An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 11 April 2016 17:11

Sojojin 'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Sun Dawo Juba

Sojojin 'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Sun Dawo Juba
Wasu daga cikin sojojin 'yan tawayen Sudan ta kudu sun shiga birnin Juba fadar mulkin kasar a yau, bisa yarjejeniyar sulhu da aka cimmawa a tsakaninsu da bangaren gwamnati.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, wasu sojojin da ke cikin rundunar 'yan wayen Sudan ta kudu su 1370 sun shiga Juba a yau, tare da sanya idon wakilai na majalisar dinkin duniya da kuma na kungiyar tarayyar turai gami da kungiyar tarayyar Afirka.

A ranar 18 ga wannan wata Afirilu ne madugun 'yan tawayen Dr. Riek Machar zai iso birnin na Juba, inda wadannan sojojin 'yan tawaye tare da na gwamnati za su ba shi kariya, inda za a sa hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa ta rikon kwarya, inda Salva Kiir zai rike shugabancin kasa, shi kuma Riek Machar a matsayin mataimakinsa na farko.

Add comment


Security code
Refresh