tsagaita bude wuta, Japan ta tilastawa China mika mata wasu tsibiran wadanda ba korea ta Arewa ba.   Wannan yakin har’ila yau ya haddasa wani yaki tsakanin Japan da tarayyar Rasha don a lokacin da take yaki da China ta kai wasu hare hare kan sansanonin rojojin Rasha da ke cikin china. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 77 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Yuli-1938M. Wasu boma bomai guda biyu sun tashi a wata kasuwar ganye da kayan marmari a cikin kasar Palasdinu, inda ya yi sanadiyyar kashi Palasdinawa 62 da kuma raunata wasu fiye da 100. Wata kungiyar yan ta’adda ta yajudawan sahyonoyya ce ta tada wadan nan boma bomai . Manufarsu ita ce samar da rashin zaman lafiya a cikin Palasdinawa wanda daga karshe zasu gudu su bar Palasdinu wa yahudawa. Wannan hali ya ci gaba a cikin Palasdinu har zuwa lokacin da yahudawan suka shelanta kafuwar HKI a shekara 1948. Har’ila yau wannan halin yana ci gaba har zuwa yanzun. ****************************. Yau Lahadi 04-Murdod-1394H.SH=09-Shawwal-1436H.K.=26-Yuli-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 71 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Murdod-1323H.SH. Bayan daurin talala na tsawon shekaru 3 a wani tsibiri a kasar Afrika ta kudu, Raza Pahlawi, wanda aka fi saninsa da Riza Khan, wanda ya assasa saurautar dangin Pahlawi a kasar Iran yam utu. An haife shi a shekra 1257 H.SH a arewacin kasar Iran. Sannan a shekara 1299H.SH, a lokacinda yake aikin soje a karkashin daular Kajarawa, ya jagoranci wani juyin mulki, tare da taimakon turawan ingila, wanda ya kauda kajarawa daga kan mulki sannan ya nada kansa sarkin kasar Iran. Riza sha yayi kokarin shigo da al’adun turawa a kasar Iran ya kuma maye gurbinsu da na addinin Musulunci, amma malaman addinin sun tsaya a gabansa. Wannan halin ya ci gaba har zuwa yakin duniya na biyu, inda ya bayyana goyon bayansa ga Hitla na kasar Jamus, hakan ya sa sojojin kawance suka mamaye Iran suka tube shi suka tilasta masa hijira zuwa kasar Afrila ta kudu inda ya zauna a can na shekaru sai yam utu a rana irin ta yau. Raza khan ya yi sarauta na tsawon shekaru 16. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 59 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Yuli-1956M. Shugaban kasar Masar na lokacin Jamal Abdunnasir ya shelanta maida mashigar ruwa ta Swiz a matsin na kasa, ya kuma kafa wata hukuma ta musamman don kula da mashigar. Kafin haka dai bayar da turawan ingila suka yiwa kasar Masar, sun gida mashigar ruwa ta swiz wacce ta hada tekun Mali da kuma na Medeteranian, inda suka takaita tafiyan ruwa daga yankin Asia zuwa Turai, kuma sun ci gaba da kula da ita. Wannan halin ya ci gaba har zuwa mulkin Jamal Abdunnasir wanda ya maida iata na kasa. Sai dai bayan shelantawar kasashe ukku Faransa, Britania da kuma HKI sun farma masar da yaki sai daga karshe basu sami nasara ba. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-yuli-1979M. Hukumar leken asiri ta HKI Mosad ta kashe Zuheir Mohsen babban sakataren kungiyar Palasdinawa ta “Sa’ikah” a garin Kan na kasar Faransa. Bayan kisan Mohsen jami’an Mosad sun bar wurin, sannan jami’an tsaron kasar Faransa sun riya cewa basu ga alamar wani wanda ya kashe Mohsen ba.  sannan kamar yadda suka saba maya manyan kasashen duniya sunyi gum da bakunansu, kan kisan ko All..wadai basu yi ba. *************************** Yau Litinin 05-Murdod-1394H.SH=10-Shawwal-1436H.K.=27-Yuli-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 243 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Yuli-1772M. Manya manyan kasashen Turai na lokacin sun rattaba hannu kan rarraba kasar Poland a tsakaninsu. Manya manyan kasashen turai a lokacin dais u ne Russia, Austria and Prussia (wacce ta kasance bangaren kasar Jamus a yanzun). Wadan nan kasashe sun rarraba kasar Poland a tsakaninsu ne wai don hana ta lalacewa.  Wani abin lura shi ne, wannan shi ne karo na hudu wannan kasashen turai suke mamayar kasar Polan da wasu kasashen turai suke yi. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Murdod-1359H.K. Sarkin kasar Iran na karshe Muhammad Rida Pahlawi ya mutu a kasar Masar. An haife shi a shekara ta 1298H.SH.  Turawan ingila sun dora shi a kan kujerar sarautar kasar Iran ne bayan da suka tube mahaifinsa a dai dai lokacinda ake yakin duniya na biyu, kuma tun lokacin ne yake khidima wa turawan da kuma Amurka wajen ruf da ciki da arzikin kasar. A shekara ta 1329 sarki Muhammad Riza ya arce daga kasar bayan borin da mutane suka yi don bukatar a maida Dr Musaddiq kan kijerarsa na Priminister. Daga ka karshe sarkin ya dawo da shi kan kujerarsa shi kuma ya dawo ya ci gaba da mulkin sai kuma a shekara ta 1357h.sh Magoya bayan Imam Khomani (q) sun tilas ta masa arcewa daga kasar a karo na biyu, bayan ya kasa kwanatar da hankali a kasar. Amma nasarar da aka samu na kifar da gwamnatinsa bayan ya fice daga kasar da kuma dawowan Imam Khumani (a) wanda ya kora daga kasar na tsawon shekaru 14 ya kawo karshen mukin sa. Ba’a dade ba sarkin ya kamu da rashin lafiya ya mutu a kasar Masar. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Murdod-1367H.SH. Dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun fara wani farmaki mai suna “Mirsad” da nufin murkushe rundunar manafukai makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran wadanda suka ketare kan iyakokan kasar Iran daga kasar Iraqi da nufin murkushe gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Amma ba kamar yadda suke tsammanin ba, duk tare da taimakon da suke samu daga sojojin Sadan Husain na kasar Iraqi sojojin Iran sun murkushesu sun kuma kawo karshensu a wannan yakin. ==================================================. Yau Talata 06-Murdod-1394H.SH=11-Shawwal-1436H.K.=28-Yuli-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 1439 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Shawwal-03Kafin Hijira  Kamariyya. Manzon Al..(s) ya je garin Ta’if kusa da birnin Makka don isar da sakon Musulunci, da kuma neman mafaka ga musulmi idan sun amsa kiransa. Manzon Al…(s) ya yi wannan tafiyar ne a jim kadan bayan rasuwar amminsa kuma mai kare shi daga cutar kuraishawa ya rasu. Amma kabilar Thaqif wacce take zaune a garin, ba wai kawai sun ki amsar kiran manzon Al…(s) ba, a’a sun ma ingazi wawayen garin suka jefeshi da duwatsu suka kore shi daga garin, bayan sun ji masa ciwo. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 26 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Murdod-1368H.SH. Mutanen kasar Iran sun fito zaben shugaban kasa a karo na 5 tun bayan kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma tare da wannan zaben akwai zaben jin ra’ayinsu kan gyare-gyaren da Imam Khomani (q) ya bukaci a gudanar da su wani lokaci kafin rasuwarsa a cikin watan khurdod 1368H.SH. Gyare-gyaren sun hada da, shafe sharadin marja’iyya a cikin wanda zai maye gurbin Jagora, shafe kujerar Priminister don bawa shugaban kasa damar aiki, da kum kaucewa dardewar ayyukan gwamnati. Har’ila yau tare da shafe majalisar koli ta gudanar da harkokin shari’a, da maye gurbinsa da alkalin alkalai wanda zai jagoranci ma’aikatar ta shari’a. Mutanen sun amince da wadan nan sauye sauye, sannan sun zabi Aya. Hashin Rafsanjani a matsayin shugaban kasa a zaben. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 286 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Yuli-1729M. Bakaken fatar arewacin Amurka sun fara wata gwagwarmaya ta samun encin kai a yankin. Da farko dai wasu bakaken fata 44 wadanda suka taso daga yankin Carolina suka nufi  Florida, inda a lokacin ake kashe duk bakar fatan aka gani a garin. A wannan karin ma kafin wadan nan bakaken fata 44 su isa Frolida wasu turawan ingila sun kamasu sunkashe.  Amma kisan nasu ya jawo bori mai yawa na bakaken fata a duk fadin yankin. Bakaken fatar Amurka dai, an kawosu Amurka ne imma a matsayin bayi don sada su ko kuma wadanda aka sace da karfin tsiya don tilas ta masu bauta a karkashin turawa yan mulkin mallaka. *******************************************. Yau Laraba 07-Murdod-1394H.SH=12-Shawwal-1436H.K.=29-Yuli-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 406 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Shawwal-1030H.K. Baha’udden Mohammad bin Hasain Amuli, babban malamin addini a kasar Lebanon ya rasu. Anawa malamin lakabi da Sheik Bahaee, an haife shi a garin Ba’alabak na kasar Lebanon, kuma kasancewa mahaifinsa babban malamin addini ne a lokacin, Sheikh Baha’uddeen ya zama babban malami a cikin dan karamin lokaci. Ya kuma rubuta littafai wadanda malaman tarihi suka ce ya kai mujalladi 100. Daga cikinsu akwai  جامع عباسی », « کشکول » ، « حبل المتین » ، « تشریح الافلاک » و « خلاصه الحساب . **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 58 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Yuli-1957M. Majalisar dinkin duniya ta kafa hukumar IAEA wacce take sanya ido kan yadda kasashen duniya masu fasahar nukliya suke amfanin da makamacin don kaucewa amfani da shi wajen kera makaman kare dangi, ko Nuklia Bom. Har’ila yau hukumar tana da cibiyar bincike babba a babban ciyarta da ke birnin Geneva, inda take bincike ta kuma bawa kasashe membobi a cikinta fasahar masu amfani da ta gano.. Sai dai hukumar ta IAEA ta fitar da kasashe 5 wadanda suka mallaki makaman nuklia wato Amurka, China, Rasha, Britania, da kuma Faransa a cikin jerin kasashen da za’a yiwa bincike. Banda haka tana nuna bambanci a cikin aikinta, inda take takurawa kasashen da basa dasawa da manya manyan kasashen da bincike, sannan takan kyale kasashen da suka mallaki makaman Nuklia kamar HKI don kusancinta da manya manyan kasashen  duniya. