An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 12 April 2016 05:43

An kafa sabuwar Gwamnati a Nijer

An kafa sabuwar Gwamnati a Nijer
Shugaban Kasar Nijer Ya gabatar da sabuwar Gwamnatinsa wacce ta kumshi ministoci 38

A jiya Litinin ne Gwamnatin ta Nijer kalkashin jagorancin Firaminsta Briji Rafini ta gabatar da sabin minstocinsa 38 daga cikin su a kwai Mata guda 7.

A ranar 20 ga watan Maris din da ya gabata ne aka sake zaben shugaba Muhamadou Issoufou a matsayin sabon shugaban kasar Nijer din a wa'adi na biyu inda zai ci gaba da Jagorantar kasar har tsahon shekaru biyar masu zuwa, wannan kuma na zuwa ne bayan da Gamayar Jam'iyun adawar kasar suka kauracewa zaben tare kuma da neman magoya bayan su, su kauracewa runfunan zaben.

'Yan adawar sun zarki Gwamnati da tabka magudi a zaben shugaban kasar zagaye na farko, inda suka gabatar da korafinsu a gaban kotun kundin tsarin kasar, ganin cewa kotun ba ta saurari korafe korafen 'yan adawar ba, hakan ya sanya suka kauracewa zaben a zagaye na biyu.

Jim kadan bayan da aka rantsar da shi, Shugaba Muhamadou Issoufou ya sake nada tsohon Firaministansa wato Briji Rafini a matsayin Firaminista na sabuwar Gwamnatin tasa.

Babban kalu balan dake gaban Sabuwar Gwamnatin Ta Nijer, Matsalar Tsaro, karamcin abinci musaman a yankin da ake fama da rikicin boko haram, samar da aiyukan yi ga duban matasan kasar da suke fama da rashin aiki, sai kuma rikici siyasa,inda 'yan adawar suka ce daga ranar 2 ga watan Avrilun da ya gabata, babu halarcecciyar Gwamnati a kasar.

Add comment


Security code
Refresh