An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 11 April 2016 11:21

Yan Adawa Sun Goyi Bayan Kudurin Majalisar Dinkin Duniya Kan Kasar DR Congo

Yan Adawa Sun Goyi Bayan Kudurin Majalisar Dinkin Duniya Kan Kasar DR Congo
Yan adawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congon sun jaddada goyon bayansu ga kudurin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan kasarsu musamman kiran da ya yi kan gudanar da zaben shugaban kasa a kan lokaci.

Yan adawar a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun jaddada goyon bayansu ga kudurin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya na neman gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Dimokaradiyyar Congo cikin watan Nuwamban wannan shekara ta 2016 kamar yadda aka tsara ba tare da jinkiri ba.

Har ila yau 'yan adawan sun mai da martani kan furucin mahukuntan kasar ta Dimokaradiyyar Congo musamman furucin ministan harkokin wajen kasar Raymond Tshibanda da ministan sadarwar Jamhuriyar ta Dimokaradiyyar Congo Lambert Mende kan sukan da suka yi dangane da matsayin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya na neman gudanar da zaben shugaban kasa a lokacin da aka tsara wato watan Nuwamban wannan shekara da muke ciki.

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a ranar 30 ga watan Maris da ya gabata ya gudanar da zama na musamman kan batun kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo inda ya fitar da kuduri mai lamba 2277 kan kara wa'adin zaman dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar tare da yin kira ga mahukuntan kasar da Hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI kan gudanar da zaben shugaban kasa a kan lokaci wato a cikin watan Nuwamban wannan shekara.

Add comment


Security code
Refresh