An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 10 April 2016 04:45

Misirawa Sun Yi Allah Wadai Da Matakin Shugaba Al-Sisi Na Mika Wasu Tsibiran Kasar Ga Saudiyya

Misirawa Sun Yi Allah Wadai Da Matakin Shugaba Al-Sisi Na Mika Wasu Tsibiran Kasar Ga Saudiyya
Kungiyar matasan yunkurin 6 ga watan Aprilu na kasar Masar sun yi Allah wadai da kuma kakkausar suka ga matakin da shugaban kasar Abdulfattah al-Sisi ya dauka na mika wasu tsibirai biyu na kasar ga kasar Saudiyya.

Kafar watsa labaran Al-Watan na kasar ta bayyana cewa wasu daga cikin kungiyoyi da jam'iyyun kasar Masar karkashin inuwar kungiyar da aka fi sani da Kungiyar Matasan Yunkurin 6 ga watan Aprilu sun nuna tsananin damuwarsu dangane da irin mika kai ga sarkin Saudiyya da shugaba Al-Sisin yayi a ziyarar da sarki Salman bin Abdul'aziz ya kai Masar din da kuma mika masa tsibiran 'Tiran' da kuma 'Sanafir' da yayi.

Rahotanni sun ce duk da cewa har ya zuwa yanzu kasashen biyu ba su cikakken bayani dangane da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin sarki Salman da shugaba al-Sisi din ba, to amma dai da dama suna ganin akwai alamun tambaya ainun kan yarjejeniyar ta su. Inda wasu majiyoyi suka ce shugaba Al-Sisin ya mika ikon wadannan tsibiran ne ga Saudiyya inda ita kuma Saudiyya za ta dinga ba wa kasar Masar din dala biliyan biyu da rabi a kowa shekara.

Su dai wadannan tsibirai guda biyu baya ga albarkatun man fetur da iskar gas da suke da su har ila yau kuma suna da wasu albarkatun na daban da kasar Masar din take amfanuwa da su.

Add comment


Security code
Refresh