An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 10 April 2016 17:18

Mayakan Ashabab sun kai hari kan Jami'an 'yan sanda a kasar Kenya

Mayakan Ashabab sun kai hari kan Jami'an 'yan sanda a kasar Kenya
'Yan sandar kasar Kenya sun sanar da jikkatar jami'an su uku sanadiyar wani hari da kungiyar Ashabab ta kai a ofishin 'yan sandar Wajir dake kan iykar kasar da Somaliya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Nairobi ya nakalto jami'an 'yan sanar kasar ta Kenya na cewa a daren jiya Assabar mayakan kungiyar Ahsbab na kasar Somaliya sun kaiwa jami'an su wani harin ba zata a ofishin 'yan sandar Diff dake kan iyakar kasar da Somaliya,lamarin da ya yi sanadiyar jikkata 'yan sanda guda uku, baya ga hakan ma, harin ya janyo asara mai dunbun yawa a cibiyar kasuwancin na garin Diff.

Garin na Diff na da nisan kilomita 500 daga arewa maso gabashin Nairobi fadar milkin kasar ta Kenya

Daga lokacin da Shugaba Uhuru kinyata na Kenya ya dare kan karagar milki a shekarar 2013, kungiyar ta Ashabab ta fara kai hare-haren ta'addanci a kasar ta Kenya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 400 a kasar.

Duk da irin matakan da kasashen Duniya suka dauka na kawar da kungiyar Ashabab a Somaliya, inda aka kafa rundunar kasashen Afirka Munusma da kuma kai hare-hare ta sama da kasa kan mayakan na Ashabab, har yanzu kungiyar na rike da ikon wani bangare na tsakiya da kuma kudancin kasar ta Somaliya, kuma kungiyar na ci gaba da kai hare-hare ba kakkwatawa kan jami'an tsaron Gwamnati da na kungiyar tarayyar Afirka a birnin Magadushu.

Add comment


Security code
Refresh