Labarai http://hausa.irib.ir Tue, 22 Aug 2017 08:58:26 +0000 en-gb Amnesty Int. Ta Bukaci Sojoji Su Yi Bayani Kan Kisan Gilla A Zaria http://hausa.irib.ir/labarai/item/33471- http://hausa.irib.ir/labarai/item/33471- Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci sojojin Najeriya su yi bayani kan kisan gillar da aka yi a Zaria a kan mabiya mazhabar shi'a.

Babban daraktan kungiyar a reshenta da ke Najeriya Muhammad kawu Ibrahim ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa bayanan da gwamnatin Kaduna ta bayar kan cewa sojoji sun bizne mabiya mazhabar shi'a 347 a wani makeken kabari guda daya a lokaci guda, ya sanya dole ne sojoji su yi bayani kan wadanda suka aikata wannan ta'asa daga cikinsu.

Kungiyar ta ce abin da ya faru yana da matukar sosai rai, kuma tana ci gaba da harhada bayanai kan hakikanin abin da ya faru, wanda za ta fitar nan ba da jimawa ba.

Yanzu haka a nata bangaren kotun manyan laifuka ta duniya tana harhada bayanai kan abin da ya faru na kisan gilla kan mabiya mazhabar shi'a a Zaria, bayan da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama masu zaman kansu suka shigar da kara a kan gwamnatin Najeriya da rundunar sojin kasar kan wannan lamari, wanda shi ma bayan kammala bincike daga bangaren kotun manyan laifuka ta duniya kan lamarin, za ta sanar da mataki na gaba ta fuskar sharia'a.

]]>
Latest Wed, 13 Apr 2016 04:37:48 +0000
Ganawar Shugaba Buhari Na Najeriya Da XI Jinping Na China http://hausa.irib.ir/labarai/item/33470- http://hausa.irib.ir/labarai/item/33470- Shugabannin kasashen Najeriya da na China sun gana a jiya a birnin Beijin, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewa, kasashen biyu za su aiki a bangarori na ci gaba, inda ya ce China za ta taimaka ma Najeriya a bangarori na bunkasa harkokin tattalin arziki da inganta masana'antu da ayyukan hakar mai da hakar ma'adanai noma da saraunsu.

A nasa bangaren shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana cewa, tun bayan gudanar da zaman da aka yi tsakanin China da kasashen Afirka a karshen 2015 a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, an samu gagarumin ci gaba ta fuskar dangantaka tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu haka dai China ta ba wa Najeriya bashin kudade kimanin dala biliyan 6 domin inda ayyukan gine-gine da samar da kayayyakin more rayuwar jama'a, yayin da kuma wasu ke danganta tafiyar baki daya da cewa tana da alaka ne da neman wannan bashi, domin cike gibin da aka samu kasafin kudin Najeriya na 2016.

]]>
Latest Wed, 13 Apr 2016 04:06:45 +0000
Bin Kadun Cin Zarafin Musulmin Turai Ta Hanyar Doka http://hausa.irib.ir/labarai/item/33468- http://hausa.irib.ir/labarai/item/33468- Kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO za tagudanar da wani zama domin bin kadun cin zarafin musulmi da ake yi a cikin wasu kasashen turai ta hanyar doka.

Shugaban Kungiyar ta ISESCO Abdulaziz Al-tuwaijari ne ya bayyana hakan, inda ya ce kungiyar za ta gudanar da zaman domin bin kadun cin zarafin musulmi da ake yi a turai musamman ma tun bayan kai harin Brussels na Belgium.

Tun bayan kai wannan hari dai mabiya addinin muslnci suna fuskantar matsaloli da dama a cikin wasu kasashen yammacin turai, da hakan ya hada har da wasu birane na kasar ta Belgium, inda a cikin wannan makon ma an kai hari kan wata babbar makarantar musulmi a garin Malmo na kasar Sweden tare da kone ta.

Kugiyar ta ISESCO ta sha alwashin daukar matakai na sharia' domin kwato wa musulmin da ke rayuwa a kasashen turai hakkokinsu ta hanyar doka.

]]>
Turai Wed, 13 Apr 2016 03:23:36 +0000
Babban Mai Bayar Da Fatawa A Quds Ya Gargadi Yahudawan Isra'ila http://hausa.irib.ir/labarai/item/33467- http://hausa.irib.ir/labarai/item/33467- Babban mai bayar da fatawa a birnin Quds Sheikh Muhammad Hussain ya gargadi yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi da ke shirin mamaye masallacin Quds.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da shehin malamin ya fitar a jiya Talata, ya ja kunnen yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi da ke shirin shiga cikin masallacin Quds, domin gudanar da bukukuwansu na shekarar yahudawa a cikin masallacin mai alfarma.

Sheikh Muhammad Hussain ya ce yin hakan na nuna cewa akwai alamar yaki na addini ya barke a tsakanin musulmi da yahudawa a Palastinu, domin kuwa musulmin Palastinu ba za su taba amincewa da keta alfarmar masallacin Quds alkiblar musulmi ta farko ba,a daidai lokacin da dubban yahudawa ke shirin shiga cikinsa domin yin bukukuwa, wadanda suke samun kariya daga daruruwan jami'an tsaron Isra'ila.

