An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 13 April 2016 03:23

Bin Kadun Cin Zarafin Musulmin Turai Ta Hanyar Doka

Bin Kadun Cin Zarafin Musulmin Turai Ta Hanyar Doka
Kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO za tagudanar da wani zama domin bin kadun cin zarafin musulmi da ake yi a cikin wasu kasashen turai ta hanyar doka.

Shugaban Kungiyar ta ISESCO Abdulaziz Al-tuwaijari ne ya bayyana hakan, inda ya ce kungiyar za ta gudanar da zaman domin bin kadun cin zarafin musulmi da ake yi a turai musamman ma tun bayan kai harin Brussels na Belgium.

Tun bayan kai wannan hari dai mabiya addinin muslnci suna fuskantar matsaloli da dama a cikin wasu kasashen yammacin turai, da hakan ya hada har da wasu birane na kasar ta Belgium, inda a cikin wannan makon ma an kai hari kan wata babbar makarantar musulmi a garin Malmo na kasar Sweden tare da kone ta.

Kugiyar ta ISESCO ta sha alwashin daukar matakai na sharia' domin kwato wa musulmin da ke rayuwa a kasashen turai hakkokinsu ta hanyar doka.

Add comment


Security code
Refresh