An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 12 April 2016 18:21

Kasashen Kongo Da Burundi Sun Sanar Da Shirin Aiki Tare Don Fada Da 'Yan Tawaye

Kasashen Kongo Da Burundi Sun Sanar Da Shirin Aiki Tare Don Fada Da 'Yan Tawaye
Rahotanni daga kasar kasar Demokradiyyar Kongo sun bayyana cewa sojojin kasar tare da hadin gwiwan na kasar Burundi sun fara aiwatar da wani shiri na fada da 'yan tawayen kasar Burundin da suke kan iyakokin kasashen biyu.

Kafar watsa labaran African Times ta jiyo kwamandan sojin hare-haren da aka ba wa suna Sokola 2, Janar Bwange Safari yana fadin cewa tun a ranar Asabar din da ta gabata ce sojojin kasashen biyu suka fara kai 'yan hare-hare kan 'yan tawayen da suke yankunan da suke kan iyakan kasashen biyu.

Sojojin kasar Kongon dai sun ce manufar wadannan hare-hare dai ita ce fatattakan 'yan tawayen daga wadannan yankunan.

har ila yau Janar Safari ya ce a yayin wadannan hare-hare an kama 'yan tawayen su 40.

Add comment


Security code
Refresh