An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 10 April 2016 14:09

An Hana 'yan Adawa gudanar da zanga-zanga a kasar Angola

An Hana 'yan Adawa gudanar da zanga-zanga a kasar Angola
'Yan Sandar Angola sun hana 'yan adawa gudanar da zanga-zanga

Kamfanin dillancin Labaran Reuteus daga birnin Luwanda fadar milkin kasar Angola ya habarta cewa A yau Jami'an 'yan sanda sun hana 'yan adawa gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga wasu shugabanin kungiyoyin 'yan siyasa da Gwamnatin kasar ta kame kan zarkin shirya tawaye a kasar.

Shaidu da ido sun bayyana cewa tun a daren jiya ne Jami'an 'yan sandar dauke da makamai suka killace 'yan adawar da suka taru a dandalin 'yanci domin fara zanga-zangar a safiyar yau, lamarin da ya yi sanadiyar jikkata akalla mutane Uku.

Rahoton ya ce manufar zanga-zangar, nuna goyon baya ga wasu 'yan siyasa 17 da kotun kasar ta bayar da umarnin tsare su a gidan kurkuku kan zarkin da yin zagon kasa ga Gwamnatin José Eduardo dos Santos.

Masu Adawa da Gwamnatin ta Angola na zarkin shugaba José Eduardo dos Santos da yake rike da madafun ikon kasar tun a shekarar 1979 da mumanan jagoranci musaman ma wajen amfani da dunbun dukiyar da kasar ke samu ta hanyar sayar da Man fetur tare kuma da gyala wani bangare na magoya bayansa suna wadaka da kudaden kasa.

Add comment


Security code
Refresh