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Murdod-1360H.SH. Abul-Hassan Bani Sadr tubebben shugaban kasar Iran, da kuma shugaban kungiyar Munafukai kuma yan ta’adda ta MKO Mas’ud Rajavi sun fice arce daga kasar Iran. Kafin haka da kwanaki 37 majalisar shoora Islamiyya ta tube Bani Sadr don munafurcin da ya bayyana a gare shi, na yin karan tsaye ga tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kin yakar sojojin Sadam Husai shugaban kasar Iraqi na lokaci da kuma dai tada rikicin a cikin kasar. Amma bayan da mutanen kasar Iran suka zabi Dr Ali Rajai a matsayin sabon shugaban kasa, munafukan sun tabbatar duk abinda zasu baza su taba komawa kan iko a kasar Iran ba sai suka badda kama da sanya kayan mata suka bar kasar zuwa faransa inda suke ci gaba da kullawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran sharri. Rajawi ya zama shugaban kungiyar Munafukai masu yakar Iran daga kasar Iraqi na wasu shekara , amma bayan kauda sadam Husain daga shugabancin kasar Iraqi kungiyar ta MKO ta tarwatse.   ======================== Yau Alhamis 08-Murdod-1394H.SH=13-Shawwal-1436H.K.=29-Yuli-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 525 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Shawwal-911H.K. Aka haifi sheikh Zainuddeen bin Ali Shami a kasar Lebanon. Sheikh Shami wanda aka fi saninsa da shaheed thani ya tashi a gaban mahaifinsa wanda ya kasance mashahurin malami a kasar Sham a lokacin. Bayan karatunsa na sharar fage ya zagaya zuwa wasu kasashen musulmi don fadada karatunsa. Daga karshen sheikh zainuddeen ya kai ga martaban mujtahidi marja’ia a gaban malamansa a garin Ba’alabaq na kasar ta Lebanon. Banda tarbiyantar da dalibai Sheikh shami ya rubuta littafai da dama mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne sharhin Lum’atu addamashqiyya. Sheikh zainudden Ali Shami ya yi shahada a hannun sarakunan lukacin a lokacinda aka tuhumeshi da zama mabiyin mazhabar ahlulbaiti (a) a shekara ta 966 H.K. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 56 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Shawwal-1380H.K. Malamin addini Marja’ee Aya. Sayyeed Husain Tabatabai Burujardee ya rasu a nan Iran. An haife shi a shekara ta 1292 H.SH a garin Burujad a nan Iran. Ya fara karatu a mahaifarsa, sannan yana dan shekara 28 a duniya ya jie birnin Najafa na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa na tsawon shekaru 8 a gaban manya manyan malamai na zamanin wadanda suka hada da Mullah Kazim Khurasani, Sheikh Shari’atu Esfahani, Sayyeed Mohammad Kazeem Yazdee. Bayan kamala karatunsa ya dawo gida Burujadd amma a shekara ta 1363 H.K. mutanen Qum suka bukace shi da ya dawo garin don raya haramin ma’asuma (a) da ilmin iyayenta. Anan ya ci gaba da tarbiyantar da dalibai har zuwa rasuwarsa. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 98 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Shawwal-1338H.K. Mirza Mohammad Taqi Shirazi ya bada fatawar wajibcin yakar turawan Ingila wadanda suke nufin mamayar kasar Iraqi a lokacin, inda ya zama jagoran borin da aka fi saninsa da borin 20-Octoba-1920M. Bayan yakin duniya na daya wanda turawa suka yi amfani da shi wajen karya daular Umania, bayan yakin sun yi watandar kasashen musulmi a tsakaninsu inda kasar Iraqi ta fada cikin rabon kasar Britania. Da wannan dalilin ne turawan Ingila suka nufi kasar Iraqi don mamayarta. Borin mutanen kasar Iraqi dai bai kai ga nasara ba, amma kuma turawan basu ji dadinta ba. ====================================. Yau Jumma’a 09-Murdod-1394H.SH=14-Shawwal-1436H.K.=31-Yuli-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 43 da suka gabata a rana irin ta yau wato 31-Yuli-1960M. Elaija Muhammad shugaban kungiyar bakakin fata musulmi a Amurka ya bukaci gwamnatin kasar ta kafa yanki na musamman don tsugunar da fakaken fatar kasar karkashin ikinta. Elaija Muhammad ya bayyana wannan bukatar ne a dai dai lokacinda bakaken fatar Amurka suke matukar shan wahala a hannun fararen fata yan wariyar launin fata. Gwamnanin Amurka dai ta lokacin bata amsa kiran Elaija Muhammad ba. Amma shi ne ya kafa kungiyar musulmi kuma bakaken fata mafi girma a Amurlka wacce ake kira “Alumma Musulmi” the nation of islam. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato .09-Murdod-1359H.SH , gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana sabon tutar kasar wacce ta tafi dai dai da manufofin gwamnatin kasar kamar yadda Imam Khomaini (q) wanda ya assasa gwamnatin ya bukata. Sabon tutan dai yana dauke da launuka ukku, Kore a sama wacce take nuna ci gaba da bunkasa ayyukan noma, sai Fari a tsakiya wacce take nuna zaman lafiya na musulman kasar Iran, sai kuma ja wacce take nuna jinin shahidai wadanda suke kare kasar daga makiya. Sai kuma a tsakiyarsu aka rubuwa All.., amma wanda ya yi kekkyawar kula zai lura cewa kalmar tana kunce da La’ila ha Illallah. Sai kuma taurari gudu 22 wadanda suke nuna ranar da aka sami nasara juyin juya halin Musulunci a ranar 22-11-57. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Murdod-1366H.SH. Mahukunta wahhabiyawa na kasar saudia sun yi dirar mikiya kan mahajjata Iraniyawa masu gudanar da bangare mai muhimmanci na aiki hajji wato bara’a ga mushirikai a birnin Makka, inda suka kashe mahajjata kimani 400. Farilla ta bara’a ga mushrikai dai ya zo cikin ailkur’ani da hadisan manzon Al..(s) kuma abinda mahajjatan suke fada a wannan bara’ar ita ce, kira ga hadin kan musulmi, la’anta ga Isra’ila da kua Amurka. Sai dai abinda ya fara a birnin Makka a lokacin ayyukan hajji a wancan shekara ya tabbatar da cewa mahukuntan kasar saudia masu ikidar wahhabiyawa masu cancanci kula da wurare masu tsarki na msulmi ba, banda haka sun tabbatar da tasirin da yahudawa da wadanda ba musulmi ba suke da shi a kansu. +++++++++++++++++++++++++++++++++. Yau Asabar 10-Murdod-1394H.SH=15-Shawwal-1436H.K.=01-Augusta-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 57 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Augusta-1958M. Aka wargaje tarayyar kasashen larabawa wacce ta dunkule kasashen Iraqi da Jordan zuwa kasa guda. Shugaban kasar Masar Jamal Abadunnasir ne ya fara hada kasashen Masar, Syria da kuma Yemen daga baya zuwa dunkulellen kasa ta hadadiyar daular Larabawa. Sai kuma daga baya kasashen Jordan da kuma Iraqi wadanda dangin hashimawa yaya sharifu makka ne suke mulkin su suka dunkule suka zama tarayyar hashimawa ko kuma tarayyar larabawa a ranar 11-Febrerun-1958M. Wadan nan kasashen suna kokarin hada kansu  ne don fuskantar HKI wacce turawa yan mulkin mallaka suka dasa a kasar  palasdinu kuma take mamaye kasashen na larabawa daya bayan daya. Amma bayan watannin 6 da hadewar kasashen Iraqi da Jordan turawan Ingila sun ingiza wasu sojojin kasar Iraqi karkashin jagorancin Abdulkarin Kasin da Abdussalam Arif suka yiwa sarakunan Iraqi juyin mulki suka kashe su a ranar 14-yulin-1958M, sannan suka kawo karshen hadewar Iraqi da Jordan a ranar 01-Augustan-1958M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 40 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Augusta-1975M. Shuwagabannin kasashen Amurka da Canada da kuma sauran kasashen turai amma banda Jamus sun fara wani taro a kasar Findland don neman kusanci tsakanin kasashen yamma karkashin jagorancinAmurka da kuma kasashen gabas karkashin jagorancin tarayyar Soviet. Sai dai bayan mamayar da Soviet ta yiwa kasar Afganistan a shekara 1979M, da kuma waragewar tarayyar ta Soviet a 1991 wanda ya sa yerjejeniyar Findlanda ta tashi daga aiki don sauran kasashen turai wadanda suka balle daga tarayyar Soviet sun hadewa tarayyar Turai. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 10 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Augusta-2005M. Sarki Fahad bin Abdulaziz sarkin kasar saudia ya rasu. An haife shi a shekara 1921 a birnin Riyad. A shekara ta 1967 ya zama mataimakin Priministan kasar sai kuma bayan shekaru 8 ya zama yerima mai jiran gadon sarautar kasar. Sai kuma a shekara ta 1982 ya zama sarkin saudia bayan mutuwar danuwansa sarki Khalid Dan Abdulaziz. A lokacin mulkinsa ya kara dankon zumunci da Amurka, sannan ya tallafwa Sadam Husain na kasar Iraqi a yakin da ya dorawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A shekara ta 1995 ya mayarwa danuwansa Abdullahi ayyukan mulkin don rashin lafiya sannan yam utu a shekara ta 2005. ============================================. Yau Lahadi 11-Murdod-1394H.SH=16-Shawwal-1436H.K.