An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 11 April 2016 06:21

India : Adadin Mutanen Da Suka Mutu Sakamakon Gobara Ya Kai 110

India : Adadin Mutanen Da Suka Mutu Sakamakon Gobara Ya Kai 110
Hukumomi a kasar India sun sanar cewa adadin mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon babbar gobara da ta tashi a wani gidan ibada na addinin India dake yankin Kollam na jihar Keralaya ya karu zuwa 110.

Gobara wace ta tashi a jiya Lahadi ta kuma yin sanadin jikkata wasu mutane 390 na daban.

firaministan kasar Narendra Modi ya kai ziyara a wurin da hadarin ya auku, a yayin da ake ci gaba da bincike kan musababin tashin gobarar.

Bayanai sun nuna cewa har yanzu akwai wasu mutanen dake binne a karkashin gidan ibadar da kangayen wasu gidajen da suka wargaje sakamakon tashin gobarar, lamarin da ya sa, mai iyuwa ne za a sami karin mutuwar mutane.

Wasu bayanai na daban dai sun nuna cewa akwai wasu mutane da su kai kayayyakin wasan wuta ba bisa doka ba a cikin gidan ibadar.

Add comment


Security code
Refresh