An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 10 April 2016 17:44

Dakarun Tsaron Siriya na ci gaba da kai hari kan 'yan ta'adda a garin Halab

Dakarun Tsaron Siriya na ci gaba da kai hari kan 'yan ta'adda a garin Halab
Ministan sadarwa na kasar Siriya ya sanar da cewa Dakarun tsaron kasar da na sa kai na ci gaba da kai hare-hare kan 'yan ta'adda domin 'yanto garin Halab

Tashar telbijin Almayadin ta kasar Lobnon ta nakalto Amran Za'abi ministan sadarwar kasar Siriya na cewa Dakarun tsaron kasar da na sa kai na ci gaba da fadada kai hare-haren su kan 'yan ta'adda domin fitar da su daga cikin garin Halab.

Ministan ya ce lokaci ya yi ga biranan da suke da alaka da Washinton musaman birnin Ankara na Turkiya da Aman na Jodan su amince da yarjejjeniyar tsagaita wuta a kasar ta Siriya.

Har ila yau Za'abi ya kara da cewa lokaci ya yi da za a gudanar da tattaunawa ta kai tsaye amma ba tare da halartar kungiyoyin 'yan ta'adda cikin wakilan 'yan adawar ba.

Yayin da yake amsa tambaya ko a kwai sojojin kasashen waje a siriyan , Za'abi ya ce duk lokacin da Dakarun tsaron kasar Iran suka shiga wannan yaki za mu sanar, amma a halin da ake ciki baya ga Dakarun tsaron siriya, da kuma dakarun sa kai na kasar, babu wasu sojoji dake yakar 'yan ta'addar a siriyan , face kwararru masu bayar da shawara ga Sojojin kasar daga kwararu na Iran sai kuma jiragen yakin kasar Rasha dake taimakawa Sojojin wajen rusa tungar 'yan ta'addar a Siriyan.

Add comment


Security code
Refresh