An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 11 April 2016 16:20

Ganawar Shugabannin Kasashen Iran Da Kazakhstan A Tehran

Ganawar Shugabannin Kasashen Iran Da Kazakhstan A Tehran
Shugaban kasar Kazakhstan Nur Sultan Nazarbayev ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a yau a birnin Tehran, domin bunkasa alaka da kasar Iran a dukkanin bangarori.

Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya gana da shugaban kasar ta Kazakhstan a yau a fadarsa da ke Tehran, inda aka sanya hannu a tsakanin kasashen biyu kan yarjeniyoyi da guda 66, da suka hada bunkasa harkokin tattalin arzki, cinikayya, al'adu, ilimin kimiyya da fasa, tsaro, yaki da ta'addanci da sauransu.

Haka nan kuma a yammacin yau shugaban kasar ta Kazakhstan tare da rakiyar shugaba Rauhani, ya ziyarci jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, inda jagoran ya tabbatar masa da cewa kasashen biyu suna da alaka ta tarihi, kuma za ta ci gaba da bunkasa domin amfanin al'ummomin kasashen biyu.

Add comment


Security code
Refresh