=02-August-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 93 da suka gabata a rana irin ta yau wato Alexander Graham Bell masanin da ya kirkiro water taro a rasu. An haifi Graham Bell a kasar Scocland a shekara ta 1847M, bayan ya kamu da cutar Tv sun kaura da shi da iyayensa zuwa kasar Canada daga nan suka wuce Amurka. A can Amurka ne Graham Bell ya hadu da wani abokin aikinsa Tomas Watson,  wanda tare da yi bincike mai tsanani har suka sami nasara kirkiro wayar tarho mai amfani da waya a shelara 1876M. duk da cewa har yanzun ana amfani da wayar tarho mai amfani da waya , amma daba baya wasu masanan sun kirkokro wayoyin da basa amfani da waya wanda yake ko ina a duniya a halinn yanzu. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Augusta-1945M. Aka kammala taron Postdam na kasar Jamus. Manufar taron wanda aka fara tun 18-yulin-1945M har zuwa 02-Augusta –wancan shekarar shi tattauna yerjejeniyar da kasashen Kawance a yakin duniya na biyu, wato Tarayyar Soviet, Amurka da kuma Ingila kan makomar kasar Jamus da kuma yadda zasu bullowa kasar Japan. Shuwagabannin kasashen Amurka True man, Tarayyar Sovier Staline da kuma na kasar Britanian Chechil sun halacci taron sannan a nan shugaban Amurka ya shaidawa Soviet cewa ya sami makaman nuclia kuma zai yi amfani da shi kan kasar Japan. Bayan taron ne shugaban Amurka Truman ya bada umurnin amfani da makaman nuklia kan kasar Japan a ranakun 6-9 na watan Augustan wancan shekara, wanda bayan amfani da dubban daruruwan mutanen Japan suka halaka, kuma a dole Japan ta mika kai aka kawo karshen yakin duniya na biyu. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Murdod-1367H.SH. Wata tawagar bincike ta Majalisar dinkin duniya wacce ta gudanar da bincike a kasashen Iran da Iraqi, ta fidda rahoton cewa sojojin shugaban kasar Iraqi Sadan Husain ya yi amfani da makaman guba kan mutanen Iran fararen hula a cikin yakin shekaru 8 wanda kasashen biyu suka yi. Wannan shi ne karon farko wanda Majalisar ta bayyana haka. Amma a lokacinda Sojojin Sadam suke kai wadan nan hare hare kan mutanen Iran, majalosar ta kasa yin hakan don manya manyan kasashen duniya suna da hannu wajen tallafawa Sadam Husain wajen kera wannan makaman. Sai dai wani abin lura shi ne, duk tare da wannan rahoton majalisar bata fitar da wani kuduri na yin Al..wadai da wannan aikin da Sadam Husain ballanta na ayi maganan biyan diyya da sauransu. ++++++++++++++++++++++++++++++++++++++. Yau Litinin 12-Murdod-1394H.SH=17-Shawwal-1436H.K.=03-August-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 1431 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Shawwal-05H.K. Aka yi yakin gwalolo, ko kuma Khadaq tsakanin Musulmi karkashin jagorancin Manzon Al..(s) da kuma rundunar Mushrikai a wajen birnin Madina. Bayan da manzon Al..(s) ya sami labarin gabatuwar rundunar, ya shawarshi sahabbansa, inda ya amince da shawarar Salman Farisi nah aka rami a mashigar Madina. A cikin dan karamin lokaci suka yi wannan aikin, wanda ya sa mushrikai wadanda adadinsu ya kasi mayaka dubu 10, karkashin Jagorancin Abu Sufyan suka yi mamakin hakan, a dole suke tsaya bayan ramin. Sai dai bayan yan kwanaki wasu jarumai daga cikinsu sun sami damar tsallaka remain, a nan ne Manzon All..(s) ya hadasu da Aliyu dan Abi Talib (a) wanda ya kashe babbansu wato Amr bin Abdovod. Da haka kuma suka tsorata suka tarwatse, Al..ya tabbatarwa manzon Al..(s) alkawarin nasarar da yayi masa. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 101 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Augustan-1914M. Aka bude mashigar ruwa ta Panama a tsakiyar Nahiyar Amurka, inda jirgin ruwa na farko ya tsallaka daga tekun Atlantika ya bulla cikin Tetun Pecific. Wasu injiniyoyin yan fasar Faransa ne suka soma aikin hakar mashigar ruwan, amma daga karshen masana Amurkawa ne suka kammala. Mashigar Ruwa ta Panama tana da tsawon kilomita 68 kuma samuwarta ya takaita ziraga zirgan jiragen ruwa daga gabacin Amurka zuwa yammacinta wand aba sai an zagaya ta kudancin nahiyar ko arewaci ba. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 55 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Augusta-1960M. Kasar Niger ta sami cikekken encinta daga hannun turawan faransa yan mulkin mallaka. Tun cikin karni 18 miladiyya ne turawan Faransa suka shigo kasar Niger da nufin mallakarta, amma hakan bai tabbata ba sai a shekarata 1922M a lokacinda ta kakkafa sansanonin sojojin ta a kasar. Kuma tun lokacinne mutanen kasar suka fara gwagwarmayan kwatar encinsu.Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara ta 1960 a lokacinda turawan suka bada enci. Kasar Niger tana da fadin kasa kilomiya murabba’I   1,267,000, kuma tana makobtaka da kasashen Nigeria, Libya, Borkina Faso Chadi, Mali da kuma Benin kasar ta dogara da arzikin man fetur da ma’adinai, da kuma tallafi daga kasashen waje. *********************************. Yau Talata 13-Murdod-1394H.SH=18-Shawwal-1436H.K.=04-August-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 838 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Shawwal-598H.K. Muhammad ibn Idris Hilly, babban malamin addinin Musulunci a zamaninsa ya rasu. An haifi ibn idris a garin hilla na kasar Iraqi a shekara ta 543H.K. Ibn idris ya fara karatunsa da alkur’ani mai girma da littafan sharar fage. Daga karshe ya shiga karatu a gaban manya manyan malamai na zamaninsa inda ya kai matsayinmujtahidi yana matashi. Ibn Idris yana da fahintar cewa mutum dole ne ya yi amfanin da baiwa ta kwakwalwa wanda All..(t) ya bashi don gano asiran halttar mutum da kuma abubuwan da ke gewaye da shi, wannan ya basa damar samun ci gaba mai yawa a cikin ilmin da ya samu. Sannan malaman da suka zu bayansa sun kara jaddada wannan fahintar. Ibn Idris ya rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai  «سرائر». **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 93 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Augusta-1922M. Sojojin kasar turkiya karkashin jagorancin Mustafa Kamal Ata Turk sun fara yaki da sojojin kasar Girka wadanda suke mamaye wanin bangare na kasar ta Turkiyya. Kafin haka dai , bayan faduwar daular Usmaniyya a karshen yakin duniya na daya da kuma watandar yankunan daular da turawan Ingila da farina suka yi, mutanen kasar Girka wadanda suka dade suna rigima da turkawan a lokacinda suke karshin daular Usmania, sun yi amfani da wannan damar inda suka mamaye wani yanki na kasar Turkiyya. Da haka ne sojojin Turkiyya suka fada masu suka kuma koresu daga kasar.  **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 85 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Murdod-1309H.SH. Aka haifi Aya. Sayyeed Ali Sistani marja’ee kuma shugaban mabiya mazhabar shia a kasar Iraqi , an haife shi a birnin Mashad na kasar Iran. Aya. Sistani ya fara karatun tun yana dan shekara biyar a duniya. Bayan kammala karatun sharar fage yana dan shekara 11 a duniya ya je birnin Qom inda ya ci gaba da karatu a gaban Aya. Burujadi. Sai kuma bayan shekaru 8 ya kama hanyar birnin najafa na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban Aya Khoee. Daga nan ya ci gaba da karantarwa da kuma tarbiyantar da dalibai. Aya. Sistani ya yi kokarin tabbatar da hadin kan mutanen kasar Iraqi shi’a da sunna musamman alokacinda Amurkawa suka mamaye kasar a shekara ta 2003. Banda haka yana da mabiya a duk fadin duniya da kuma cibiyoyin yada ilmi  masu yawa a wurare daban daban a ciki da wajen kasar Iraq. ===================== Yau Laraba 14-Murdod-1394H.SH=19-Shawwal-1436H.K.=05-August-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 120 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Augustan-1895M. Wani inginia dan kasar Jamus mai suna Rodoalf Desel ya sami nasarar kera ingi mai amfani da man desel. Kafin haka dai Desel ya gano cewa makamashin gawayi coal da na man fetur wanda ake Konawa a jiragen ruwa da manya manyan ingina suna sarayar da kashi 90 % na zafi ko karfin da suke samarwa. Don haka ya fara tunanin yadda zai samar da wata inji ko na’urwa wacce zata yi amfani da karfin da wadan nan makamashi suke samarwa. Anan ne bayan wani kokari ya samar da cilenda wacce za’a takura iska a cikinsa sannan a samar da zafi mai yawan centigrade 500. Hakan zai sa mafi yawan makamashin da ya shiga cilintar zai kone a kuma yi amfani da shi wajen motsa abin hawar. Ya yi muwafakar samar da wannan injin ne wanda ake kira innjin desel a rana irin ta yau a shekara ta 1895M.  **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 109 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Murdod-1285H.SH. sarki Muzaffardeen kajaar ya amince da kundin tsarin mashrudiyyat a kasar Iran, bayan tashe tashen hankula wanda malaman addini suka jagoranta a kasar. Manufar samar da kundin tsarin mashrudiyya shi ne rage zaluncin da sarakunan da kuma makusantansu sukewa talakawa. Kafin a kai ga nasara da Sarki Muzaffar deen ya bada umurni ga jami’an tsaronsa na su murkushe borin da mutanen kasar suke yi. Hakan ya kai ga shahadar mutane da dama. Malaman da suka jagoranci borin dai sun hada da Aya. Sayyeed Muhammad Tabatabai da kuma Aya. Sayyed Abdullahi Bebahani. Bayan amincewar sarkin dai an gudanar da zaben yan majalisa sannan yan majalisar suka rubuta kundin tsari wa gwamnatin kajarawa, wanda kuma ya sami amincewar sarkin. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 52 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Augusta-1963M. Kasashen Amurka, Tarayyar Soviet da kuma Britania sun rattaba hannu kan wata yerjejeniya ta hana gwaji ko kuma jarraba makaman Nuklia. Kafin haka dai kasashen da suka mallaki makaman nuklia a duniya suna da gwada makaman, suna kuma kera makaman linzami wadanda suke iya keta nahiyoyi a duniya. Wannan halin ya sanya duniya cikin barazanan yaki nuklia. Wannan halin ya sanya wadan nan kasashe wadanda sune a gaba wagen mallakar irin wadan nan makamai suka amince da dakatar da gwaje-gwajen makaman a shekara ta 1963M.. Sai dai duk tare da wanan yerjejeniyar wadan nan kasashe da ma wasu kasashen duniya da suke kokarin mallakar wadan nan makamai sun ci gaba da gwaje gwaje gwajen.  ******************************. Yau Alhamis 15-Murdod-1394H.SH=20-Shawwal-1436H.K.=06-August-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 38 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Murdod-1356H.SH. Priministan kasar Iran na kasar a zamanin tagudu wato sha mohammad Riza ya sauka daga kujerarsa. Kafin haka dai Hassan Ali Mansur ne Priministan kasar Iran a lokacinda sarkin ya kori Imam Khomani (q) daga kasar Iran, daga baya magoya bayan Imam Sun halaka Hassan Ali Mansur, sai kuma sarkin ya sanya Amir Abbas Huwaida wanda ya ci gaba da aikin murkushe magoya bayan Imam da kuma aiwatar da manufofin Amurka a kasar Iran na tsawon shekaru 13. Amma bayan da abubuwa suka rikicewar sarkin kafin ya bara kasar ya sauke Huwaida ya dora Shappor Baktiyar. Amma bayan yan watannin juyin juya halin Musulunci ya kai ga nasara Imam Ya dawo daga gudun hijira ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran an gurfanar da Huwaida a gaban kotu aka kuma yake masa hukuncin kisa aka kuma zartar da shi. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Khurdod-1366H.SH. Komandan sojojinn sama na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Air Vicemarshal Abbas Babayi ya yi shahada a wani firkin da ya kaiwa sojojin kasar Iraqi a cikin yakin shakaru 8 da kasar Iraqin ta dorawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. An haifi Babayi a shekara ta 1326 H.SH a garin Kazwin sannan bayan kammala mkaratun sakandari ya  shiga makaranar koyon aikin tukin jiragen yaki a nan Tehran. Bayan nasarar juyin juya halin musulmunci Babayi ya shiga khidiwa wa kasar tare da zuciya daya, sannan bayan fara yaki tsakanin Iran da iraki ya shiga cikin yakin da imani inda da shi da abokinsa suka yi ta kaiwa makiya farmaki . amma a rana irin ta yau bayan ya kammala aikin farmaki kan sojojin Iraqi da aka bashi yana dawowa aka harbi jirginsa ya fada ya yi shahada, **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Murdod-1367H.SH. Shugaban kasar Iraqi na lokacin Sadam Husain ya amince da shirin tsagaita bude wuta wanda kudurin MDD na 598 ya bukata. Kafin haka dai sojojin Iraqi karkashin shugaba Sadam Husain ne suka soma mamaye kasar Iran a shekara ta 1980 da nufin mamaye kasar da kuma kifar da jaririyar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Amma har zuwa shekaru 8 sadam Husain ya kasa cimma wannan manufar, banda ma haka sojojin kasar Iran bayan sun amce dukkanin yankunanta da ke hannun sojojin Iraqi sun shiga kasar ta Iraqi. Wannan ya sanya MDD yafidda kuduri na 598 na tsagaita bude wuta a rana irin ta yau ce sadan Husain ya amince da tsagaita bude  wutan ala tilas bayan ya kasa samun nasara a yankin. ============================================. Yau Jumma’a 16-Murdod-1394H.SH=21-Shawwal-1436H.K.=07-August-2015M. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 1344 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Shawwal-92H.K. Komandan sojojin Musulmi mai suna Tariq bin Ziyar ya jagoranci mayakansa zuwa fatahin kasar Andulos a a nahiyar Turai. Bin Ziyar ya yi amfani da jiragen ruwa dauke da mayakansa dubu 12 suka tsallaka tekun Medeteranian ta kasar Morocco zuwa Espania kusa da wani dutse da aka bawa suna Jabal Tariq. Da haka kuma Musulmi suka fara yada addinin Musulunci a nahiyar Turai, daular Musulunci ya bunkasa a wannan yakin na tsawon shekaru fiye da 800, inda a cikin karni na 9 sarakunan kasashen turai suka yi amfani da damar da suka samu ta raunin da musulmin suka fada ciki suka kawo karshen daular. Sanna suka kori alhirin musulmai daga kasar. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 55 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Augusta-1960M. Kasar Ivory Coast ta sami encin kanta daga hannun turawan faransa yan mulkin mallaka. Turawan Potigal ne suka fara mamayar kasar Ivory a cikin karnin 16 miladia, sai kuma a shekara ta 1891M turawan Faransa suka mamaye kasar ta Ivory Coast, amma a shekara ta 1960 turawan sun mikawa mutanen kasar Ivory Coast bayan gwagwarmayan da mutanen kasar suka yi ta fafatawa da su. Kasar Ivory Coast tana da fadin kasa kilomita murabba’a dubu 332,463. Kuma tana makobtaka da tekun Atlantika daga kudu, sai kuma kasar Mali daga arewa, har’ila yau tana makobtaka da kasashen Ghana, Liberia, Guinea da kuma Borkina Faso duk a yammacin Afrika. **Masu saurare ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Augusta-1982M. Kungiyar kwatar encin Palasdinawa PLo karkashin shugabancin Yasar Arafa ta rattaba hannun kan yerjejeniyar sulhu da HKI tare da sanya ido na gwamnatin Amurka. An kulla wannan yerjejenian ne a birnin Beyrut na kasar Lebanon bayan fafatawar da mayakan PLO da sojojin kasar suka yi da sojojin HKI na tsawon kwanaki 80. Yahudawan sun shiga kasar Lebanina a cikin watan yuni na wancan shekarar da nufin murkushe kungiyar PLO ko kuma kareta daga kasar. Yerjejeniyar dai ta bukaci PLO ta kwace mayakanta 12 zuwa wasu kasashen larawa 8. Sai dai duk da haka mayakan kungiyar Hizbullah yan asalin kasar ta Lebanin bayan fatatawa na tsawon shekaru 18 da sojojin HKI bayan ficewar PLO ta sami nasarar korar yahudawan daga kasar Lebanon a shekara ta 2000M. ***********************************. Yau Asabar 17-Murdod-1394H.SH=22-Shawwal-1436H.K.=08-August-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 2348 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Augustan-333 Kafin haihuwar annabi Isa (a). An kammala gida birnin Eskandaria wanda sarki Iskandar Maqdoni na daular Roma a lokacin ya bada umurnin ginawa a bakin tekun medetrnian a arewacin kasar masar. Birnin Iskandaria dai ya kasance cikin birane masu muhimmanci a kudancin tekun medeteranin. Manufar gina wannan birnin dai shi ne wanzar da sunan sarki Eskandar a dukkan kasashen da ya ke iko da su. An dau shekara  da fiye da 20 ana gina birnin sai sdai amma sarki elexanda bai ga karshen gina birnin ba har zuwa rasuwarsa a shekara ta 323 . Amma sarakunan Roma da suka zo daga baya sun dauki gawarsa zuwa birnin bayan am kammala gininsa. A halinn yanzu dai birnin Eskandia ya shara da ilmin da kuma yawan wuraren tariki a yankin. Kuma shi ne birni na biyu a girma a kasar Masar. **Masu sauraro ko kun san cew ashekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Augusta-1945M. Sojojin tarayyar Soviet sun awkawa kasar Japan da yaki a karshen yakin duniya na biyu. Kafin haka dai kasashen biyu sun rattaba hannu kan yerjejeniyar rashin yakar juna a tsakaninsu, amma bayanda Amurka ta jefa makaman nuklia kan kasar Japan, tarayyar Soviet ta yi amfani da wannan damar inda ta mamaye koria ta Arewa kafin japan ta mika kai ga kasashen kawance. Kuma tun lokacin ne kasar Koreia ta arewa ta zama kasar mai bin tafarkin gurguzu na kasar rasha. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Augusta-1990M. Shugaban kasar Iraqi ta bawa sojojinsa umurnin mamaye kasar Kuwait wacce take mokobtaka da kasarsa. Bayan yakin shekaru 8 tsakanin Iran da Iraqi, Sadam Husain ya bukaci kasashen larabawa da su yafe masa basussuka na dalar Amurka kimani billion 30 da suka bashi a lokacinda yake yakar Iran. Amma kasar Kuwaita taki amincewa, da wannan dalilin ne sadam ya tura sojojinsa suka mamaye kasar Kuwai ya kuma dauyketa a matsayin daya daga cikin jihohjin kasar Iraqi. Amma bayan cacan baki na watannin 6 wasu sojojin kasashen yamma sun fidda sojojinsa da karfin daga kasar Kuwait. =======================================. Yau Lahadi 18-Murdod-1394H.SH=23-Shawwal-1436H.K.