An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 10 April 2016 09:57

Sabuwar Gwamnatin Tsibirin Zanzibar Ta Sanar Da Kafa Majalisar Ministocinta

Sabuwar Gwamnatin Tsibirin Zanzibar Ta Sanar Da Kafa Majalisar Ministocinta
Shugaban tsibirin Zanzibar da ke cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar Tanzaniya ya sanar da sabuwar majalisar ministocin kasar da ta kunshi ministoci 15.

Shugaban tsibirin Zanzibar da ke cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar Tanzaniya Ali Mohammed Shein a yau Lahadi ya sanar da kafa sabuwar majalisar ministocin gwamnatinsa da ta kunshi ministoci 15 da kananan ministoci 7 domin gudanar da ayyukan ma'aikatun kasar na tsawon shekaru biyar.

Rahotonni sun bayyana cewa; Biyu daga cikin ministocin sun fito ne daga jam'iyyun adawar kasar duk da cewa babu wata jam'iyyar adawa da ta bukaci gwamnatin shugaba Ali Mohammed Shein da ta raba madafun iko da ita.

A ranar 20 ga watan Maris da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a Tsibirin na Zanzibar bayan da Hukumar zaben yankin mai zaman kanta "ZEC" ta rusa zaben farko da aka gudanar a watan Oktoban shekara ta 2015 da ta gabata saboda da zargin tafka magudi, inda shugaba Ali Mohammed Shein ya samu damar yin tazarce domin gudanar a wa'adin mulki karo na biyu, duk kuwa da matakin da 'yan adawa suka dauka na kauracewa zaben.

Add comment


Security code
Refresh