Print this page
Tuesday, 12 April 2016 09:14

Wakilin M.D.D. A Kasar Libiya Ya Ce Kuskure Ne Daukan Matakin Soji Kan Kasar Ta Libiya

Wakilin M.D.D. A Kasar Libiya Ya Ce Kuskure Ne Daukan Matakin Soji Kan Kasar Ta Libiya
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kasar Libiya ya bayyana cewa shirin kasashen yammacin Turai da Amurka na daukan matakin soji kan Libiya; wani babban kuskure ne da zai kara janyo tabarbarewan matakan tsaron kasar.

Martin Kobler wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya ya yi kakkausar suka kan duk wani shirin kasashen yammacin Turai da Amurka na sake daukan matakin soji kan kasar Libiya; Yana mai jaddada cewa kamata ya yi a samar da rundunar soji mai karfi ta kasa a Libiya da zata dauki alhakin gudanar da duk wani yaki da ta'addanci musamman yaki da 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish.

Kobler ya kara da cewa: Kasashen yammacin Turai da Amurka sun tafka mummunan kuskure dangane da matakin da suka dauka na kaddamar da yaki kan kasar Libiya a shekara ta 2011 saboda dole ne su yi tunanin abin da zai biyo bayan kaddamar da hare-haren kafin fara farma kasar.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Libiya ya jaddada cewa; Halin da ake ciki a yanzu haka a Libiya ya yi muni saboda ko alluran rigakafi ba a samun damar yi wa kananan yara kuma makarantu duk suna rufe.

Related items

Add comment


Security code
Refresh