Daga Karshe Sheikh Muhammad Hussain ya kirayi al'ummar musulmi da ta saufke nauyin da ya rataya a kanta ta hanyar taka birki ga yahudawan sahyuniya, dangane da keta alfarmar wurare masu alfarma na musulmi da suke yi a cikin yankunan palastinu baki daya, da hakan ya hada har da masallacin Quds.

]]>
Palastin Wed, 13 Apr 2016 03:10:01 +0000
Kasashen Kongo Da Burundi Sun Sanar Da Shirin Aiki Tare Don Fada Da 'Yan Tawaye http://hausa.irib.ir/labarai/item/33466- http://hausa.irib.ir/labarai/item/33466- Rahotanni daga kasar kasar Demokradiyyar Kongo sun bayyana cewa sojojin kasar tare da hadin gwiwan na kasar Burundi sun fara aiwatar da wani shiri na fada da 'yan tawayen kasar Burundin da suke kan iyakokin kasashen biyu.

Kafar watsa labaran African Times ta jiyo kwamandan sojin hare-haren da aka ba wa suna Sokola 2, Janar Bwange Safari yana fadin cewa tun a ranar Asabar din da ta gabata ce sojojin kasashen biyu suka fara kai 'yan hare-hare kan 'yan tawayen da suke yankunan da suke kan iyakan kasashen biyu.

Sojojin kasar Kongon dai sun ce manufar wadannan hare-hare dai ita ce fatattakan 'yan tawayen daga wadannan yankunan.

har ila yau Janar Safari ya ce a yayin wadannan hare-hare an kama 'yan tawayen su 40.

]]>
Latest Tue, 12 Apr 2016 18:21:29 +0000
Shugabar Kasar Brazil, Rouseff, Na Fuskantar Barazanar Tsigewa A Majalisar Kasar http://hausa.irib.ir/labarai/item/33465- http://hausa.irib.ir/labarai/item/33465- Rahotanni daga kasar Brazil suna nuni da cewa shugabar kasar Dilma Rouseff na fuskantar barazanar rasa kujerarta bayan da kwamitin musammman na majalisar dokokin kasar ya kada kuri'ar amincewa da batun tsige ta da 'yan adawa suka gabatar.

An cimma wannan matsaya ne bayan kuri'ar da aka kada a kwamitin musamman din kan batun tsige shugabar inda aka samu kuri'u 38 masu goyon baya a kan 27 da suka ki amincewa da hakan.

Rahotanni sun ce a halin yanzu dai za a sake gabatar da batun don samun cikakkiyar kuri'a a zauren majalisar dokokin inda matukar aka samu kashi biyu bisa uku to za a ci gaba da batun tsige shugabar.

'Yan adawan dai suna zargin shugaba Rouseff da yi wa tattalin arzikin kasar ta'annuti bugu da kari kuma kan zargin rashawa da cin hanci da ake zarginta da shi, zargin da shugabar ta musanta; tana mai bayyana hakan a matsayin kokarin yi mata juyin mulki.

A ranar Asabar mai zuwa ne ake sa ran za a kada cikakkiyar kuri'ar a majalisar mai mutane 513.

]]>
Amurka Tue, 12 Apr 2016 18:11:31 +0000
UNICEF: Ana Samun Karuwar Masu Kunar Bakin Wake Tsakanin Yara A Yammacin Afirka http://hausa.irib.ir/labarai/item/33464- http://hausa.irib.ir/labarai/item/33464- Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar (UNICEF) ya bayyana cewar amfani da kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake na ci gaba da karuwa Yammacin Afirka cikin shekara gudar da ta gabata.

A wani rahoto da cibiyar ta UNICEF ta fitar ta ce an yi amfani da yara 44 wajen kai hare-haren kunar bakin wake a yankin arewa maso gabashin Nijeriya da kuma kasashen da ke makwabtaka da Nijeriyan irin su Kamaru da Chadi a shekarar da ta gabata ta (2015) idan aka kwatanta da 'yan kunar bakin wake guda hudu a shekarar 2014.

Rahoton wanda aka fitar da shi don tunawa da zagayowar shekaru biyu da sace 'yan matan sakandaren nan na Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi na nuni da cewa a halin yanzu dai kashi biyar cikin dari na hare-haren kunar bakin waken da aka kai kasashen Nijeriya, Kamaru da Chadi an yi amfani ne da kananan yara.

Rahoton ya kara da cewa tsakanin watan Janairun shekara ta 2014 da Fabrairun 2016, an kai hare-haren kunar bakin wake 40 da ake samun ana amfani da kananan yara alal akalla sau guda ko ma sama da haka; wato rahoton ya ce an kai irin wadannan hare-hare guda 21 a kasar Kamaru, 17 a Nijeriya da kuma 2 a Chadi.

