An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 13 April 2016 03:10

Babban Mai Bayar Da Fatawa A Quds Ya Gargadi Yahudawan Isra'ila

Babban Mai Bayar Da Fatawa A Quds Ya Gargadi Yahudawan Isra'ila
Babban mai bayar da fatawa a birnin Quds Sheikh Muhammad Hussain ya gargadi yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi da ke shirin mamaye masallacin Quds.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da shehin malamin ya fitar a jiya Talata, ya ja kunnen yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi da ke shirin shiga cikin masallacin Quds, domin gudanar da bukukuwansu na shekarar yahudawa a cikin masallacin mai alfarma.

Sheikh Muhammad Hussain ya ce yin hakan na nuna cewa akwai alamar yaki na addini ya barke a tsakanin musulmi da yahudawa a Palastinu, domin kuwa musulmin Palastinu ba za su taba amincewa da keta alfarmar masallacin Quds alkiblar musulmi ta farko ba,a daidai lokacin da dubban yahudawa ke shirin shiga cikinsa domin yin bukukuwa, wadanda suke samun kariya daga daruruwan jami'an tsaron Isra'ila.

Daga Karshe Sheikh Muhammad Hussain ya kirayi al'ummar musulmi da ta saufke nauyin da ya rataya a kanta ta hanyar taka birki ga yahudawan sahyuniya, dangane da keta alfarmar wurare masu alfarma na musulmi da suke yi a cikin yankunan palastinu baki daya, da hakan ya hada har da masallacin Quds.

Add comment


Security code
Refresh