An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 13 April 2016 04:37

Amnesty Int. Ta Bukaci Sojoji Su Yi Bayani Kan Kisan Gilla A Zaria

Amnesty Int. Ta Bukaci Sojoji Su Yi Bayani Kan Kisan Gilla A Zaria
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci sojojin Najeriya su yi bayani kan kisan gillar da aka yi a Zaria a kan mabiya mazhabar shi'a.

Babban daraktan kungiyar a reshenta da ke Najeriya Muhammad kawu Ibrahim ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa bayanan da gwamnatin Kaduna ta bayar kan cewa sojoji sun bizne mabiya mazhabar shi'a 347 a wani makeken kabari guda daya a lokaci guda, ya sanya dole ne sojoji su yi bayani kan wadanda suka aikata wannan ta'asa daga cikinsu.

Kungiyar ta ce abin da ya faru yana da matukar sosai rai, kuma tana ci gaba da harhada bayanai kan hakikanin abin da ya faru, wanda za ta fitar nan ba da jimawa ba.

Yanzu haka a nata bangaren kotun manyan laifuka ta duniya tana harhada bayanai kan abin da ya faru na kisan gilla kan mabiya mazhabar shi'a a Zaria, bayan da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama masu zaman kansu suka shigar da kara a kan gwamnatin Najeriya da rundunar sojin kasar kan wannan lamari, wanda shi ma bayan kammala bincike daga bangaren kotun manyan laifuka ta duniya kan lamarin, za ta sanar da mataki na gaba ta fuskar sharia'a.

Add comment


Security code
Refresh