An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 12 April 2016 17:55

UNICEF: Ana Samun Karuwar Masu Kunar Bakin Wake Tsakanin Yara A Yammacin Afirka

UNICEF: Ana Samun Karuwar Masu Kunar Bakin Wake Tsakanin Yara A Yammacin Afirka
Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar (UNICEF) ya bayyana cewar amfani da kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake na ci gaba da karuwa Yammacin Afirka cikin shekara gudar da ta gabata.

A wani rahoto da cibiyar ta UNICEF ta fitar ta ce an yi amfani da yara 44 wajen kai hare-haren kunar bakin wake a yankin arewa maso gabashin Nijeriya da kuma kasashen da ke makwabtaka da Nijeriyan irin su Kamaru da Chadi a shekarar da ta gabata ta (2015) idan aka kwatanta da 'yan kunar bakin wake guda hudu a shekarar 2014.

Rahoton wanda aka fitar da shi don tunawa da zagayowar shekaru biyu da sace 'yan matan sakandaren nan na Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi na nuni da cewa a halin yanzu dai kashi biyar cikin dari na hare-haren kunar bakin waken da aka kai kasashen Nijeriya, Kamaru da Chadi an yi amfani ne da kananan yara.

Rahoton ya kara da cewa tsakanin watan Janairun shekara ta 2014 da Fabrairun 2016, an kai hare-haren kunar bakin wake 40 da ake samun ana amfani da kananan yara alal akalla sau guda ko ma sama da haka; wato rahoton ya ce an kai irin wadannan hare-hare guda 21 a kasar Kamaru, 17 a Nijeriya da kuma 2 a Chadi.

Kungiyar nan ta Boko Haram dai ita ce ake zargi da kai irin wadannan hare-hare na ta'addanci.

Add comment


Security code
Refresh