=09-August-2015M. **Masu sauraro ko kun san yau ce 9-Augusta- ranar da majalisar dinkin duniya ta ware na tunawa da mutanen da, ko kuma mutam tun kafin wayewarsa da kuma samun ci gaba. Mutanen da dai suna mutanen da haryanzun basu sauya rayuwarsu irin ta wacce mutum ya fara da it aba, watu har yanzun sun ki karba ko kuma wayewa da ci gaban duniya bata kai masu ba. Manufar sanya rana ta 9-Augusta a matsayin ranar mutanen da shi tunawa da irin rayuwar da mutanen da suka yi da kuma wayar da kan wadanda suke kan irin wannan rayuwar don su rungumi ci gaban da dan adama ya samu a cikin wannan lokaci mai tsawo. Banda haka ana mutanen zamani suna iya amfani da irin rayuwar mutanen da don samar da karin ci gaba a  rayuwarmu ta yanzu. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 96 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Augusta-1919M. Sarakunan kasar Iran na lokacin sun rattaba hannu kan wata yerjejeniya da turawan ingila wacce a cikinta sarkin ya mikawa turawan ingila ragamar gudanar da harkokin tattalin arziki siyada da kuma tsaro na kasar Iran. Turawan ingila sun kulla wannan yerjejeniya ne jim kadan bayan nasarar da juyin juya halin gurguzu ta samu a kasar Rasha. Kafin haka dai kasar Rasha a lokacin tana mamaye da wasu yankunan kasar Iran, amma juyin juya halin gurguzu a kasar ya maida hankalinta cikin gida. Mutanen kasar Iran musamman malaman addini basu amince da wanna yerjejniyar ba kuma nan take suka fara yunkurin bayan bayanta. Bayan sun tilastawa sarkin yin watsi da yerjejeniyar, turawan sun shirya wani juyin mulki wanda ya kawo karshen sarautar kajarawa ya kuma dora Mohammad Riza Palawi kan sarautar kasar Iran, wanda kuma ya ci gaba da yi masu khidima na wani lokaci. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Augusta-1945M. Kwanaki ukku bayan harin makamin nulia na farko a kan birnin Heroshima na kasar Japan, shugaban kasar Amurka na lokacin Hari Truman ya bada umurnin sakin makaman nulkiya zagaye na biyu kan birbib Nagasaki, inda a cikin kebtawar ido makamin ya share birnin ya kuma halaka mutane akalla dubu 80, sannan yawan wadanda suka halaka sun yi ta karuwa don gubar uranium da ta shiga cikin jikin mutane. Manufar harin dais hi ne tilastawa Japan mika kai ga kasashen kawanci masu yakar Hilata da magoya bayansa. Duk da cewa kasar Japan da mika kai ga wadan nan kasashe amma kuma an bude wata kofa ta gasar kere makaman nuklia wanda ya jefe duniyan cikin zullumin fadawa cikin yakin nuklia. Kuma har yanzun wannan barazanar tana nan musamman a bangaren Amurka wacce take son cimma manufofinta a duniya ko ta kaka. ****************************. Yau Litinain 19-Murdod-1394H.SH=24-Shawwal-1436H.K.=10-August-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 223 da suka gabata a rana irin  ta yau wato 10-Augusta-1792M. Bayan nasar juyin juya halin kasar Faransa, da kadan wata majalisar korarru a kasar ta faransa ta tsige sarki Luwi 15 kan kujerar sarautar kasar ta kuma yake maka hukuncin kisa. Tun bayan nasarar juyin juya halin dai, sarki Luwi ya rasa da dama daga cikin ikon da yake da su a kasar, amma bayan wani kaye da sojojin faransa suka yi a yakin da suka shiga da wata kasa a waje, masu adawa da sarkin sun yi amfani da wannan damar inda suka yada farfagandar cewa sarkin ya na tare da makiyan kasar da haka kuma suka tada zangaza zanga wacce ta kaiga majalisu masu fada a ji a kasar suka tube shi a rana a irin ta yau. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru  196 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Augustan-1819M. Kasar Colombia ta sami encin kanta daga hannun turawan Espania yan mulkin mallaka, bayan shan kayen da su ka yi a hannun sojojin Saimon Boliva. Turawan Espania sun yi wa kasar Colombia mulkin mallaka na tsawon shekaru 300 kafin a sami nasara akansu. Kasar Colombia dai tana daga cikin kasashen da suka samar da kasar Colombia babba a shekara ta 1819 M kasashen sun hada da kasar Colombia, Venezuela, Ekwado da kuma Panama. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru  95 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Augustan-1920M. Aka rattaba hannu kan yerjejeniyar Sevres na kasar Faransa tsakanin turawan Ingila da Faransa da kuma daular Usmania. Yerjejeniyar sevres dai ta fayyace kan cewa, daular Usmaniya ta rasa kashi 80% na fadin kasarta, wato daga kilomita murabba’I miliyon 3 zuwa dubu 600 kacal. Yerjejeniyar ta halattawa kasashen Ingila da Faransa watandar kasashen musulmi, inda kasashen Iraqi, Jordan da falasdinu suka fada cikin rabon Ingila, sai kuma Syria da kuma Lebanon. Har’ila yau yerjejeniyar ta bukaci kasar Turkiya ta yanzu ta mika wasu yankunan kasar ga kasashen girka, Armenia da kuma Italia. Wannan kaskancin dai ya sanya mutanen wadan nan kasashen suka yi bori wa turawan. **************************. Yau Talata 20-Murdod-1394H.SH=25-Shawwal-1436H.K.=11-August-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1288 da suka gabata a rana irin  ta yau wato 25-Shawwal-148H.K. Imam Ja’afar Assadiq (q) limami na 6 daga cikin limamai masu tsarki wasiyyan manzon Al..(s) ya yi shahada. An haife shi a Madina a shekara ta 83H.K. Ya gaji mahaifinsa Imam Mohammad Baqir (a) a yana dan shekara 31 a duniya. Imam Sadiq(a) rayu tare da sarakunan bani umayya 5 da kuma Abbasiywa 2. Rigingimun da wadan nan sarakunan suka yi ta yi kan mulki ya sa suka rage sanya ido a kansa, wannan kuma ya bashi damar ilmantar da alummar kakansa da dama, a kuma fannonin ilmi da dama. Malaman tarihi sun ce daliban Imam sadiq(a) sun kai malamai 4000. Daga cikin dalibansa akwai Jabir bin hayyan wanda ya kirkiri ilmin kimiyyar sinadarai. Dag karshe sarki Mansur dawaniki daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya kosa da ganin irin ci gaban da Imam Yake yi ya bada umrnin aka kashe shi da guba a rana irin ta yau. A halin yanzu kabarinsa da makabartan Baqiyya dake Madina. Mutan mika ta’aziyyarmu ga musulmi musamman mabiya mazhabar ja’afariyya. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 486 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Augusta-1529M. Bayan gwagwarmaya na shekaru masu yawa daga karshen gwamnatocin kasashen turai a lokacin sun amince da samuwar Mazhabar Protestan ta kiristoci. Kafin haka dai mazhabar Catholic ace kadai karkashin jagorancin paparoma take iko da mutanen yankin. A cikin karni 16 miladiyya ne aka sami wani malamin addinin kirista mai suna Mathin Lutha wanda ya gabatar da wasu gyare gyare a kan yadda malaman catholica suke tafiyar da harkokin addinin a yankin. Inda da farko ya sabawa umurnin Paparoma na kada a tarjama linjila zuwa harshen harshen Jamusanci, amma ya tarjama shi ya kuma watsa shi cikin mutane. Banda haka Mathin Lutha ya bukaci kiristoci mabiyansa su yi biyayya ga ubangiji kadai. Kuma shi kadai zai gafarta masu zubansu. Wannan ra’ayin ya sa shi shiga wando daya da shuwagabannin lokacin wadanda suke iko da kasashen a lokacin . Sai daga karshe a dole sun amince da samuwar mazhabarsa ta Protestan wacce take nufin “bijirewa”. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 63 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Augusta-1952M. Sarkin kasar Ethiopia na lokacin Haile Selassie ya sanya hannu a kan wata kuduri na Majalisar dinkin duniya ta hade kasar Eretaria da kasar Ethiopia su zame kasa guda. Kasar Eretarai wacce mafi yawan mazaunata musulmi ne sun fada karkashin mamayar turawan Italia ne da farko, sannan a cikin yakin duniya na biyu turawan Ingila suka maye gurbin turawan Italia a mamayar kasar. Sai kuma a shekara ta 1950 majalisar dinkin duniya ta samar da wani kuduri wanda ya bukaci dunkulewar kasar Ethiopia da Eretarea kasa guda a cikin tsarin federaliyya. Amma mutanen kasar Eretaria wadanda basu amince da wannan dunkulewarba sun dauki makamai don samarwa kansu enci daga kasar Ethiopia a shekara 1960m. wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara 1993 a lokacinda aka gudanar da zaben jin ra’ayin mutanen kasar kan samun enci ko ci gaba da zama karkashin kasar Ethiopia inda suka zabi samun enci. ***************************************. Yau Laraba 21-Murdod-1394H.SH=26-Shawwal-1436H.K.=12-August-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 66 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Augusta-1949M. Aka gudanar da taron kasa da kasa kan yadda za’a kula da fursinoni da wadana suka ji rauni a yake yake a birnin Geneva cibiyar majalisar dinkin duniya a turai. An gudanar da taron Geneva ne jim kadan bayan yakin duniya na biyu, kuma taron ya tsaida wasu kudurori kan wadan nan batutuwa, wadanda suka hada da rashin kashewa ko cutarda fursinan yaki, kula da lafiyansu, basu damar sadarwa da danginsu, sanarda kungiyar agaji ta Red Cross sunayensu da sauri sannan bawa jami’an kungiyar damar ganinsu. Sai dai duk tare da wadan nan yerjejeniyoyi kasashen duniya da dama basa kiyayewa fursinoni da wadanda suka ji rauni hakokansu a lokacin yaki. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 46 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Augusta-1969M. Kasar Amurka da cilla tauraron dan adam na sadarwa na farko a duniya mai suna Eci-1 zuwa sararin samaniya, wanda kuma bayan daidaitawarsa a sararin samani ya aikawa shugaban kasar Amurka na lokacin sako na farko. Da wannan tauraron dan adama ne aka bude fagen samar da taurarin dan adam masu aiko da sauti hoto da kuma wakoki zuwa ko ina a duniya. Bayan Eco-2, hukumar NASA ta aike da Eco-2, sanna wasu taurain suka biyo bayan. A halin yanzu dai dubban taurarin yan adam ne masu ayyuka daban daban suke shawagi a sararin samaniya a nisa daban daban daga doron kasa. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 16 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Augusta-1999M. Majalisar dinkin duniya ta zabi ranar 12 ga watan Augusta na ko wace shekara a matsayin ranar matasa ta duniya. Manufar raya wannan ranar dai ita ce tunatarda gwamnatocin kasashen duniya kan muhimmancin matasa a ko wace kasa. Don sune zasu fayyace makomar ko wacce kasa. Don haka akwai bukatar gwamnatoci su bada  kula ta musamman ga matasa, kula wajen ilmantar da su, kare lafiyarsu ta jiki da ruhi, samar masu aiki da yi masu aure ko kuma samar masu damar haka. Kare su daga shan kwayoyi da shagaltuwa da wasannin da ba zasu amfanesu ba. Daga karshe karesu daga duk wata lalacewa. ===================== Yau Alhamis 22-Murdod-1394H.SH=27-Shawwal-1436H.K.=13-August-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 62 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Murdod-1332H.SH. Sarki sha Muhammad Riza pahalawi na kasar Iran ya tube Priministan kasar Dr Muhammad Musaddiq, yam aye gurbinsa da wani Komandan sojojin kasar wanda ake kira Zahidi. Sarkin ya dau wannan matakin ne tare da shawarar Amurka da kuma Britania, wadanda suka rasa amfanin da suke samu bayan da Dr Musadikkin ya maida kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar ya zama na gwamnati. Bayan wannan sauyin gwamnati sarkin ya arce zuwa arewacin kasar Iran don ya san abinda zai biyo bayan hakan. Don haka bayan da mutane sun tilasta masa dawo da Dr Musaddik kan kujerarsa sai ya kara gaba zuwa kasar Iraqi da can ya wuce Italia. Amma bayan watannin 2 ko kwanaki 60 Amurka da Britania sun jagoranci wani juyin mulki wanda ya kifar da gwamnatin dr Musaddiq a ranar  28-Murdod –shekarar. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 45 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Augustan-1961M. Bayan kasa fahintar juna tsakanin manya manyan kasashen duniya da suka mamaye kasar Jamus a karshen yakin duniya na biyu kan yadda zasu yi da birnin Balin, jamus ta gabas wacce take karkashin ikon tarayyar Soviet a lokacin ta fara gina Katanga wacce ta raba birnin biyu. Da farko dai an yi amfani da wayoyi masu kaya ne wajen raba birnin mai tsawon kilomita 45. Daga bata an maye shi da karfe. Wannan halin ya kai ga rana kasar Jamus biyu, kuma hakan ya ci gaba na tsawon shekaru 28. Inda a ranar 9-Nuwambar-1989M mutane suka tada wani bori wanda ya kai ga suka rusa bongon, sannan daga karshe a cikin watan Octoba na wancan shekara kasashen biyu da kuma birnin na Balin suka sake dunkulewa. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 40 da suka gabata  a rana irin ta yau wato 13-Auguistan-1975M. A wani juyin mulki wanda sojojin kasar Bangladesh suka aiwatar an kashe shugaban kasar kuma wanda ya jagoranci kasar zuwa samun encin kai daga kasar Pakistan Mujiburrahman. Bayan samun encin kai na kasar India daga turawan Britania daga kuma ballewar Pakistan daga kasar India a shekara ta 1947M, kasar Bangladesh ta zama bangare na kasar Pakistan ta gabas. Mujiburrahman ya zama dan majalisar Pakistan ta gabas a shekara ta 1954 sannan ya kafa jam’iyyar awami leaque a shekara ta 1962 don samarwa Bangladesh enci daga Pakistan. A ranar 26-Maris-1971 ya shelantar samun encin Bangladesh daga Pakistan wannan ya jawo yakin basasa a kasar, wanda ya kai ga kisan mutane kimani miliyon 3 dakuma korar wasu miliyon 10 daga kasar amma daga karshen yencin kasar ya tabbata. Daga nan Najib ya zama shugaban kasa amma bayan shekaru biyar al-amura sun sake rikicewa a kasar wanda ya kai ga juyin mulkin da ya rasa ransa a cikinsa yana dan shekara 55 a duniya. =============================================== Yau Jumma’a 23-Murdod-1394H.sH=28=Shawwal-1436H.K.=14-Augusta-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 68 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Augusta-1947M. Kasar Pakistan ta shelanta samun encinta daga kasar India. Kafin haka kasar India babba wacce ta hada da kasashen India, Pakistan da kuma Bangladesh suna karkashin renon turawan Ingila ne. Amma bayan da gwagwarmayan samun yenci daga hannun turawan yan kankama musulmin kasar India karkashin jagorancin Muhammad Ali Janah sun kama wata jam’iyya mai suna Musulim leaque a shekara ta 1906, tare da manufar kafa daular musulmi a wani yanki na kasar India. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara 1947 sanda turawan suka bada encin kai ga kasar ta India, daga nan ne a cikin watan Augustan shekarar kasar Pakistan babba wacce ta hada da kasar Pakistan da yanzu da kuma Bangladesh ta shelanta rabuwarta da kasar India da kuma kafa kasar Pakistan, sai dai daga baya a shekara ta 1971M Bangladesh ta balle daga Pakistan bayan rashin amincewa da juna da ta shiga tsakaninsu. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 44 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Murdod-1350H.K. Kasar Bahrain ta shelanta samun yencinta daga kasar Iran. Kafin haka dai tsibirin Bahrai bangare ne na kasar Iran tun kafin daular kajarawa. Bayan haka ne turawan ingila suka kulla wata yerjejeniya da sarakunan kajarawa ta mikawa turawan kula da tsibirin na Bahrai don basu damar tabbatar da tsaro a tekun farisa. Wannan halin ya ci gaba har fiye da shekaru 150. Daga karshe a shekara ta 1336 kasar Iran ta bayyana kasar Bahrain a matsayin jiha ta 14 daga cikin jihohinta, wannan ya sa kasashen larabawa suka nuna rashin amincewarsu. Daga karshen Majalisar dinkin duniya ta shiga tsakani inda aka gudanar da zaben raba gardama a kasar ta Bahrain mutanen kasar suka zabe bellewa daga kasar Iran a rana irin ta yau. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 9 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Augusta-2006M. Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbulla a kasar Lebanon bayan yakin kare kai daga hare haren HKI da nufin shafe kungiyar daga doron kasa na tsawon kwanaki 33, kungiyar ta amince da kudurin majalisar dinkin duniya mai lamba 1706 wanda ya bukaci tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu. A ranar 12-Yuli-2006 ne yahudawa suka farka dakarun hizbullah da yaki. Kafin tsagaita bude wuta dai dakarun huzbullah sun lalata jirgen ruwan yaki 2, masu saukar unguli 6, tankunan yaki masu yawa da kuma sojojin hki da dama. Hasarar da HKI ta yi wannan yakin ya lalata shirin Amurka na samar da sabuwar gabas ta tsakiya wacce babu hizbulla da kawayenta cikinta. ======================= Yau Asabar 24-Murdod-1394H.sH=29=Shawwal-1436H.K.=15-Augusta-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 101 da suka gabata a rana irin ta yau wato aka bude mashigar ruwa ta Panama a kasar Panama da ke tsakiyar nahiyar Amurka. Mashigar ruwa ta Panama ce ta hade tekun Atlantic daga gabas da kuma tekun Pecific daga yamma. Wani kamfanin kasar faransa ne ya fara aikin hakar mashigar a shekara ta 1881M, bayan shekaru 11 ya kasa kammalawa, sai Amurka ta karba ta kammala aka kuma bude ta a ranar 15-Augustan-1914M. Sai dai Amurka ta ci gaba da iko da mashigar har zuwa shekara ta 2000M. wato kimani tsawon karni guda sannan ta mayarwa kasar Panama ikonta.   **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 68 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Augusta-1947M. Turawan ingila sun mikawa kasar india encin kanta bayan mulkin mallaka na kimani shekaru 200. Tun shekara 1930 ne mutanen india suka fara gwagwarmayan neman encin kasarsu daga hannun turawan, amma turawan basu bada encin ba saida suka samarda sabani tsakanin musulmi da indiyawa wadanda suke rayuwa shakude da juna. Wannan sabanin ya kai ga lokacin bada encin kasar kasar India ta rubuwa zuwa Pakistan a kasar musulmi, sannan india kuma inda hundu suke iko, duk da cewa akwai miliyoyin musulmi a shakude da su. Mahadma gandi madugun gwagwarmayar samarwa kasar India enci shi ne ya kasance shugaban kasar na farko. Kasar india tana da fadin kasa kilimiya murabba’I miliyom 3 da dubu 287.   Kuma tana makobtaka da kasashen Pakistan Bagladesh, Miyanmar, Butan Nepal da kuma China. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Murdod-1369H.SH. Sadam Husain shugaban kasar Iraqi na lokacin ya aike da wasika zuwa ga shugaban kasar Iran na lokacin Aya. Hashimi Rafsanjani, inda a wasikar ya bayyana amincewarsa da yerjejeniyar Algies na kan iyakokin kasashen Iran da Iraqi wacce aka rattabawa hannun tsakanin kasashen biyu a shekara 1975M. Kafin wannan wasikar dai a ranar 27-Shariwar-1359H.SH. Sadam Husain ya yaga wannan yerjejeniyar a gaban yan jaridu na duniya, sannan bayan kwanaki ukku ya tura sojojinsa suka mafa mamayar kasar Iran, ya kuma bayyana cewa zai kawo karshen Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yan kwanaki. Hakan ya jawo yaki tsakanin kasashen biyu har na tsawon shekaru 8, inda MDD ta shiga tsakanin aka tsaida yakin. Kasashen yama da magoya bayansu daga cikin kasashen larabawa ne suka ingiza sadam Husain don kifar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan sun kasa yin haka da wasu hanyoyin. Wannan wasikar ta tabbatar da gaskiyar mutanen kasar Iran a yakin shekaru 8 da suka shiga da kasar Iraqi. ========================================= Yau Lahadi 25-Murdod-1394H.sH=01-Zulkada-1436H.K.=16-Augusta-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1263 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Zukada-173H.K. Aka haifi Sayyida Ma’asuma (s) diyar Imam Musa (a) jikan manzon Al..(s) a garin Madina. Fatima (s) ta na kan hanyarta daga Madina zuwa yankin khurasan a kasar Iran don haduwa da yayanta Imam Rida (a)  a shekara ta 201 H.K. sai rashin lafiya ya kamata a kusa da garin qum, bayan jinya na kwanaki 17 sai ta rasu . Fatima (s) ta shahara da ilmi da tsoron All.. har’ila yau tana daga cikin malaman da suke ruwaito hadisan manzon All..(s) daga iyayenta masu tsarki. A halin yanzu hubbarenta na birnin Qum a nan kasar Iran Iran masoya iyalan gidan manzon Al..(s) daga ko ina a fadin duniya suke ziyararta. Har’ila yau albarkacin samuwarta a nan qum garin ya zama cibiyar yada ilmin iyalan gidan manzon Al..(s) mafi girma a duniya. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 12 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Augusta-2003M. Kasar Libya ta dauki nauyin tarwatsa jirgin saman Fasinja mallakin kamfanin jiragen sama na Panam a kan kauyen Lokabi na yankin scotlanda. Jirgin dauke da fasinjoji 270 mafi yawansu Amurkawa ya tarwatse a sararin samaniyar kauyen lokabi a ranar 21-Decemba- 1988. Kasashen Amurka da Britania sun zargi gwamnatin kasar Libya da daukar nauyin tarwatsa jirgin, da haka kuma komitin tsaro na MDD ya kakabawa gwamnatin kasar Libya takunkumai don tilasta mata amincewa da laifin. Bayan shekaru 4 da kakaba mata takunkumin gwamnatin kasar Libya ta rubutawa komitan tsaro na MDD wasika inda ta tabbatar da zargin da ake mata, sannan ta amince da biyan diyyar mutane 270 da suka mutu sanadiyyar faduwar jirgin, diyyar da ya kai dalar Amurka billion 2.7. sannan zata mika mutane biyun da ake zargi da shigar da boma boman cikin jirgin. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 157 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Augustan-1858M. Sarauniyar Victoria ta kasar Ingila ta aike da sakon telegraph na farko daga birnin London zuwa ga shugaban kasar Amurka na lokacin a James Buchaman a birnin Washington Dc. Sarauniyar ta aike da sakon ne ta waya wanda aka shimfida daga cikin cikin tekun Atlantika har zuwa Newfoundland a gabacin kasar Canada, daga nan sai sake aika da sakon kan wayoyi har zuwa Amurka. Sakon sarauniyar na farko yana kunshe da kalmomi 99 mai haruffa 509, kuma an fara aikar sakon ne da misalin karfe 10.30 na safe, sannan ya kare da karfe 4.30 na safiyar washe gari, wato sakon ya dauki kimani sa’oee 18 kafin ya isa Newfoundland na kasar Canada. Wannan ya nuna cewa ko wani harafi yana daukar mintuna biyu kafin ya isa Canada. Shuwagabannin biyu sun yi ta musayar sakonnin telegraph a tsakaninsu har na tsawon kwanaki goma. Amma bayan watan guda wayar ta lalace. ===================================. Yau Litinin 26-Murdod-1394H.sH=02-Zulkada-1436H.K.=17-Augusta-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Augus-1945M. Mutanen kasar Indonasia sun fara gwagwarmayan kwatar encinsu daga hannun turawan Hlanda yan mulkin mallaka. Ahmad Sokarno shi ne madugun wannan gwagwarmayan har na tsawon shekaru 4. Bayan haka ne majalisar dinkin duniya ta shiga tsakani inda ya bukaci turawan su kafa gwamnati ta hadin guiwa tsakanin turawan da musulman kasar indonasia wacce za’a kira Tarayyar Indonasia da Holand”. Amma tara da hakan mutanen kasar sun wargaza gwamnatin hadin kan mutanen biyu sun kuma shelanta samuwar entacciyar kasar Indonasia a shekara 1956M. Bayan haka Ahmad sokarno ya zama shugaban entacciyar kasar Indonasia na farko. Indonasia dai tan da fadin kasa, mai tarin tsibiru wadanda suka kai kilomita mutabba’a miliyon daya da dubu 900. Ita ce kasa ta 4 wacce ta yawan mutane a duniya, sannan ita ce kasar musulmi mafi girma a fadi da yawan mutane. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Augusta-1988M. Shugaban kasar Pakistan Janar Diya’ul –Haq yam utu sanadiyyar faduwar jirgin saman da yake cikinsa wanda kuma yake kan hanyarsa daga Yankin Punjam zuwa Islama bad. Ziya’ul-Haq ya shiga soja tun yana matashi ya jagoranci juyin mulki wanda ya kifar da gwamnatin Priminista Zulfikar Ali Buto a ranar 5-Yuli-1977M. Sannan ya kashe shi a ranar 4-Afrilun-1979M. ya yi alkawarin maida tsarin democradiyya a kasar cikin dan karin lokaci ya kasa, sai da yi shekaru 11 ya na mulki . sai a rana irin ta yau yam utu a hatsarin jirgin samansa. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Murdod-1369M. Tawagar fursinonin yaki Iraniyawa ta farko daga kasar Iraqi sun dawo gida. Bayan amincewa da kudurin MDD mai lamba 598 wacce ta dakatar da yaki tsakanin kasashen biyu, shugaban kasar Iraqi sadam Husain ya sake amincewa  da yerjejeniyar Algies ta 1975M wacce ya kayyade kan iyakokin kasashen biyuu, sai kuma ya fara sakin fursinonin yaki, wadanda ya tsaresu a cikin mummunan hali na shekaru masu yawa. Musayar fursinonin yaki na daga cikin yerjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin kasashen biyu. Amma fursinonin kasasr Iraqi kimani dubu 7 wadanda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sallamesu sun ki komawa gida don irin kekyawar rikon da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi masu a lokacinda suke tsare da kuma yanayin da kasar Iraqi take a lokacin. Maimakon su koma gida sun nemi mafaka a hukumar Red cross ta duniya. ========================================= Yau Talata 27-Murdod-1394H.sH=03-Zulkada-1436H.K.=18-Augusta-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Murdod-1358H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bada umurnin a kawo karshen mamayar da wasu yan awaren kasar masu samun goyon bayan kasashen waje sukewa garin Powe daya daga cikin garuruwan kabilar Qurdawa a kasar. Kafin haka dai bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a nan iran da kimanin watannin 6 ne wasu yan aware masu samun goyon bayan kasashen waje, musamman a yankin kurdawa na kasar Iran suke son ballewa daga kasar, amma sojojin kasar da kuma mayakan sa kai suka fi karfinsu. To haka abin yake a garin Pawe, inda bayan wannan umurnin na Imam a cikin yan kwanaki aka kawo karshen amamayar. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Murdod-1360H.SH. Aya. Sheikh Ba’ha’uddeen Mahallati, daya daga cikin malamai masu gwagwarmaya da zaluncin sarakunan Iran da kuma goyon baya ga Imam Khomani(q), ya rasu. An haifi Aya. Mahallati a shekara ta 1275H.SH. Ya fara karatun sharar fage a gaban mahaifinsa da kuma sauran malamai a mahaifarsa jihar fars. Bayan kammalawa ya je birnin Najafa na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban maya manyan malamai na lokacin cikin shekaru 10. A nan ne ya sami darajar Mujtahidi ya kumakomo gida, inda ya fara karantarwa da rubuce rubuce. Aya. Mahallati na daga cikin malaman da suke goyon bayan yunkurin Imam Khomaini (q) na fada da zaluncin sarakunan Palawi. Bayan samun nasara juyin Musulunci ya ci gaba da karantarwa a yankinsu na Fars a tsakiyar kasar Iran. **Masu sauraro ko kun san cewa sheklaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Murdod-1367H.SH. Aka soma tsagaita bude wuta da kuma shirin sulhu tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Iraqi a yakin shekaru 8 da suka fafata. Kafin haka dai, bayan kasawar da kasashen yamma suka yi na durkusar da jaririyar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran iran, sun biyu ta sadam Husain na kasar Iraqi wanda ya tura sojojinsa suka mamaye kasar Iran don cimma burinsu ta haka. Sai dai jajircewar mutanen kasar Iran ya kai ga anan ma suka kasa samun nasara, sannan suka bukaci MDD ta samar da wannan qudurin na sulhuntawa da kawo karshen yakin. Duk da cewa kudurin bata ambaci wanda ya soma takalar yaki ba amma dai bangarorin biyu sun amince da shi. ===========================================. Yau Laraba 28-Murdod-1394H.sH=04-Zulkada-1436H.K.