Kungiyar nan ta Boko Haram dai ita ce ake zargi da kai irin wadannan hare-hare na ta'addanci.

]]>
Afirka Tue, 12 Apr 2016 17:55:57 +0000
Jagora Ya Ja Kunnen Kasashen Turai Saboda Goyon Bayan Ta'addanci Da Wasunsu Suke Yi http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/33463- http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/33463- Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunnen wasu kasashen turai dangane da irin goyon bayan ayyukan ta'addanci da tsaurin ra'ayi da suke yi wanda ya ce a halin yanzu shika ta fara komawa kan mashekiya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da firayi ministan kasar Italiya Matteo Renzi wanda ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke nan birnin Tehran inda ya bayyana cewar: Wasu daga cikin kasashen Turai sun kasance suna goyon bayan kungiyoyi masu tsaurin ra'ayi da amfani da karfi wajen cimma manufofinsu, to amma a halin yanzu wadannan kungiyoyi na 'yan ta'adda sun fara kai hare-hare Turai din.

Ayatullah Khamenei ya bayyana taimakon kudade da kuma makamai da Amurka take ba wa kungiyoyin 'yan ta'adda a matsayin babbar abin da ke kafar ungulu ga kokarin da ake yi na kawar da ta'addanci a duniya inda ya ce: Akwai karfafan dalilai da suke tabbatar da irin taimakon da Amurka take ba wa kungiyar Da'esh (ISIS) da sauran kungiyoyin ta'addanci. Duk da cewa a halin yanzu ma sun kirkiro abin da suka kira hadin gwiwan fada ta da kungiyar Da'esh, to amma duk da haka wasu cibiyoyin Amurkan suna taimakon kungiyar ta Da'esh ta hanyoyi daban daban.

Jagoran ya bayyana cewar Iran da kasar Italiya za su iya hada kai wajen fada da ta'addanci.

A yau Talata ce firayi ministan kasar Italiyan Matteo Renzi ya kawo ziyarar aiki nan Iran don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma bin sahun yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma a kwanakin baya a lokacin da shugaba Ruhani ya kai ziyara kasar Italiya.

]]>
Top News Tue, 12 Apr 2016 17:35:44 +0000
Shugaba Ruhani: Akwai Bukatar Aiki Tare Wajen Fada Da Ta'addanci http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/33462- http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/33462- Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar ayyukan ta'addanci suna ci gaba da zama babbar barazana ga zaman lafiyar dukkanin kasashen duniya, don haka akwai bukatar aiki tare tsakanin kasashen duniya wajen fada da wannan annobar.

Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da firayi ministan kasar Italiya Matteo Renzi wanda yake ci gaba da ziyarar aiki a kasar Iran inda ya ce: Ya kamata masu goyon bayan kungiyoyin ta'addanci su san cewa wadannan kungiyoyi ne dai barazana da kuma cutarwa ne ga dukkanin bil'adama, yana mai cewa kashe duk wani mutum a ko ina yake kuwa babban bala'i ne.

Shugaban na Iran ya kara da cewa a halin yanzu dai akwai bukatar hadin kai tsakanin dukkanin al'ummomi wajen fada da ta'addanci da tsaurin ra'ayi na addini a duk fadin duniya, yana mai sake jaddada kudurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na hada kai da dukkanin kasashen duniya wajen cimma kudurin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi na kawo karshen amfani da karfi da tsaurin ra'ayi a duniya a 2013.

Shi dai wannan kudurin, shugaba Ruhanin ne ya gabatar da shi a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 2013 inda kuma aka amince da shi.

A yau Talata ce firayi ministan kasar Italiyan Matteo Renzi ya kawo ziyarar aiki nan Iran don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma bin sahun yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma a kwanakin baya a lokacin da shugaba Ruhani ya kai ziyara kasar Italiya

]]>
Top News Tue, 12 Apr 2016 17:23:27 +0000
Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadi Kan Bullar Masifar Cuta A Kasar Afrika Ta Tsakiya http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/33461- http://hausa.irib.ir/labarai/babban-labari/item/33461- Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan bullar cututtuka a tsakanin kananan yara a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sakamakon matsalar rashin abinci mai gina jiki da na harkar kiwon lafiya mai inganci a kasar.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya bayyana cewa; Matsalar rashin abinci mai gina jiki da bullar cututtuka da suka hada da cutar cizon soro wato maleriya, amai da gudawa, gurbatar yana yi da ke janyo rashin iska mai kyau da sauransu sun fi zama babbar barazana ga kananan yara a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a kan matsalar tashe-tashen hankulan da suke ci gaba da addabar kasar.

Har ila yau Dujarric ya kara yin gargadi kan bullar yawaitar mutuwar kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar a duniya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, yana mai jaddada bukatar Majalisar Dinkin Duniya na samun tallafin kudade dalar Amurka miliyan 531 domin tallafawa jama'ar da suke cikin halin kaka-ni ka yi a Jamhuriyar AFrika ta Tsakiya.

]]>
Top News Tue, 12 Apr 2016 10:04:04 +0000