=19-Augusta-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 62 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Mudod-1332H.SH. Kasashen Amurka da Britania sun shiya kuma sun jagoranci wani juyin mulkin wanda sojojin kasar Iran suka yiwa Priministan kasar Dr Mohammad Musaddiq. Kafin haka dai sarkin kasar Muhammad Riza Pahlawi ya tube Dr Musaddiq kan kujerar Priminister amma mutane suka tilasta masa dawo da shi. Amma bayan kwanaki 60 sai aka yi wannan juyin mulkin wanda ya dora Kanar Zahidi kan kujerar Priminista sannan ya bawa Sarkin Sha dawowa kasar Iran bayan arcewarsa zuwa kasar Italia. Dr Musaddiq ya sami nasara kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar daga hannun turawa a lokacin mulkinsa. Amma tun bayan juyin mulkin Amurka ta ci gaba da jujjuya kasar Iran har zuwa lokacinda Imam Khomaini (q) ya jagorancin juyin juya halin da ya kawo karshen sarautar sarakuna a kasar a shekara 1979. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru da suka gabata a ran airin ta yau wato 28-Murdod-1357H.SH. Aka yi gobarar gidan sinima ta REX a birnin Abadan na kasar Iran. Wannan gobarar tana daga cikin jerin abubuwan da suka faru kwanaki kafin samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Jami’an yansandan ciki na sarki sha ne suka haddasa gobarar a cikin gidan cinema mai dauke da yan kallo 388, wadanda kuma duk suka kone kurmus a cikin gobarar, jami’an tsaron sun yi haka ne don su dorawa masu gwagwarmaya da sarautar kasar laifi, su kuma nisantasu daga mutane, amma hakan sai ya kara masu bakin jini a wajensu. Wanda ya kaiga a cikin yan kwanaki aka kawo karshen sarautar sarkin. Wato a ranar 22-Bahman na wancan shekarar. **Masu sauraro ko kunn san cewa shekaru 24 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Augustan-1991M. Wasu sojojin masu kishin tsarin gurguzu da kuma wanzuwar tarayyar Soviet sun aiwatar da wani juyin mulki a tarayyar ta Soviet. A lokacin juyin mulkin dai shugaban tarayyar na lokacin Michel Gorbacheve yana hutu a Black sea na kasar tarayyar, amma tare da taimakon Boris Yelson shugaban jumhuriyar Rasha a cikin tarayyar an kawo karshen juyin mulkin. Kafin haka dai tarayyar Soviet ta fara wasu sauye sauye na barin tsarin gurguzu wacce take iko da ita na kimani shekaru 70. Har’ila yau juyin mulkin ya fidda Boris Yeltson sannan ya gaggauta faduwar da wargajewar tarayyar a cikin watan Decemban shekarar. =========================================================. Yau Alhamis 29-Murdod-1394H.sH=05-Zulkada-1436H.K.=20-Augusta-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 772 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Zulkada-664H.K. Radiyyuddeen Aliyu bin Musa wanda aka fi saninsa da sayyeed bin Tawus, babba malamin addini ya rasu. An haifi Sayyeed a garin Hilla na kasar Iraqi, ya kuma ya karatu a gaban mahaifinsa da sauran malaman kasar Iraqi. Ibn tawus ya rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai al-malahem wal-fitan da kuma al-luhoof-. Sayyeed ya ki karban mukamai da aka bashi a daular abbasiyawa na lokacin. Kuma yana raye sanda mogolwa suka kifar da daular Abbasiyawan suka kuma mamaye birnin Bagdaza. Amma bayan mamayarta, shugaban mongolawan ya kira shi, ya kuma amintar da shi da mabiyansa suka koma garin hill aba wanda ya tabasu. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 101 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Augusta-1914M. Sojojin kasar Jamus sun mamaye birnin Brusses babban birnin kasar Beljika a farkon yakin duniya na daya. Kuma shine babban birnin wata kasar da jamus ta mamaye a yakin duniya a turai. Tun ranar 4-Augustan shekarar ne sojojin na jumus suka fara yakar sojojin Beljika da nufin mamayar kasar duk da cewa ta nuna cewa ita yar ba ruwanta ne a yakin. A kasar yakin dai kasashen Faransa da ingila sun sami nadir kan Jamus da kawayenta, sun kuma wargaza daular Usmaniyya. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 27 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Murdod-1367H.SH. Gwamnatin kasar Amurka ta amince da cewa ta yi kuskure wajen harban jirgin fasinja samfurin Boeng mallakin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dauke da fasinjoji 298 a kan tekun farisa a ranar 3-Jenerun-1988M. Jirgin fasinjar dai ya tashi ne daga birnin Bandar Abbas kan hanyarsa ta zuwa birnin Dubai a lokacinda wani jirgin yakin Amurka da ke cikin tekun farisa ya aunashi ya kuma cilla makaman linzami guda biyu ya kuma tarwatsa shi. Saidai bayan kawani arba’in da faruwan wannan ta’asar gwamnatin kasar Amurka ta bawa captin na girjin lambar girmamawa na jarunta. ====================================================. Yau Jumma’a 30-Murdod-1394H.sH=06-Zulkada-1436H.K.=21-Augusta-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 30-Murdod ranar da aka ware a nan Iran a matsayin ranar tunawa da babban malamin addini kuma marubucin littafin Biharul-anwar, wato Allamah Mohammad Bakir Majlisi. Mahaifinsa Mohammad Taqi Majlisi daliban Sheikhul-Bahaee ne. Majlisi ya fara karatu tun yana dan shekara 4 a duniya. Mafi muhimmanci a cikin littafan day a rubuta sun hada da Biharul anwar, wanda ya tattara hadisan manzon Al..(s) da kuma hadisan iyalansa masu tsarki. Allamah Majlisi ya rubuta littafin cikin mujalladai 110, kuma shi ne littafin da ya fi tara hadinsai na mazhabar ahlulbaiti (a). Banda wannan Allamah majalisi yana da wasu littafai wadanda suka hada da   حقُّ الیقین، عین الحیاة، , رسالةٌ فی الاوزان . **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 71 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Augusta-1944M. Kasashen da suka sami nasara a yakin duniya na biyu sun gudanar da taro a jihar Colombia na kasar Amurka don tattauna makomar duniya bayan yakin. Shuwagabannin kasashen Amurka, Trayyar soviet , Faransa da kuma Ingila na cikin wadanda suka halarci taron. Shuwagabannin sun tattauna batun samar da majalisar dinkin duniya wacce a fadarsu zata yi kokarin sulhunta kasashe kafin su fada cikin yaki. Sai dai kuma bayan amincewa da hakan wadan nan kasashe suka warewa kansu matsayi na musamman a majalisar wato hakkin Veto wanda ya maida su masu tafiyar da duniyar ta yadda suke so. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 56 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Augusta-1959M. Kasashen Ingila, Iran, Turkiyya , Pakistan da kuma Iraqi sun kafa wata kungiyar tsaro wacce suka sanya suna CENATO a kasar Turkiyya. Kungiyar kamar kungiyar NATO ce amma a kudancin Asia, kuma manufarta it ace kula da duk harkokin tarayyar Soviet a lokacin wadanda zasu zama hatsari ga kasashen yamma. Duk fa cewa Amurka bata cikin kungiyar amma tare da ita ake kulla kome a cikinta. Amma bayan ficewar kasar Iran daga cikinta bayan nasaran juyun juya halin musulunci a kasar a shekara 1979 kungiyar ta wargaje. ==================================================== Yau Asabar 31-Murdod-1394H.sH=07-Zulkada-1436H.K.=22-Augusta-2015M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 174 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Zulkida-1262H.K.Aya. Fadayee Ostonee daya daga cikin manya manyan malaman addini na lokacinsa ya rasu. Aya. Ostonee ya fara karatu tun yana karami, inda ya farad a haddan alqur’ani, daga nan ya fara karatun fiqihu da usul. Har’ila yau ya zagawa zuwa garuruwa da dama a nan iran don samun Karin karatu. Bayan kamala karatunsa Aya. Ostoni ya dawo gida inda ya ci gaba da karantarwa da kuma rubuce rubuce. Daga cikin rubuce rubucensa day a barmana akwai diwanin wakokinsa. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 155 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Augusta-1860M. Aka haifi Paul Gottlieb Nipkow, masani dan kasar Jamus wanda ya kirkoro na’urar transmitter ta watsa hoto da sautin television. Nipkow ya tashi a cikin talauci, amma duk da haka y adage sai da ya kamala karatunsa na jami’a. Bayan haka ya shiga gudanar da bincike a bangren Physics ko kimiyyar lissafi inda daga karshe ya yi muwafakar gano transmitter na television sai dai Trinsmitern day a kirkiro baya aika da hoto da kuma sauti fiye da na tsawon mita 30. Amma wasu masanan daga bayan sun inganta aikin nasa wanda ya kaiga taransamita tana iya aika da hotona da sauti zuwa dubbai ko miliyoyin kilomita a halin yanzu. Nipkow ya rasu a shekara 1940M. **Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 151 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Augudsta-1864M. Wasu kasashe turai, Asia da kuma nahiyar Amurka sun rattaba hannu kan wata yerjejeniya da ake kira yerjejeniyar Geneva. Manufar wannan yerjejeniyan it ace bada dama ga likitoci, malaman jinya da duk wadanda suke aiki tare das u isar da taimako ga mutanen da aka jikata ko aka yi wa rauni a ko wani irin yaki. Har’ila yau wadan nan mutane zasu zama yan ba ruwammu a yakin don haka suna da dama ita ko ina a duk inda ake yaki. Hakanan ba ya halatta ga wani bangare daga cikin bangarorin da suke yaki su cutar das u. Wani dan rajin kare hakkin bil’adama dan kasar Sweden mai suna Henry Dunon ne ya fara kawo wannan shawarar.
More in this category: « Teer -1394 Hijira Shamsiyya

Add comment


Security code
Refresh